Babin Zababbu Daga Hikimomin Amirul Muminina (A.S) Da Wa’azozinsa, Ya Hada Da Amsoshin Tambayoyinsa Da Gajerun Kalamansa Da Makamantansu.

1.  Ka zama cikin fitina kamar dan saniya mai shan nono bashi da baya balle a hau kuma bashi da hantsa balle a tatsa.

2.  Wanda ya yi kwadayi ya wulakanta kansa, wanda ya bayyanar da matsalarsa (asirinsa) ya yarda da kaskanci, wanda ya sallada harshensa (ya saki harshensa) akan ransa ya wulakanta ta, rowa aibi ne, tsoro tawaya ne, talauci yana dakusar da kaifin hankali gabarin hujjarsa, mai karantawa bako ne a garin sa, gajiyawa aibi ne, dauriya jarunta ne, zuhudu jari ne, taka tsantsan garkuwa ne, madalla da aboki (ya zama) yarda, ilmi gado ne mai daraja, ladabi ado ne mai sabuntuwa, tunani karau ne mai tsafta, kirjin mai hankali akwatin sirrinsa, sakin fuska tarkon soyayya ne, kawo hanzari kabarin aibobi ne.

3.  Amincewa juna maboyar aibi ne, duk wanda ya amincewa kansa fushi zai karu a kansa, sadaka magani ce mai warkarwa, ayyukan bayi na ibada a magaggauciya [Duniya] natsuwar (farin cikin) ido ne a majinkirciya [Lahira]

4.   Abin mamaki ga mutum yana gani ta hanyar kitse, yana Magana ta hanyar tsoka, yana ji ta hanyar kashi, kuma yana numfashi ta hanyar kafa.

5.   Idan duniya ta fuskanto mutum sai ta ara masa kyawawan waninsa, amma idan ta bada baya gare shi sai ta kwace masa kyawawan kansa.

6.   Kuyi ma’amala da mutane irin mu’amalar da in kun rasu zasu yi kukan rashinku, sannan  in kun rayu zasu kaunace ku.

7.   Idan ka sami iko akan makiyin ka, to ka sanya afuwa gare shi ta zama godiya ga Allah akan wannan iko da ka samu a kansa.

8.   Mafi gajiyawar mutane wanda ya kasa samun yardar ‘yanuwa, mafi gajiyawa daga gareshi shi ne wanda ya tozarta wanda ya samu daga cikinsu.

9.   Idan farkon ni’imomi suka zo muku, to kada ko kore mafi nisanta da karancin godiya.

10.   Wanda na kusa ya tozarta shi, sai a yalwata masa samun na nesa.

11.   Ba duk wanda aka fitanar ba ne abin zargi.

12.   Abubuwa suna rusunawa gaddarawa, har sai ajali ya yi halinsa.

13.   An tambaye shi game da fadin annabi (S.A.W) “ku canja furfura, kada ku yi kama da yahudawa”. Sai ya ce manzo ya fadi haka ne a lokacin da addini ya karanta (musulmi ba su da yawa) amma yanzu addini ya fadada, ya kuma karfafa, kowa yana iya yin abinda ya zaba.

14.   Ya fada game da wadanda suka ki yaki tare da shi: sun bar gaskiya, ba su taimaki barna ba.

15.   Wanda ya yi tafiya a tsakatsakin burinsa, ya hadu da ajalinsa.

16.   Ku zode wa ma’abota mutunci kananan laifuffukansu, domin ba wanda zai yi kuskure daga cikinsu sai hannunsa ya kasance a hannun Allah yana daukaka shi.

17.   An gwama tsorata da rasawa (idan ka ji tsoron yin abu ka rasa shi), kunya kuma da hani (haka nan wanda ya faye jin kunyar abu sai ya rasa), dama tana wucewa ne kamar wucewar gajimare, ku riki damar alheri.

18.   Muna da hakki idan an ba mu shi, in ba haka ba (ba a ba mu ba) sai mu hau kan duwainiyar rakumi, (wato sai mu dau hakuri) komai daren dadewa. Hawa duwainiyar rakumi gun larabawa alama ce ta kaskantar da mai hakki, wato wanda aka goya a baya rakumi yana zama dai dai kan duwainiyarsa ne ba gaba ba, wato kamar yaro ko bawa da ake goyawa a bayan rakumi ne[1].

19.   Wanda aikinsa ya jinkirtar da shi, dangantakarsa ba zata daukaka shi ba.

20.   Yana daga kaffarar zunubai taimakon wanda yake cikin kunci, da yaye wa mai bakin ciki bakin cikinsa.

21.   Ya kai dan adam, idan ka ga ubangijinka yana bibiyar ni’imarsa a gareka kana saba masa, to ka kiyaye shi.

22.   Ba wanda ya taba boye wani abu sai ya bayyana a harshensa da fadin fuskarsa.

23.   Tafi tare da ciwonka matukar zai tafiyu tare da kai. (Amma idan ba zaka iya ci gaba da aiki ba sai ka huta)

24.   Mafificin zuhudu, shi ne boye zuhudu.

25.   Idan ka kasance cikin tahowa da-baya-da-baya, mutuwa kuma cikin gabatowa gaba, to lallai ya mamakin saurin haduwa!

26.   Hattara hattara! Na rantse da Allah ubangiji ya boye (kurakurai) kai ka ce ya riga ya gafarta.

27.   An tambaye shi game da imani sai ya ce yana kai ginshiakai hudu ne: akan juriya, da yakini, da adalci, da jihadi: Hakuri yana kan rassa hudu: akan shauki, da tsoro, da zuhudu, da taka-tsantsan: wanda ya so aljanna zai fidiye daga shahawaice-shahawaice, wanda ya ji tsoron wuta zai nisanci haram, wanda ya yi gudun duniya zai ga saukin musibu, wanda ya yi sauraron mutuwa zai gaggauta zuwa aikata alherai.

Yakini yana kan rassa hudu ne: akan kaifin kwakwalwa, da fassarar hikima, da wa’aztuwa da daukan darasi, da bin dabi’un magabata: wanda ya ke da kwakwalwa hikima zata bayyana gareshi, wanda hikima ta bayyana gareshi zai dau darasi, wanda ya dau darasi, kamar yana cikin na farko ne.

Adalci yana kan rassa hudu ne: akan zufin fahimta, da sirrin ilimi, da kayen ni’ima, da kafaffen hakuri: duk wanda ya fahimata zai san zurfafan ilimi, wanda ya san zurfafan ilimi zai zo da komai daga hukunce-hukunce, wanda ya yi hakuri ba zai yi shisshigi da wuce gona da iri a al’amuransa ba, kuma zai rayu cikin mutane abin yabo.

Jihadi kuma Yana Kan rassa hudu ne: Akan umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna, da gaskiya a ko’ina, da kin fasikai. Wanda ya yi umarni da kyakkyawa ya karfafi muminai, Wanda ya hana mummuna ya turmuza hancin munafukai a kasa (ya bakanta ran munafikai), Wanda ya yi gaskiya a ko’ina ya sauke nauyin da yake Kansa, Wanda ya ki fasikai ya yi fushi saboda Allah Allah zai yi fushi saboda shi ya kuma yardar da shi ranar sakamako.

Kafirci yana kan shika-shikai hudu ne: akan zurfafawa, da jayayya, da karkata, da sabawa: wanda ya zurfafa ba zai karkata zuwa ga gaskiya ba, wanda jayayyarsa ta yi yawa da jahilci makantarsa ga barin gaskiya zata dawwama, wanda ya karakace mummuna zai zama kyakkyawa gunsa kuma kyakkyawa ya zama mummuna gunsa ya yi maye mayen bata, wanda ya saba hanyoyinsa zasu kulle masa (su yi tsauri), al’amarinsa ya tsananta, mafitarsa ta yi wahala ta kuntata.

 Kokwanto yana kan rassa hudu ne: akan jayayya, da tsoro, da kai-kawo, da mika wuya: wanda ya sanya jayayya ta zama masa al’ada darensa ba zai waye ba, wanda abinda yake gabansa ya tsorata shi zai sallama (tankwasa ya rusuna akan kafafunsa) a gabansa, wanda ya kai-kawo a kokwanto kofatun shedanu sa tattaka shi, wanda ya mika wuya ga halakar duniya da lahira zai halaka a cikinsu.

28. Mai aikata alheri ya fi alheri alheri, mai aikata sharri ya fi sharri sharri. (wato mai aikata alheri shi ne mafi girman alheri daga alheri shi kansa, haka ma mai sharri shi  ya fi sharri zama sharri)

29. Ka zama mai sauki kada ka zama mai almubazzaranci, ka zama mai tsakaitawa, kada ka zama mai kwauro.

30. Mafi girman wadata barin buri.

31. Wanda ya gaggautawa mutane (wato farkon saninsu da shi) da abinda suke ki, sai su fadi abinda ba su sani ba game da shi.

32. Wanda ya tsawaita buri zai munana aiki.

33. Dagatoci sun hadu da shi akan hanyarsa ta sham sai suka sauka daga kan dawakansu suka gaggauta  zuwa wajansa:

Sai ya ce da su: menene wannan kuka aikata? 

Sai suka ce: dabi’a ce da muke girmama sarakunanmu da ita.

Sai (A.S) ya ce: wallahi wannan ba zai amfana wa sarakunanku komai ba, ku kuna tsanantawa kanku ne kawai a duniya ku kuma tabe da shi a lahira, tir da wahala da bayanta azaba ce, kuma ribar sakin fuska ta yawaita da aminci daga wuta yake tare da ita.

34. Yana mai gaya wa dansa Hasan (A.S): ya kai dana ka kiyaye hudu daga gareni, matukar ka yi aiki da su ba abinda zai cutar da kai: Hakika mafi wadatar wadata shi ne hankali, mafi girman talauci shi ne wauta, mafi dimuwar dimuwa shi ne ji-ji-da-kai, mafi girman nasaba shi ne kyawun dabi’u.

Ya dana na hana ka abota da wawa, domin shi ya kan so ya amfane ka sai ya cutar da kai. Kuma na hana ka abota da marowaci, domin shi ya barka shi ne ya fi da bukatuwar da zaka zama kana yi masa.

Na hanaka abota da fajiri, domin shi zai iya sayar da kai da dan kankanin abu. Na hana ka abota da makaryaci, domin shi kamar sururi ne: da yake kusantar da nesa gareka, yake nesantar da kusa gabarinka.

35. Babu wani kusanci da Allah da nafiloli, idan ta cutar da farillai.

36. Harshen mai hankali yana bayan zuciyarsa, zuciyar wawa tana bayan harshensa[2].

Wata ruwayar tana cewa zuciyar wawa tana bakinsa, harshen mai hankali yana zuciyarsa. (Ma’anarsu da ta sama daya ce).

37. Yana mai gaya wa wani daga sahabbansa da ya samu wata rashin lafiya: Allah ya sanya zoginka ya zama shafewa ga zunubanka, domin rashin lafiya ba shi da lada sai dai yana shafe zunubai, yana kakkabe ta irin kakkabewar ganyayyakin itace, domin lada kadai yana samuwa ne ta hanyar zance da harshe, da aiki da hannaye da kafafu, kuma Allah yana shigar da wanda ya so daga bayinsa aljanna da kyakkyawar niyya da zuciya ta gari.

38. Game da Habbab Dan Aratt yana cewa: Allah ya ji kan Habbab, ya musulunta da son kansa, ya yi hijira yana mai biyayya, ya wadatu da kadan, ya yarda da ubangijinsa, ya rayu mai jihadi.

39. Farin ciki ya tabbata ga Wanda ya tuna lahira, ya yi aiki saboda hisabi, ya wadatu da kadan, ya yarda da hukuncin ubangijinsa.

40. Da zan doki hancin mumini da takobina wannan akan sai ya ki ni da bai ki ni ba, da na zuba duniya da dukkan kawanyarta (adonta) ga munafuki akan sai ya so ni da bai so ni ba: saboda an hukunta kuma ya zartu daga harshen Annabi ummiyyi (S.A.W) cewa: “Ya Ali! Mumini ba zai ki ba, munafuki ba zai so ka ba”.

41. Mummuna da zai bata maka rai shi ya fi kyakkyawa da take kayatar da kai a wajan Allah.

42. Kimar mutum tana daidai gwargwadon himmarsa, gaskiyarsa kuma tana daidai mutuncinsa, jarumtakarsa tana daidai gwargwadon karfinsa, kamewarsa tana daidai gwargwadon kishinsa.

43. Rabauta da daukar niyya ne, niyya kuma tana daga tuntuntunin ra’ayi, ra’ayi kuma yana samuwa da kewaye sirrai.

 (Matakai ne guda hudu akwai ilimi da abu da sanin sirrinsa, sannan sai kyakkyawan ra’ayi, sannan niyya da azama akansa sannan sai a shiga aikata shi a samu rabauta).

44. Ku ji tsoron hayewar mai karimci idan ya ji yunwa, marowaci kuma idan ya koshi.

45. Zukatan maza dabbar daji ce, wanda ya saba da ita sai ta kusanto gareshi.

46. Ka rabauta kwarai matukar aibinka ya zama asirtacce.

47. Wanda ya fi cancanta a cikin mutane ya yi afuwa shi ne wanda ya fi ikon ukuba daga cikinsu.

48. Kyauta ita ce wacce take tun farko, amma idan ta kasance domin an roka ne to wannan kunya ce da gudun zargi.

49. Babu wadata kamar hankali, babu talauci kamar jahilci, babu gado kamar ladabi, babu mai taimako kamar shawara.

50. Hakuri kala biyu ne: hakuri akan abin da kake ki, da hakuri gabarin abinda kake so.

51. Wadata acikin bakunta zaman gari ne, talauci a cikin zaman gari bakunta ce.

52. Wadata dukiya ce da ba ta karewa.

53. Dukiya mabubbugar shahawa ce.

54. Wanda ya yi maka gargadi kamar wanda ya yi maka albishir ne.

55. Harshe zaki ne, idan aka bar shi sai ya yi cizo.

56. Mace kunama ce harbinta mai zaki ne.

57. Idan aka gaishe da kai da gaisuwa to ka amsa da mafi kyawunta, idan aka mika maka hannu ka saka mata da abin da ya zarta nata, amma duk da haka fifiko yana ga wanda ya fara.

58. Mai ceto shi ne ginshikin (karfin) mai nema.

59. Mutanen duniya kamar matafiya ne da ake tafiya da su alhalin suna bacci.

60. Rashin masoya bakunta ne.

61. Kubucewar bukata ya fi sauki daga nemanta wajan wadanda ba ma’abotanta ba.

62. Kada ka ji kunyar bayar da kadan domin hanawa ya fi shi karanci.

63. Kamewa (gabarin tambaya) adon talauci ne, godiya adon wadata ce.

64. Idan babu abinda kake nema (ko kuma abin da kake so bai wakana ba) to kada ka damu da yaya ka kasance.

65. Ba yadda zaka ga jahili sai dai imma mai wuce gona da iri ko mai gazawa.

66. Idan hankali ya cika Magana sai ta yi karanci.

67. Zamani yana tsofar da jiki, yana kuma jaddada buri, yana kusantar da mutuwa, yana nesantar da burace-burace, wanda ya same shi ya jigata, wanda ya kubuce masa ya wahala.

68. Wanda ya sanya Kansa shugaba ga mutane to yana kansa ya fara koyar da kansa kafin ya koyar da waninsa, ya zama tarbiyyatar da zuciya kafin ya tarbiyyatar da harshensa, mai koyar da kansa mai ladabtar da ita shi ya fi cancanta da girmamawa fiye da mai koyar da mutane mai ladabtar da su.

69- Lumfashin mutum takunsa ne zuwa ajalins.

70- Duk abin kididdiga mai tawaya ne, kuma duk abin da ake sauraro mai zuwa ne.

71- Idan al'amura suka rikitar suke cakude sai a kiyasta karshenta da farkonta.

72- Daga labarin Dhirar dan Dhamuratad Dhubabi yayin da ya shiga wajan Mu'awiya da kuma tambayarsa game da Amirulmunin (A.S) ya ce: Na shaida hakika na gan shi a irin tsayuwar da yake yi dare ya riga ya yi duhu, yana mai tsayuwa a mihrabinsa yana rike da gemunsa yana mai makyarkyata irin makyarkyatar wanda aka sara[3], yana mai kuka kukan mai bakin ciki, yana cewa: Ya duniya! Ya duniya! Ki yi nesa da ni, shin kin zo mini ne ko kuma kina shauki da bege zuwa gareni? A'aha, Ki sani lokacin da zaki shiga zuciyata bai yi ba tukuna! Ya munana har abada! Ki yaudari wanina, ba na bukatar ki, hakika na riga na sake ki saki uku da babu dawowa a cikinta!

Rayuwarki gajeriya ce, al'amarinki kankani ne, burinki wulakantacce ne.

Wayyo! Saboda karancin guzuri, da tsayin tafarki, da nisan tafiya, da girman mashiga!

73- Yana daga cikin maganarsa yayinda mai tambaya ya tambaye shi: Shin tafiyar mu zuwa Sham da hukuncin Allah ne da kuma kaddarawarsa? Bayan magana mai tsayi yana mai cewa: Kaiconka! Kai kana tsammanin hukunci na tilas, da kuma kaddara ta lallai! Da kuma ya kasance haka ne da lada da azaba sun zama wasa, da kuma alkawari da narko sun saraya.

Allah madaukakin sarki ya umarci bayinsa bisa zabi, ya hana su bisa tsoratarwa, ya kuma kallafa musu mai sauki, bai kallafa musu mai tsanani ba, ya ba su mai yawa a kan dan kadan –da suka aikata- ba a kuma saba masa don rinjayarsa, ba a bi shi don tilastawa ba, bai kuma aiko annabawa don wasa ba, bai saukar da littafi don raha ba, bai kuma halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu don barna ba, “Wannan shi ne tsammanin wadanda suka kafirta, to azabar wuta ta tabbata a kan wadanda suka kafita”

74. Imam Ali (A.S) ya ce:  ka karbi hikima ko’ina take, ka sani hikima tana kasancewa a kirjin munafuki sai ta jujjuya a kirjinsa har sai ta fita sai ta zauna tana mai tafiya zuwa ga ma’abotanta a cikin kirjin mumini.

75. Imam Ali (A.S) ya fadi kwatankwacin hakan: Hikima bataccen kayan mumini ne, ka riki (karbi) hikima koda kuwa daga munafukai ne.

76. Imam Ali (A.S) ya ce: Kimar kowane mutum shi ne abin da yake kayatar da shi.

{wasu sun fassara wannan magana da cewa “Kimar kowane mutum shi ne abin da yake kawatuwa da shi” ko kuma “Kimar kowane mutum (wato; abin da yake ba wa mutum kima) shi ne abin da mutum din yake kyautata shi”}

77. Imam Ali (A.S) ya ce: na yi muku wasici da abubuwa biyar da zaku yi tafiye-tafiye da rakuma domin ku same su da sun cancanci hakan: kada wani daga cikinku ya kaunaci kowa sai ubangijinsa, kuma kada ya ji tsoro sai zunubansa, kada wani ya ji kunya idan aka tambaye shi abin da bai sani ba ya ce: ban sani ba, kuma kada wani ya ji kunya idan bai san wani abu ba ya nemi saninsa.

Kuma game da hakuri, hakika misalin hakuri ga imani kamar misalin kai ne ga jiki, kuma babu wani alheri ga jikin dab a shi da kai, ko kuma imanin dab a shi da hakuri tare da shi.

78. Imam Ali (A.S) ya ce da wani mutum da ya yawaita yabonsa, kuma alhalin Imam (A.S) ya kasance yana sanin cewa (shi wannan mutumin karya yake yi a zuciyarsa): Ni ina kasan abin da ka fada, kuma sama da abin da yake cikin ranka nake.

79. Imam Ali (A.S) ya ce: ragowar takobi (mutanen da suka rage bayan yaki domin ‘yancinsu) su ne wadanda jama’arsu ta fi wanzuwa, kuma suka fi  yawaitar yaduwar ‘ya’ya.

80. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya bar fadin: ban sani ba, to an samu makasarsa.

81. Imam Ali (A.S) ya ce: ra’ayin dattijo ya fi soyuwa gareni fiye da karfin jarumtakar saurayi.

An ruwaito a wata ruwaya fiye da halartar saurayi (a wajen yaki).

82. Imam Ali (A.S) ya ce: Ina mamakin wanda yake yanke kauna alhalin akwai istigfari tare da shi.

  

83. Abu Ja’afar Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ruwaito daga Imam Ali (A.S) ya ce: Akwai aminci biyu masu tseratarwa daga azabar Allah (S.W.T) da suka kasance a fadin kasa, gashi hakika an riga an dauke dayan, don haka ku yi riko da dayan: amma wanda aka dauke shi ne manzon Allah (S.A.W).

Amma wanda ya wanzu shi ne istigfari, ubangiji madaukaki ya ce: “Allah bai kasance mai yi musu azaba ba alhalin kai kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai yi musu azaba ba alhalin suna istigfari”.

84. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya gyara tsakaninsa da Allah to Allah zai gyara tsakaninsa da mutane, wanda kuma ya gyara lahirarsa, to Allah zai gyara masa duniyarsa, wanda kuma ya kasance mai yi wa kansa wa’azi, to Allah zai kasance mai kiyaye wa gareshi.

85. Imam Ali (A.S) ya ce: malamin da lallai shi ne ya isa malami shi ne wanda bai sanya mutane sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai sanya su yanke kauna daga tausayawar Allah ba, kuma bai amintar da su daga makircin (azabar) Allah ba.

86. Imam Ali (A.S) ya ce: mafi kaskancin ilimi shi ne wanda ya tsaya a kan harshe kawai, mafi daukakarsa shi ne wanda ya bayyana a kan gabobi da sassan asali na jiki.

  

87. Imam Ali (A.S) ya ce: Hakika wadannan zukata suna kosawa kamar yadda jikunkuna suke kosawa, don haka ku nema mata hikima mai dadi.

88.Imam Ali (A.S): kada xayanuk Ya ce: ya ubangiji ni ina neman tsarinka daga fitina, domin babu wani mutum sai yana tare da wata fitina, sai dai dukkan wanda zai nemi tsari to ya nemi tsari daga masu vatarwa na daga fitinu, haqiqa Allah maxaukaki yana cewa: “Ku sani cewa haqiqa dukiyoyinku ‘ya’yanku fitina ne”, ma’anar wannan shi ne; cewa shi maxaukaki yana jarraba su da dukiyoyi da ‘ya’ya domin ya bayyanar da mai fushi da arzikinsa da kuma wanda ya yarda da rabonsa, duk da kuwa ubangiji maxaukaki ya fi su sanin kawukansu, sai dai domin ya bayyanar da ayyukan da, da sun e zasu cancanci lada da uquba, domin wasu suna son maza kuma suna qin mata, wasu kuma suna son juya (havaka) dukiya ne suna qin tawayar halal.

Wannan yana daga cikin maganganu masu qayatarwa da aka ji daga gareshi (A.S) a tafsiri.

89. An tambayi Imam Ali (A.S) game da alheri mene ne shi? Sai Imam Ali (A.S) ya ce: alheri ba shi ne dukiyarka da ‘ya’yanka su yawaita ba, sai dai alheri shi ne; iliminka ya yawaita, kuma haqurinka ya girmama, kuma ka yi alfahari ga mutane da bautar ubangijinka, idan ka kyauta sai ka godewa Allah, idan kuma ka yi munana sai ka nemi gafarar Allah. Kuma babu wani alheri a duniya sai ga mutane biyu: mutumin da ya yi zunubi yana mai riskarsa da yin tuba, da kuma mutumin da yake gaggawa cikin aikata alheri. kuma aiki ba ya qaranta tare da taqawa, yaya kuwa abin da ake karva zai qaranta?

90. Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa mafi cancantar mutane ga annabawa su ne mafi sanin abin da suka zo da shi, sannan sai ya karanta ayar nan “haqiqa mafi cancantar mutane da ibrahim su ne waxannan da suka bi shi, da wannan annabi da kuma waxannan da suka yi imani, kuma Allah shi ne majivancin muminai…”

Sannan sai Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa masoyin Muhammad (S.A.W) shi ne; wanda ya bi Allah koda kuwa nasabarsa ta nisanta, kuma maqiyin Muhammad (S.A.W) shi ne wanda ya savawa Allah (S.W.T) koda kuwa nasabarsa ta kusanta!

91. Imam Ali (A.S) ya ce: -alokacin ya ji wani mutum daga Haruriyya[4] yana sallar dare, yana karatun kur’ani, sai ya ce: Bacci a kan (bisa) yaqini ya fi salla cikin kokwanto.

92. Imam Ali (A.S) ya ce: ku sanya wa labari hankali idan kuka ji shi hankalin kiyayewa ba hankalin ruwaitowa ba, ku sani haqiqa masu ruwaito ilimi suna dayawa, amma kuma masu kiyayewa (sanya masa hankali) ‘yan kaxan ne.

93. Imam Ali (A.S): -a lokacin ya ji wani mutum yana cewa; “Inna lil-Lahi wa’inna ilaihi raji’un” sai ya ce: Haqiqa faxinmu cewa: “Inna lil-Lahi” furuci ne a kan kawukanmu ga mulkin Allah, kuma faxinmu; “Wa’inna ilaihi raji’un” furunci ne a kan kawukanmu da halaka.

94. Imam Ali (A.S) ya ce: -a lokacin da wasu mutane suka yabe shi a gabansa-: Ya ubangiji kai ne mafi sani da ni daga kaina, kuma ni ne mafi sani da kaina fiye da su, ubangiji ka sanya ni fiye da yadda suke tsammani, ka gafarta mana abin da ba su sani ba.

95. Imam Ali (A.S) ya ce: Ba yadda biyan buqatu zai daidaitu sai da abubuwa uku: da qaranta ta domin ta girmama[5], da kuma neman voye ta domin ta bayyana, da kuma gaggauta ta domin ta yi sannu-sannu.

96. Imam Ali (A.S) ya ce: Da sannu wani zamani zai zo wa mutane da ba a kusantarwa a cikinsa sai annamimi, kuma ba a qayatarwa sai fajiri, kuma ba a raunatarwa sai mai adalci, suna ganin sadaka a matsayin abin biyan bashi, kuma sadar da zumunci a matsayin gori, kuma ibada domin neman fifiko a kan mutane! A lokacin ne sarauta (tafiyar da mulki) zata kasance da shawarar bayi, da jagorancin yara, da kuma tsarawar fixiyayyun mutane!

97. Imam Ali (A.S) ya ce: -yana sanye da wani zane tsoho da ya qoqe, sai aka yi masa magana game da haka. Sai (A.S) ya ce: Zuciya tana tsoratuwa saboda shi, kuma rai tana qasqantuwa da shi, kuma muminai suna koyi da shi.

98. Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa duniya da lahira maqiya ne biyu masu karo da juna, kuma hanyoyi biyu ne masu savawa, duk wanda yake son duniya ya jivance ta to sai ya qi lahira ya yi gaba da ita, su kamar gabas da yamma ne. mai tafiya tsakaninsu duk sadda ya kusanta da xayarsu sai ya yi nesa daga xayar, kuma su masu kishiyantar juna ne!

99. Daga Nuf al’bikaliyyu, ya ce: Na ga Imam Ali (A.S) a wani dare, ya fito waje daga kan daga shimfixarsa, sai ya saurara kaxan sannan sai ya ce: Ya kai Nuf, shin kana bacci ne ko kuma kana farke?

Sai na ce: Ina farke ne ya amirul muminin.

Sai ya ce: Ya kai Nufu, Farin ciki ya tabbata ga masu gudun duniya, masu kwaxayi a lahira, waxannan su ne mutanen da suka riqi qasa mashimfixa, turvayarta kuma shimfixa, ruwanta kuma daddaxa, Kur'ani kuwa alami[6], addu’a kuwa tufafi[7], sannan sai suka yayyaga (kekketa) duniya irin yayyagawar nan (irin ta tafarkin) da Masihu (A.S) (annabi Isa) ya yi mata.

Ya kai Nufu, Haqiqa Dawud (A.S) ya tsaya daidai irin wannan awar ta dare, sai ya ce: wannan sa’a ce da babu wani bawa da zai kira Allah ya yi addu’a a cikinta sai an amsa masa, sai dai idan ya kasance mai karvar haraji ne, ko kuma xan leqen asiri, ko kuma xan sanda, ko mai buga ganga, ko kuma makaxi.

100. Imam Ali (A.S) ya ce: Haqiqa Allah maxaukaki ya farlanta muku wasu farillai to kada ku tozarta ta, kuma ya shata muku iyaka kada ku shige ta, kuma ya hana ku wasu abubuwan to kada ku keta (kutsa) su, sannan ya yi shiru gabarin wasu abubuwa da bai bar su ba don mantuwa, to kada ku xora wa kanku nauyinsu.

101. Imam Ali (a.s) ya ce: Mutane ba su taba barin wani abu na lamarin addininsu ba saboda gyara duniyarsu, sai Allah ya bude musu abin da ya fi shi cutarwa.

102. Imam Ali (a.s) ya ce: Da yawa malamin da jahilcinsa ya kashe shi, kuma iliminsa yana tare da shi ba ya amfanarsa.

103. Imam Ali (a.s) ya ce: Hakika an damfara wata tsoka da jijiyar mutum da take ita ce mafi ban mamakin cikinsa: wannan ita ce; zuciya, ga ta da tarin hikimomi, da kuma abubuwan da suka sassaba mata, idan ya samu kansa cikin yin kauna sai kwadayi ya kaskantar da shi, idan kuwa ya samu rarumar kwadayi sai zari ya halaka shi, idan kuma yanke kauna ya mamaye shi sai bakin ciki ya kashe shi, ida kuwa ya samu fushi sai takaici ya tsananta masa, idan kuwa yarda ta rabautar da shi sai ya manta da kiyayewa, idan kuwa tsoro ya kama shi sai hattara ta shagaltar da shi, idan ya samu yalwar aminci sai gafala ta yi masa kwace, idan musiba ta auka masa sai raki ya kunyata shi, idan ya samu dukiya sai ya yi takama, idan talauci ya cije shi sai bala'i ya shagaltar da shi, idan yunwa ta raunata shi sai raunin jiki ya gurfanar da shi, idan kuwa koshi ya yi masa yawa sai katon ciki ya kuntata masa (lumfashi), don haka ne duk wani takaitawa gareshi mai cutarwa ce, duk wani wuce gona da iri nasa mai batawa ne.

104. Imam Ali (a.s) ya ce: Mu ne matasan tsakiya, da su ne wanda yake zuwa yake riska, garesu ne mai shisshigi yake komawa.

105. Imam Ali (a.s) ya ce: Ba mai tsayar da lamarin Allah sai wanda ba ya kagowa, ba ya kamantuwa, ba ya bin kwadayi.

(Mai wakiltar Allah ba ya kago karya, ba ya kama da masu barna, ba ya kwadayi)

106. Imam Ali (a.s) -Lokacin nan Sahalu dan Hunaif Ansari ya rasu a Kufa bayan ya dawo daga Siffain, ya kasance daga mafi soyuwar mutane a gunsa, sai ya ce: Da dutse ya so ne, da ya tsattsage.

{Wato; masu sona bala'i yana yi musu yawa, yana gaggauta musu, wannan ya yi kama da fadinsa mai zuwa}

 107. Imam Ali (a.s) ya ce: Wanda ya so mu Ahlul Baiti (a.s) to ya tanadi bargon talauci.

108. Imam Ali (a.s) ya ce: Babu Dukiyar da ta fi hankali amfani, kuma babu wata kadaita da ta fi jin kai dimuwa, babu hankalin da ya kai shirya lamurra, babu wata kyauta da ta kai takawa, babu wani aboki da ya kai kyawun halaye, babu gadon da ya kai ladabi, babu jagoran da ya kai dacewa, babu kasuwancin da ya kai aiki na gari, babu ribar da ta kai lada, babu tsantsenini da ya kai tsayawa gun shubuha, babu wani zuhudun da ya kai gudun haram, kuma babu ilimin da ya kai tunani, babu ibadar da ta kai yin farilla, babu imanin da ya kai kunya da hakuri, babu nasaba da ta kai kaskantar da kai, babu daukakar da ta kai ilimi, babu taimakon da ya kai yin shawara.

109. Imam Ali (a.s) ya ce: Idan gyara ya mamaye zamani da mutanensa, sannan sai wani mutum ya munana zato ga wani mutum da babu wani kuskure da ya bayyana gareshi, to ya zalune shi! Amma idan barna ta mamaye zamani da mutanensa, sai wani mutum ya kyautata wa wani mutum zato, to ya yaudari kansa.

110. Imam Ali (a.s) ya ce: Yaya muka same ka ya Sarkin Muminai? Sai ya ce: Yaya wanda yake karewa da wanzuwarsa zai kasance, kuma yake cutuwa da lafiyarsa, kuma ake zo masa ta inda yake aminta!.

111. Imam Ali (a.s) ya ce: Da yawa wanda aka yi wa istidraji da kyautata masa, kuma da mai ruduwa da suturta masa, da mai fitinuwa da kyakkyawan yabon sa! Babu wani mutum da aka jarraba da wani abu kamar yi masa jinkiri.

112. Imam Ali (a.s) ya ce: Mutum biyu sun halaka a kaina: Mai so mai wuce gona da iri, da mai ki mai gaba.

113. Imam Ali (a.s) ya ce:  Tozarta dama, bakin ciki ne.

114. Imam Ali (a.s) ya ce: Misalin duniya kamar macijiya ce: Taba ta yana da taushi, amma guba mai halakarwa ce a cikinta, mai ruduwa jahili yana son ta, mai kula da hankali yana gudun ta.

115. Imam Ali (a.s) ya fada –Yayin nan an tamaye shi game da Kuraishawa-: Amma Banu Makhzum su kanshin Kuraishawa ne, muna son zancen mazajensu, kuma muna aurar matansu. Amma Banu Abdusshams, Su ne mafi nisan ra’ayi, kuma mafi hanin abin da yake garesu. Amma mu, mu ne mafi sakin hannu, mafi kyautar rayukanmu yayin mutuwa, su ne mafi yawa, mafi makirci, mafi munani, mu kuma mu ne mafi fasaha, mafi rangwame, mafi kyawu.

116. Imam Ali (a.s) ya ce: Akwai bambanci tsakanin ayyuka biyu: Aikin da dadinsa yake tafiya, wahalarsa ta rage, da aikin da wahalarsa take tafiya, ladansa ya rage.

117. Wani mutum ya bi wata janaza yana mai yin dariya, sai Imam Ali (a.s) ya ce: Kamar dai mutuwa a cikin (duniya) an rubuta ta ne a kan waninmu, kamar dai gaskiya a cikinta ta wajabta kan waninmu ne, kamar dai wannan abin da muke gain na matattu tafiya ce da bayan jimawa zasu dawo gunmu! Muna binne jikinsu, muna cin gadonsu, kamar dai mu zamu dawwama ne, mun mance dukkan wani mai wa’azi, an jefe mu da dukkan lalacewa!!.

118. Imam Ali (a.s) ya ce: Farin ciki ya tabbata ga wanda ya kaskan da kansa, ya dadada nemansa, ya kyautata halinsa, ya ciyar da abin da ya rage na dukiyarsa, ya kuma kame harshensa, ya nesantar da sharrinsa daga mutane, kuma sunna ta ishe shi, ba a danganta shi da bidi’a ba.

119. Imam Ali (a.s) ya ce: Kishin mace kafirci ne, Kishin namiji kuwa imani ne.

120. Imam Ali (a.s) ya ce: Zan yi bayanin musulunci da bayanin da wani bai yi ba kafina: Musulunci shi ne mika wuya, mika wuya kuwa shi ne yakini, yakin kuwa shi ne gaskatawa, gaskatawa kuwa shi ne furuci, furuci kuwa shi ne bayarwa, bayarwa kuwa shi ne yin aiki.

121. Imam Ali (a.s) ya ce: Ina mamakin marowaci yana gaggauto da talaucin da yake guje masa, kuma wadatar da yake nema tana kubuce masa, sai ya yi rayuwar talakawa a duniya, kuma a yi masa hisabin masu wadata a lahira. Kuma ina mamaki ga mai girman kai wanda ya kasance mani a jiya, gobe kuma mushe ne. Kuma ina mamakin wanda yake kokwanton samuwar Allah, alhalin yana ganin halittar Allah. Kuma ina mamakin wanda ya manta da mutuwa alhalin yana ganin mutuwa. Kuma ina mamakin wanda ya yi musun tashin karshe, alhalin yana ganin tashin farko. Kuma ina mamakin mai raya gidan karewa, yana barin gidan wanzuwa.

122. Imam Ali (a.s) ya ce: Wanda ya takaita a aiki sai a jarrabe shi da bakin ciki, kuma babu wata bukata ga Allah ga wanda Allah ba shi da wani rabo a cikin ransa da dukiyarsa.

123. Imam Ali (a.s) ya ce: Ku kiyayi sanyi a farkonsa, ku kuma fuskance shi a karshesa, ku sani yana yi wa jiki abin da yake yi wa shuka, farkonsa yana kuna, karshensa yana yin ganye. (Yana taba jiki a karshensa bayan ya saba da shi, sai ya kasance ya fi sauki ga jiki a lokacin).

124. Imam Ali (a.s) ya ce: Girman mahalicci gunka, yana kaskantar da abin halitta a idanuwanka.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria
Hfazah@yahoo.com

125. Imam Ali (a.s) ya ce: -A lokacin ya dawo daga yakin Siffain, sai ya yi nuni ga kaburburan bayan birnin Kufa ya ce- "Ya ku mutanen gidaje masu dimautarwa, masaukan talauci, kaburbura masu duhu. Ya ku ma'abota turbaya, ya ma'abota bakunci, ya ma'abota kadaitaka, ya ma'abota dimuwa, ku ne masu rigo masu wucewa gaba, mu masu biyo sawunku ne. Amma gidaje dai an zauna su, kuma mata an aure su, kuma dukiyoyi an raba su. Wannan shi ne labarinmu ku kuma me ye labarinku. Sannan sai ya juya wurin sahabbansa sai ya ce: Amma da an yi musu izinin yin magana da sun ba ku labarin cewa "Hakika Takawa ita ce mafificin abu.".

126. Imam Ali (a.s) ya fada yayin da ya ji wani mutum yana sukan duniya: "Ya kai mai zagin duniya, mai ruduwa da rudinta, mai yaudaruwa da barnarta, yaya kake ruduwa da duniya sannan sai ka zarge ta, kai ne mai laifi gareta ko kuwa ita ta yi maka laifi, yaushe ne ta kawar da hankalinka ko ta yaudare ka? Shin don ta kayar da iyayenka saboda tsufa, ko kuma saboda makwancin uwayenka karkashin kasa? Mutum nawa ka yi jinya da hannunka, ko ka sanya kuma nawa ka yi wa hidima suna rashin lafiya da kake nema musu waraka, kana mai siffanta musu magani -yadda za a yi amfani da shi- tausayawarka ba ta amfani daya daga cikinsu ba, kuma ba su abin bukatarsu bai magance musu komai ba, kuma ba ka iya kare shi ba da karfinka, duniya ta nuna maka ita wace ce, kuma faduwarsa ita ma faduwarka ce. Hakika duniya gidan gaskiya ce ga wanda ya gaskata ta, kuma gidan lafiya ce ga wanda ya fahimce ta, kuma gidan wadata ce ga wanda ya yi guzurinta, kuma gidan wa'azi ce ga wanda ya wa'aztu da ita, masallacin masoya Allah ce, masallatar mala'ikun Allah ce, kuma masaukar wahayin Allah ce, wurin kasuwar waliyyan Allah ne, ku nemi rahama a cikinta, ku ribaci aljanna a cikinta. Waye wannan da yake zaginta alhalin ta san 'ya'yanta, kuma ta yi kira da rabuwa da ita, ta yi jimamin rashinta da rashin ma'abotanta.

Sai ta misalta musu bala'i da bala'inta, ta kwadaitar da su zuwa ga farin ciki da farin cikinta, sai ta huta da lafiya, ta wayi gari da musiba, tana mai kwadaitarwa da tsoratarwa, tana mai firgitarwa da yin gargadi. Sai wasu mazaje masu wayewar gari da nadama suka zage ta, wasu kuwa suka yabe ta ranar kiyama, duniya ta tunatar da su sai suka tunatu, ta yi musu magana sai suka gaskata, ta yi musu wa'azi sai suka wa'aztu".

127. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah yana da wani mala'ika da yake kira kowace rana cewa; Ku Haifa domin mutuwa, ku tara domin karewa, ku gina domin rushewa".

128. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duniya gidan wucewa ne zuwa gidan tabbatuwa, mutane a cikin iri biyu ne: Mutumin da ya sayar da ransa sai ya halaka ta, da mutumi da ya sayi ransa sai ya 'yanta ta".

129. Imam Ali (a.s) ya ce: "Aboki ba ya zama aboki sai ya kiyaye abokinsa cikin abubuwa uku: Cikin bala'insa, da boyuwarsa, da mutuwarsa".

130. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda aka ba wa hudu to ba za a haramta masa hudu ba : Duk wanda aka ba wa addu’a ba za a haramta masa addu’a ba, kuma dukkan wanda aka ba wa tuba ba za a haramta masa karba ba, kuma duk wanda aka ba wa istigfari ba za a haramta masa gafara ba, kuma duk wanda aka ba wa godiya to ba za a haramta masa dadi ba. Kuma gaskiyar wannan a cikin littafin Allah shi ne fadin Allah madaukaki a cikin addu’a: Ku kira ni zan amsa muku, kuma ya fada game da istigfari: Duk wanda ya yi mummuna ko ya zalunci kansa sannan sai ya nemi gafarar Allah, zai samu Allah mai gafara mai rahama, haka nan ya fada game da godiya: Idan kun gode to zan kara muku. Ya fada game da tuba: Hakika tuba gun Allah na wadannan da suke aikata mummuna da jahilci ne, sannan sai su tuba a kusa, to wadannan Allah yana karban tubansu, kuma hakika Allah masani ne mai hikima".

131. Imam Ali (a.s) ya ce: "Salla kusancin dukkan mai tsoron Allah ce, kuma hajji jihadin duk wani mai rauni ne, kuma kowane mutane yana da zakka, amma yin azumi ne zakkar jiki, kyakkyawan zaman aure kuma shi ne jihadin mace".

132. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku nemi saukar arziki da yin sadaka, kuma duk wanda ya yi yakini da mayewa to zai kyautata bayarwa".

133. Imam Ali (a.s) ya ce: "Taimako yana sauka gwargwadon bukata ne".

134. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya tsakaita a -rayuwa- ba zai yi talauci ba".

135. Imam Ali (a.s) ya ce: "Karancin Iyali dayan Yalwa ne guda biyu, Soyayyar (mutane) rabin hankali ne, Bakin ciki rabin tsufa ne". Nahajul Balaga: Hikima: 135.

136. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakuri yana sauka ne gwargwadon musiba, wanda kuwa ya buga hannunsa a kan cinyarsa gun wata musiba, hakika ya shafe ladansa".

137. Imam Ali (a.s) ya ce: "Sau da yawa mai azumin da ba shi da komai a azuminsa sai kishirwa, kuma da yawa mai tsayuwar sallar dare ba shi da komai sai wahala, madalla da baccin masu hankali da cin abincinsu!".

138. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku kiyaye imaninku da sadaka, ku kare dukiyoyinku da zakka, ku kare tunkudowar bala’i da addu’a". Nahajul Balaga: Hikima 138.

139. Daga cikin maganarsa da ya yi wa Kumail dan Ziyad anNakha'i. Kumail ya ce: Imam Ali as ya riki hannuna, sai ya fito da ni zuwa makabarta, yayin da ya kai sahara sai ya yi lumfashi mai tsawo sannan sai ya ce:

"Ya kai Kumail dan Ziyad, Hakika wannan zukata jaka ce, wacce ta fi su ita ce mafi kiyayewa, to ka kiyaye abin da nake gaya maka: mutane uku ne: Masani na Allah, da mai neman sani mai tsira, da kuma yuyar gayya masu bin duk wani mai kira, suna masu karkata tare da kowace iska, ba su haskaka da hasken ilimi ba, kuma ba su karkata zuwa ga wata madafa mai aminci ba".

Ya Kumail dan Ziyad, sanin ilimi addini ne da ake yi, da shi ne mutum yake samun biyayya a rayuwarsa, da kyawun taraswa bayan mutuwarsa, ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa.

Ya kai Kumail dan Ziyad, masu taskace dukiya sun mutum alhalin suna raye, malamai kuwa masu wanzuwa ne matukar zamani ya wanzu: Idanuwansu suna rasa –bacci- misalansu suna cikin zukata.

Lallai hakika a nan akwai tarin ilimi mai yawa –ya nuna kirjinsa- da ma na samu masu daukarsa! Sai da na samu masu saurin fahimta amma ba abin amincewa ba gareshi, wadanda suke amfani da addini a matsayin tsanin samun duniya, suna masu danne bayin Allah da ni'imarsa, da kuma danni masoyansa da hujjojinsa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai karkata zuwa ga rikon gaskiya amma ba shi da basira a tare da shi, shakku yana shiga zuciyarsa da zaran wata shubuha ta zo masa.

Ku sani babu wannan babu wancan! Ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, wadanda babu ruwansu da wani addini, abin da suka fi kusanci da shi su ne dabbobin kiwo! da haka ne sai ilimi yake mutuwa da mutuwar masu rike da shi.

Ya ubangiji haka ne! Babu wani lokaci da duniya zata zamanto babu mai tsayuwa da hujjar Allah, Imma dai zahiri mashahuri, ko mai jin tsoro mai boyuwa, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su baci.

Ya girman wancan -ina shi- ina wadancan? Wadancan wallahi! Su ne suka fi kowa karancin adadi, da girman daraja, da su ne Allah yake kiyaye dalilansa da ayoyinsa, har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu, ilimi ya zo musu a cikin hakikanin basira, suka kuma kusanci ruhin yakini, suka tausasa abin da masu shekewa suka tsaurara shi, suka samu nutsuwa da abin da jahilai suka samu dimauta da shi, kuma suka sahibanci duniya da jikinsu da rayukansu suna rataye da mahalli mafi dakaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganinsu!. -sannan sai imam Ali (a.s) ya ce masa juya (tafi) idan ka so-.

140. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutum boyayye ne karkashin harshensa".

141. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutumin da bai san kimarsa ba, ya halaka".

142. Imam Ali (a.s) ya ce da wani mutum da ya tambaye shi ya yi masa wa’azi: "Kada ka kasance daga wadanda suke neman lahira ba tare da aiki ba, suke jinkirta tuba da dogon buri, suke Magana game da duniya da fadin masu zuhudu, suke kuma aiki a cikinta da aikin masu neman lada. Idan an ba shi wani abu daga cikinta ba ya koshi, idan kuwa aka hana shi ba ya wadatuwa, yana kasa godewa kan abin da aka ba shi, kuma yana neman ba shi abin da ya yi ragowa, yana hanawa shi ba ya hanuwa, yana umarni amma shi ba ya aikatawa, yana son salihai amma ba ya aiki irin nasu, yana kin masu zunubi amma yana cikinsu, yana kin mutuwa saboda yawan zunubansa, yana kuma kana bin da yake kin mutuwa saboda shi, idan ya yi rashin lafiya sai ya yi ta nadama, idan ya samu lafiya sai ya shagaltu, yana jiji da kansa idan aka ba shi yalwa, yana yanke kauna idan aka jarrabe shi, idan bala’i ya same shi sai ya yi addu’a yana mai raki, idan kuwa yalwa ta same shi sai ya kawar da kai yana mai ji da kai, ransa tana rinjayarsa kan abin da yake tsammani, amma ba ya iya rinjayarta kan abin da yake da yakini, yana ji wa waninsa tsoro da abin da bai kai zunubinsa ba, yana so wa kansa ladan da ya fi karfin aikinsa. Idan ya samu yalwa sai ya yi girman kai ya fitinu, idan kuwa ya samu talauci sai ya yanke kauna ya yi rauni, yana takaitawa idan ya yi aiki, yana azuzutawa idan ya roka, idan wata sha’awa ta zo masa sai ya gaggauta sabo ya jinkirta tuba, idan kuwa wata jarabawa ta fado masa sai ya fita daga cikin tabbata da hakuri, yana siffanta abin lura –ga wasu- amma shi ba ya daukar darasi, yana zuzutawa a cikin wa’azi amma shi ba ya wa’aztuwa, shi mai surutu ne a magana, amma mai karanta aiki, yana ta gogoriyo da gasa a kan abin da yake karewa, yana mai sakaci da baya-baya kana bin da yake wanzuwa, yana ganin samu ramuwa, ramuwa kuwa samu. Yana jin tsoron mutuwa amma ba ya gaggauta samun dammar shirya mata, yana girmama sabon waninsa da abin da yake karanta abin da ya fi shi muni na sabonsa, kuma yana yawaita girmama da’arsa da abin da yake rena da’ar waninsa da shi. Shi dai mai sukan mutane ne, mai yabon kansa, wasa da masu kudi ya fiye masa ambaton Allah tare da talakawa. Yana yi wa waninsa hukunci –ya ba shi laifi- don amfanin kansa, amma ba ya yi wa kansa hukunci -da rashin gaskiya- don amfanin waninsa, yana shiryar da waninsa yana halakar da kansa, shi ana bin sa amma yana sabo, yana neman a cika masa shi ba ya cikawa, yana tsoron halitta ba don ubangijinsa ba, amma bay a tsoron ubangijinsa a kan halittarsa".

Muhammad Abduh yana cewa: Da babu wani abu a cikin wannan littafin sai wannan maganar da ta isa wa’azi mai amfani, da hikima mai balaga, da basira ga mai neman ganin haske, kuma darasi ga mai lura mai tunani.

143. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kowane mutum yana da karshe mai zaki ko mai daci".

144. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wani abu mai zuwa yana da komawa, kuma abin da ya koma ya juya baya kai ka ce bai kasance ba".

145. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai hakuri ba ya rasa rabauta ko da kuwa zamani ya tsawaita gareshi".

146. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai yarda da aikin wasu mutane kamar mai shiga cikinsu ne tare da su, kuma duk wani mai shiga cikinsu yana da zunubi biyu: Zunubin aiki da shi, da zunubin yarda da shi".

147. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku kiyaye alkawura gun ma'abotanta".

148. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku yi biyayya ga wanda ba a yi muku uzurin jahilcinsa".

149. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika an nuna muku idan kun nemi gani, kuma an shiryar da ku idan kun nemi shiryuwa, kuma an jiyar da ku idan kun nemi ji".

150. Imam Ali (a.s) ya ce: "Dora wa dan'uwanka nauyi da kyautata masa, ka kore sharrinsa da yi masa ni'ima".

151. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya jefa kansa wurin tuhuma, kada ya zargi wanda ya munana masa zato".

152. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi mallaka zai yi danniya,, wanda ya kayatar da ra'ayinsa zai halaka, wanda ya yi shawara da mazaje zai yi  tarayya da su a  hankulansu, wanda kuma ya boye sirrinsa to zabin yana hannunsa".

153. Imam Ali (a.s) ya ce: "Talauci shi ne mafi girman mutuwa".

154. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya biya hakkin wanda ba ya biyan hakkinsa to hakika ya bautar da shi".

155. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu biyayya ga abin halitta cikin sabon mahalicci".

156. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ba a aibata mutum da jinkirta hakkinsa, sai dai ana aibata wanda ya karbi abin da ba nasa ba.

157. Imam Ali (a.s) ya ce: "Jin kai yana hana neman daduwa".

158. Imam Ali (a.s) ya ce: "Lamarin kusa yake, ga abota kadan ce".

159. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika safiya ta waye ga mai idanuwa biyu".

160. Imam Ali (a.s) ya ce: "Barin yin zunubi ya fi neman tuba sauki".

161. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da yawa wani cin ya hana wasu cin".

162. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutane makiyan abin da suka jahilta ne".

163. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda ya fuskanci ra'ayoyi zai san inda kuskure yake".

164. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya wasa mashin fushi saboda Allah, to zai samu karfin rusa mafi tsananin barna".

165. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan ka ji tsoron wani lamari to ka fada masa, hakika tsananin kaffa-kaffa daga gareshi ya fi girman abin da kake ji na tsoro".

166. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yalwar kirji -hakuri- shi ne makamin jagoranci".

167. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka saka wa mai munanawa da ladan sakamakon mai kyautatawa".

Wato idan ka kyautatawa mai kyautatawa, to sai mai munanawa ya daina ya yi kyakkyawa domin shi ma a kyautata masa.

168. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka girbe sharri daga zuciyar waninka, ta hanyar cizge shi daga zuciyarka".

169. Imam Ali (a.s) ya ce: "Gaba -don bangaranci ba gaskiya ba- tana kawar da tunani".

170. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kwadayi bauta ce madawwamiya".

171. Imam Ali (a.s) ya ce: "Nadama ce sakamakon sakaci, aminci kuwa sakamakon himma ne".

172. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu alheri cikin yin shiru ga hukunci, kamar yadda babu alheri cikin yin magana da jahilci".

173. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu yadda wasu da'awowi biyu zasu saba, sai dayarsu ta kasance bata ce".

174. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ban taba kokwanton gaskiya ba tun da na gan ta".

175. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ban yi karya ba, ba a karyata ni ba, ban bata ba, ba a bata saboda -biyayyata- ba".

176. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai fara zalunci a gobe zai ciji tafinsa".  Ranar kiyama zai ciji yatsansa don nadama.

177. Imam Ali (a.s) ya ce: "Tafiya ta kusa".

178. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda ya bayyanar da fuskarsa -ya fito don gaba da- gaskiya ya halaka".

179. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda hakuri bai tseratar da shi ba, to raki zai halaka shi".

180. Imam Ali (a.s) ya ce: "Abin mamaki! a yanzu halifanci zai samu don sahabantaka, amma ba zai samu ba don sahabantaka da kusanci?".

An ruwaito wata waka tasa da wannan ma'ana kamar haka:

Idan dai da shura ne ka mallaki lamarinsu

To yaya haka alhalin masu shawarar ba sa nan*

Idan kuwa ka kafa hujja da kusanci ga mai jayayya

To waninka shi ya fi cancantar Annabi da kusanci *

181. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika mutum a wannan duniya karan bara ne da lokutan mutuwa suke harinsa su kafe cikinsa, abin hari ne da musibu suke gaggauta masa, a tare da kowace hadiyar ruwa akwai shaka, akwai kuma makalewa tare da kowace loma. Kuma bawa ba ya samun wata ni'ima sai ya bar wata, kuma ba ya fuskantar wata rana ta rayuwarsa sai ya rabu da wata zuwa ajalinsa. Mu 'yan'uwan mutuwa ne, kuma rayuka masu kafuwa cikin halaka ne, yaya kuwa -idan haka ne- zamu nemi wanzuwa alhalin ga dare da rana nan ba su taba daga wani abu sama ba sai sun gaggauta komowa don rusa abin da muka gina shi, da rarraba abin da muka hada shi".

182. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya kai dan Adam, duk abin da ka nema sama da karfinka, to kana tara shi ga waninka ne".

183. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika wannan zukata suna da sha'awa da gaba da baya, ku zo musu ta gaba".

184. Imam Ali (a.s) ya ce: “Yaushe ne zan huce daga bakin cikina idan na yi fushi? Shin a lokacin da zan kasa daukar fansa sai a ce mini da ka yi hakuri? Ko kuwa lokacin d azan kasa  ramawa sai a ce da ni: da ka yafe”.

185. Imam Ali (a.s) ya fada –a lokacin da ya wuce wata bola- sai ya ce: “Wannan shi ne abin da masu rowa suka yi rowarsa”. A wata ruwayar ya ce: “Wannan shi ne abin da kuke rigengentu a kansa jiya”.

186. Imam Ali (a.s) ya ce: “Abin da ya yi maka wa'azi bai tafi daga dukiyarka ba”. –Wato idan ya zama abin da ka kashe na dukiyarka ya yi maka wa'azi to ba ka yi asararsa ba don kashe shi, sannan muna iya fassara shi da cewa matukar abin da ka mallaka na dukiya ya yi maka wa'azi to ba zai tafi ba, domin kana da ladansa da ka kashe shi kan alheri-

187. Imam Ali (a.s) ya ce: “Hakika wadannan zukata suna kosawa kamar yadda jiki yake kosawa, don haka ku nema masu hikima mai dadi”.

188. Imam Ali (a.s) -yayin da ya ji fadin Hawarijawa cewa; Babu hukunci da mulki sai ga Allah sai ya ce:- “Kalmar gaskiya da ake nufin barna da ita”.

189. Imam Ali (a.s) -yana fada game da siffar wawaye da gabaye cewa-:  “Su ne wadanda idan suka hadu sai su yi galaba, idan kuwa suka watse ba a sanin su”. A wani kaulin kuma an ce, ya ce; "Su ne idan suka hadu sai su cutar, idan suka watse sai su yi amfani". Sai aka ce mun san cutarwar haduwarsu, to me ye amfani rarrabuwarsu da watsewarsu? Sai ya ce: "Masu sana'a zasu koma wa sana'arsu, sai mutane su amfana da su, kamar yadda mai gini yake koma wa gininsa, mai saka yake koma wa sakarsa, mai yin burodi zai koma wa aikin burodinsa".

190. Imam Ali (a.s) –yayin da aka zo masa da wani mahaukaci tare da shi akwai yuyar wawayen mutane sai ya ce: “Ba maraba ba, da fuskokin da ba a ganin su sai inda aka samu kowane irin abin kaico”.

191. Imam Ali (a.s) ya ce: “Hakika a tare da kowane mutum akwai mala'iku biyu da suke kare shi, idan kaddara ta zo sai su kyale shi da ita, kuma hakika ajali garkuwa ce mai kariya”.

192. Imam Ali (a.s) yayin da Dalha da Zubair suka ce masa: Zamu yi maka bai'a a kan mu kasance tare da kai cikin wannan lamarin na jagorancin jama'a, sai ya ce: “A'aha, sai dai ku kasance masu tarayya da ni a cikin karfi da taimako, masu agazawa a kan gajiya da wahala”.

193. Imam Ali (a.s) ya ce: “Ya ku mutane, ku ji tsoron Allah wanda idan kun fada zai ji, kuma idan kuka boye zai sani, ku gaggauta zuwa ga mutuwar da idan kun guje –mata- zata riske ku, idan kun tsaya zata rike ku, idan kun manta da ita zata tuna ku”.

194. Imam Ali (a.s) ya ce: “Kada wanda ba ya gude maka alheri –da kake yi- ya sanya karanta yin sa, ta yiwu wanda ba ya amfanar komai daga gareshi ya gode maka, kuma tayiwu ka samu -alheri- daga godiyar mai godewa fiye da abin da butulcin –rashin godiyar- mai butulci ya sanya ka rasa, (Kuma Allah yana son masu kyautatawa)”.

195. Imam Ali (a.s) ya ce: “Duk wata jaka tana yin kunci saboda abin da aka sanya cikinta sai jakar ilimi, ita tana dada fadi ne”.

196. Imam Ali (a.s) ya ce: “Farkon abin da mai hakuri yake samu sakamakon hakurinsa shi ne cewa mutane zasu kasance mataimakansa a kan jahilin –Mai wauta-”.

197. Imam Ali (a.s) ya ce: “Idan ba kasance mai hukuri ba, to ka nemi zama mai hakuri –wato ka yi kokarin yin sa-, domin da kyar ne zaka samu mutum bai yi kamata da mutane ba, sai ya kasance daga cikinsu”.

198. Imam Ali (a.s) ya ce: “Wanda ya yi wa ransa hisabi to ya rabauta, wanda kuwa ya gafala daga shi -ran nasa- to ya yi hasara, wanda ya ji tsoro ya aminta, wanda ya yi lura ya samu basira, wanda ya samu basira ya fadaka, wanda kuwa ya fadaka to ya samu ilimi”.

199. Imam Ali (a.s) ya ce: “Hakika duniya zata karkato -ta tausaya- mana bayan tutsunta -wato tsanantawarta a kanmu- kamar yadda rakuma mai hana nononta take tausaya wa danta”. Sannan sai ya karanta fadin Allah madaukaki: "Kuma muna son mu yi baiwa ga wadannan da aka zalunta a bayan kasa, mu sanya su jagorori, kuma mu sanya su masu gadewa".

200. Imam Ali (a.s) ya ce: “Ku ji tsoron Allah tsoron wanda ya daura damara, ya shirya sosai, ya kuma yi tafiya cikin lura, ya gaggauta cikin tsoro, ya yi duba cikin makomar matabbatarsa -wuta ko aljanna-, da karshen sakamakon aiki, da kuma abin da zai tarar a makoma -na ni'imar aljanna ko azabar wuta-”.

201. Imam Ali (a.s) ya ce: “Sakin hannu -da baiwar kyauta- shi ne mai kare mutunci, hakuri takunkumin wawa ne, rangwame zakkar rabauta ce, mantarwa -rufe idon- musanya ne ga wanda ya yi yaudara, neman shawara ainihin shiriya ne, kuma duk wanda ya wadatu da ra'ayinsa ya fada hadari, hakuri kuma yana maganin musibu, tsoro kuwa yana daga masu taimakawar zamani, mafi girman wadata shi ne barin buri, kuma da yawa wani hankali ya zama ribatacce karkashin sarautar wani son rai! Kiyaye tajriba -darasi- yana daga cikin dacewa, da soyayyar makusanta abar amfanuwa, kuma kada ka sake ka amincewa mai kasalarwa -mai sukarwa da sanya yanke kauna-”.

202. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mamakin mutun da jin kansa, shi daya daga cikin mahassadan hankalinsa ne".

203. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka rufe ganinka daga ganin kwantsa, da jin zafi, ka yarda har abada".

204. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda jikinsa -kamar jikin itaciya- ya yi taushi, to rassansa zasu yawaita.

205. Imam Ali (a.s) ya ce: "Sabani yana rusa ra'ayi".

206. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya samu ya nemi tsawaitawa -nuna daukaka da fifiko-".

207. Imam Ali (a.s) ya ce: "Sanin hakikanin mazaje yana cikin jujjuyawar halaye".

208. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yi wa aboki hassada yana daga abin da yake kawo raunin soyayya da kauna".

209. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi yawan wurin kaskantar hankali, yana cikin wuraren kwadayi".

210. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yin hukunci da amintuwa bisa zato, ba ya daga cikin adalci".

211. Imam Ali (a.s) ya ce: "Tir da guzurin lahira idan ya kasance gaba ne da zaluntar bayi".

212. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kau da kai daga abin da ya sani, yana daga cikin mafi daukakar ayyukan mutum mai daraja".

213. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda kunya ta sanya wa tufafinta, mutane ba zasu ga aibinsa ba".

214. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da yawaitar shuru ne zaka samu kwarjini, da yin adalci ne masoya suke yawaita, da yin falala ne daraja take girmama, da kaskan da kai ne ni'ima take cika, da kuma daukar nauyin ciyarwa ne shugabanci yake samuwa, da kyakkyawan halayen adalci ne ake cin nasara kan musibu, da hakuri daga wauta ne mataimaka suke yawaita".

215. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mamakin gafalar mahassada daga lafiyar jiki ya girmama!".

216. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai kwadayi yana cikin daurin igiyar kaskanci".

217. Imam Ali (a.s) ya fada a lokacin an tambaye shi game da imani sai ya ce: "Imani sani ne da zuciya, furuci ne da harshe, aiki ne da gabobi".

218. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya wayi gari yana bakin ciki a kan duniya to ya wayi gari yana mai fushi da kaddarar Allah ne, wanda kuma ya wayi gari yana mai kai kukan wata musiba da ta same shi, to hakika ya wayi gari ne yana kai kukan Ubangijinsa, wanda ya zo wa wani mawadaci sai ya rusuna masa saboda kudinsa, to ya tafiyar da sulusin addininsa, wanda ya karanta Kur'ani sai ya mutu ya shiga wuta, to shi ya kasance daga cikin wadanda suka riki ayoyin Allah da isgili ne, wanda kuwa zuciyarta ta furta da son duniya, to zuciyarsa zata damfaru da abubuwa uku: bakin ciki da ba ya rabuwa da shi, da kwadayin da ba zai bar shi ba, da buri da ba ya riskarsa".

219. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wadatar zuci ta isa ta zama mulki, kyakkyawan hali ya isa ya zama ni'ima".

220. Imam Ali (a.s) ya ce: "An tambaye shi game da fadinsa madaukaki (s.w.t) cewa: Zamu raya shi rayuwa mai dadi, sai ya ce: Ita ce wadatar zuci".

221. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku yi tarayya da wanda arziki ya zo masa, domin shi ne ya fi zama mafi dacewa ga wadatuwa, kuma mafi dacewa da gabatowar rabo gareshi".

222. Imam Ali (a.s) ya fada game da fadin Allah madaukaki (Hakika Allah yana umarni da adalci da kyautatawa) sai ya ce: "Adalci shi ne yin adalci -ga kawukan mutane- kyautatawa kuwa ita ce yin falala".

223. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya bayar da gajeren hannu za a ba shi da dogon hannu".

224. Imam Ali (a.s) ya ce da dansa Hasan (a.s): "Kada ka yi kira zuwa ga yaki, amma idan aka kira ka zuwa gareshi ka amsa, domin mai kira mai shisshigi ne, mai shisshigi abin kayarwa ne".

225. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zababbun dabi’un mata shi ne munanan dabi’un maza, jin kai, da tsoro, da rowa; idan mace ta kasance mai girman kai bat a yarda ta bayar da kanta ga wani, idan kuwa tana da rowa sai ta kare dukiyarta da dukiyar mijinta, kuma idan ta kasance mai tsoro sai ta ji tsoron komai da yake kawo mata hari".

226. An ce da Imam Ali (a.s) siffanta mana mai hankali? Sai ya ce: "Shi ne wanda yake sanya komai mahallinsa". Sai aka ce masa: Siffanta mana jahili? Sai ya ce: "Ai na yi".

227. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wallahi wannan duniyar taku ta fi muni a idanuna fiye da gumin alade a hannun kuturu".

228. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika wasu mutane sun bauta wa Allah domin kwadayi, to wannan ibadar ‘yan kasuwa ke nan, wasu kuwa sun bauta wa Allah don tsoro, to wannan ita ce ibadar bayi ke nan, wasu kuwa sun bauta wa Allah domin godiya, to wannan ita ce ibadar ‘yantattun bayi".

229. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mace sharri ce dukkanta, sharrin da yake cikinta shi ne babu makawa daga gareta!".

230. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya bi lalaci to zai tozarta hakkoki, wanda kuwa ya bi mai yada jita-jita zai rasa aboki".

231. Imam Ali (a.s) ya ce: "Dutse daya na kwace a -ginin- gida, ya isa ya rusa shi".

232. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ranar abin zalunta a kan azzalumi ta fi tsanani a kan ranar azzalumi a kan abin zalunta".

233. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka ji tsoron Allah wani jin tsoro komai karancinsa, ka sanya sitira tsakaninka da Allah ko mai rasha-rashanta".

234. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan amsa ta cakushe, sai gaskiya ta boyu".

235. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika Allah yana da hakki a kan kowace ni’ima, duk wanda ya bayar da ita, sai ya dada masa, wanda kuwa ya hana ta to lallai ya fada hadarin gushewar ni’imarsa".

236. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan iko –shugulgula- suka yawaita, sai sha’awa ta karanta".

237. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku ji tsoron gujewar ni’ima (ni’ima ta kau saboda sakaci), domin ba duk abin da ya tsere ba ne yake dawowa".

238. Imam Ali (a.s) ya ce: "Karimci ya fi kusanci tausayawa".

239. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi maka kyakkyawan zato, to ka gaskata zatonsa".

240. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi kyawun ayyuka shi ne abin da ka tilasta kanka a kan yinsa".

241. Imam Ali (a.s) ya ce: "Na san Allah ne ta hanyar bata matakai, da warware niyyoyi".

242. Imam Ali (a.s) ya ce: "Dacin duniya shi ne zakin lahira, zakin duniya shi ne dacin lahira".

243. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah ya farlanta imani domin tsarkake mutane daga shirka, salla kuwa domin tsarkakewa daga girman kai, zakka kuwa domin jawo arziki, azumi kuwa domin jarraba ikhlasin bayi, hajji kuwa domin kusantar addini, jihadi kuwa izzar musulunci ne, umarni da kyakkyawa maslahar al’umma ne, hani daga mummuna kariya daga wawaye ne, sadar da zumunci kuwa mai kara zuriya ne. Kisasi kuwa domin kare jinni, tsayar da haddi domin girmama mutuncin hurumi, barin shangiya kuwa domin kariya ga hankali, nisantar sata kuwa domin samar da kame kai, barin zina kuwa domin kiyaye nasaba, barin luwadi kuwa domin yawaita zuriya, sheda kuwa domin fito da abin da aka yi musu, barin karya kuwa domin daukakawa ga gaskiya, aminci kuwa domin kubuta daga tsoro, jagoranci kuwa domin tsarin al’umma, biyayya kuwa domin girmama jagoranci ne".

244. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku rantsar da azzalumi idan kuna son rantsuwarsa da cewa shi ya barranta daga dubarar Allah da karfinsa, domin idan ya rantse da haka yana mai karya to za a gaggauta masa ukuba. Domin kuwa idan ya rantse da Allah wanda babu wani abin bauta sais hi to ba za a gaggauta masa ita ba, domin ya kadaita Allah ne".

245. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya kai dan Adam, ka kasance mai yi wa kanka wasiyya, kuma ka yi aiki da dukiyarka da abin da zaka so a yi da ita bayan wucewarka".

246. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kaifin -zafin- zuciya wani nau’i ne na hauka, domin mai shi yana nadama, idan kuwa bai yi nadama ba, to haukansa ya yi karfi ke nan".

247. Imam Ali (a.s) ya ce: "Lafiyar jiki tana daga karancin hassada ne".

248. Imam Ali (a.s) ya ce da Kumail dan Zaiyad anNakah’i: "Ya Kumail ka umarci iyalanka su yi tafiya zuwa ga neman kyawawan halaye, su kuma kutsa cikin biyan bukatar mabukaci, domin na rantse da wanda jinsa ya yalwaci duk sautoci, babu wani mutum da zai sanya farin ciki cikin wata zuciya sai Allah ya halitta masa wani ludufi sakamakon wannan farin cikin, idan kuwa wata fitina ta fado masa zai yi tafiya a kanta kamar yadda ruwa yake gudana yayin kwararowarsa har sai ya kore ta daga gareshi kamar yadda ake kore bakon rakumi ".

249. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan kuka yi talauci to ku yi ciniki da Allah da yin sadaka".

250. Imam Ali (a.s) ya ce: "Cikawa ga mayaudara yaudara ne a gun Allah, yaudarar masu yaudara cikawa ne gun Allah".

251. Imam Ali (a.s) ya ce: "Sau da yawa aka yi wa wani shigo ba zurfi da kyautata masa, da kuma wani mai rudin kansa da aka suturta masa, da wanda aka fitina da fadin kyakkyawan zance kansa, babu wani mutum da Allah ya jarraba da wani abu kamar cika baki wurin yabonsa".

252. Yayin da labarin harin da mutanen Mu’awiya suka kai garin Anbar ya zo masa sai Imam Ali (a.s) ya fito da kansa yana tafiya a kasa har sai da ya isa Nukhaila, sai mutane suka riske shi a wurin suka ce: Ya Kai shugaban musulmi, mu mun ishe su. Sai ya ce: "Wallahi ba kwa iya kare mini kawukanku, to yaya kuwa zaku kare mini waninku? Saud a yawa al’umma take kuka da jagororinta, amma ni a yau ni ne nake kuka da al’ummata. Kai ka ce ni ne wanda ake jagoranta su kuwa su ne jagorori, ko kuwa masu hukunci ni kuma abin hukuntawa ".

(yayin da ya fadi wannan Magana mai tsayi ce da ya yi ta, sai wasu mutane biyu daga sahabbansa suka yo gaba, sai dayansu ya ce: Ni ban a mallaka sai dai kaina da dan’uwana, ka ba mu umarninka ya kai jagoran muminai zamu yi fansa da rayukanmu gareshi. Sai (a.s) ya ce: Yaya kuwa zaku iya yin abin da nake so?.

253. An ce: Haris dan Haud ya zo masa (a.s) sai ya ce: Yanzu kana ganin ina zaton ma’abota rakumi suna kan bata ne?

Sai Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya kai Hari! Da ka duba kasanka ba ka duba samanka ba, sai ka fada dimuwa! Kai ba ka san gaskiya ba balle ka san ma’abotanta, ba ka san bata ba balle ka san wanda ya zo masa. Sai Haris ya ce: Ni na bar kowane bangare ne kamar yadda Sa’id dan Malik, da Abdullahi dan Umar suka yi ne. Sai Imam Ali (a.s) ya ce masa: Sa’id da Abdullah ba su taimaki gaskiya ba, kuma ba su ki barna ba".

254. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai sarauta kamar mahayin zaki ne, ana burin matsayinsa, alhalin shi ne ya fi sanin matsayin da yake".

255. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku kyautata ga abin da wasu suka bari, kuma sai a kyautata wa abin da kuka bari".

256. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zancen masu hikima idan ya kasance daidai ne, to sai ya kasance magani, amma idan ya kasance kuskure ne sai ya kasance cuta".

257. Wani mutum ya tambayi Imam Ali (a.s) ya gaya masa mene ne imani sai ya ce:

"Sai ya ce masa ka zo mini gobe domin in gaya maka mutane suna ji, idan ka manta Maganata to wani ya kiyaye maka ita, ka sani Magana kamar korarren dabba ce da wani yake rasa ta, wani kuma ya same ta".

(an fadi abin da ya gaya masa wanda yake game da rassan imani sai a koma domin dubawa).

258. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya kai dan adam, kada ka dora bakin cikin ranar dab a ta zo maka ba, a kan na ranar da ta zo maka, domin idan dai ka rayu, to Allah zai zo maka da arzikinka".

259. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka so masoyinka da sauki, tayiwu ya kasance makiyinka kwarai a wata rana, kuma ka ki makiyinka da sauki, ta yiwu ya kasance masoyinka kwarai wata rana".

260. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutane a duniya masu aiki biyu ne: Mai aiki da yake aiki domin duniya, kuma aikinsa ya shagaltar shi daga lahirarsa, yana jin tsoron kada talauci ya mamaye shi, yana kuma amintuwa ga kansa, sai ya karar da rayuwarsa a cikin amfanin waninsa.

Da mai aikin da yake aikin a duniya don abin da zai zo bayanta, sai abin da yake duniya ya zo masa ba tare da wani aiki ba, sai ya samu duka rabo biyu tare, ya mallaki gidaje biyu, sai ya wayi gari yana mai daraja da kima gun Allah, ba ya tambayar Allah wata bukata ya hana shi ita".

261. An ruwaito cewa an ambaci adon Ka’aba gun Umar dan Khaddabi da yawan –tsadarsa- sai wasu mutane suke ce: Da dai ya rike shi sai ya yi wa rundunar musulmi kayan yaki das hi da ya fi lada, me Ka’aba zata yi da wani ado? Sai Umar ya yi niyyar yin hakan, sai ya tambayi Imam Ali (a.s) kan lamarin.

Sai Imam Ali (a.s) ya ce:

"Hakika Kur’ani ya sauka ga annabi (s.a.w) kuma dukiya guda hudu ce: Dukiyar Musulmi sai ya raba ta tsakanin magada a cikin gado, da kuma Fai’u, sai ya raba tag a masu cancanta, da Humusi, sai ya sanya shi inda Allah ya ce ya sanya shi, da kuma sadakoki, sai ya sanya su inda ya sanya su. Kuma adon Ka’aba ya kasance yana daga ciki a wannan zamanin, kuma Allah ya bar shi kamar yadda yake bisa halinsa, bai bar shi don mantuwa ba, kuma wani wuri bai boyu gareshi ba, ka bar shi yadda Allah da manzonsa suka bar shi (suka tabbatar da shi)".

Sai Umar ya ce masa: Ba don kai ba, da mun kunyata, sai ya bar adon kamar yadda yake.

262. An ruwaito cewa an kawo masa wasu mutane guda biyu da suka saci dukiyar Allah, dayansu bawa ne daga dukiyar Allah, daya kuma bawan wasu mutane ne.

Sai Imam Ali (a.s) ya ce: "Amma wannan shi dukiyar Allah ce babu haddi kansa, dukiyar Allah ce da wata ta cinye wata, amma dayan akwai haddi kansa, sai ya yanke hannunsa".

263. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da kafafuna sun daidaita a kan wadannan fitintinu da na canja abubuwa".

264. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku sani sanin yakini cewa Allah bai sanya wa bawa (komai girman dubararsa, da tsananin nemansa, da karfin makircinsa) fiye da abin da ya raba masa a cikin Ambato mai hikima ba. Kuma bai shiga tsakanin bawa duk da rauninsa da karancin dubararsa ba da kaiwa ga abin da aka sanya masa a cikin Ambato mai hikima ba. Masani ga wannan mai aiki das hi shi ya fi kowa hutu cikin amfanuwa a cikin mutane, kuma mai barin sa, mai kokwanto a cikinsa shi ya fi kowane mutum shagaltuwa cikin cutuwa. Saud a yawa wanda aka yi wa ni’ima aka yi masa shigo ba zurfi a cikin abin ni’ima, kuma sau da yawa wanda aka jarraba wanda aka yi shi da bala’o’i! to ka kara godiyarka ya kai mai ji, ka takaita cikin gaggawarka, ka dakata gun iyakacin arzikinka".

265. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ku sanya ilminku jahilci, kuma yakininku shakku, idan kuka sani to ku yi aiki, kuma idan kuka yi yakini sai ku gabatar".

266. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika kwadayi shigar sa ake yi ba a fita (daga halakarsa), kuma mai lamuncewa ne ba mai cikawa ba. Kuma da yawa mai shan ruwa ya shake kafin ya koshi, kuma duk sa’adda girman darajar abin da ake rige saboda shi ta girmama, to sai musibar rashinsa ta girmama. Burace-burace suna makantar da zukata ne, amma rabo yana zo wa wanda ba ya zo masa ne".

267. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ubangiji! Ni ina neman tsarinka daga kyautatar zahiri na a cikin idanuwa, kuma badinina da nake boye maka ya munana, ina mai kiyayewa kan riya ga mutane da dukkan abin da kake saninsa daga gareni, sai kuma in bayyanar maka da zahirina, kuma in zo wurinka da mummunan aikina, ina mai neman kusanci zuwa gareka, ina mai nisantar yardarka".

268. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wallahi na rantse da wanda muke yammanci saboda shi a cikin ragowar duhun dare mai tsanani, muke wayewar gari da rana mai haske, abu kaza bai kasance abu kaza ba".

269. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kadan da kake dawwama kansa, shi ya fi mai yawan mai kosarwa".

270. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan nafilfili suka cutar da farillai, to ka guje su".

271. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya tuna kafin ya yi tafiya, to ya shirya".

272. Imam Ali (a.s) ya ce: "Amfani da hankali bai kasance kamar gani da idanu ba, tayiwu idanuwa su yi wa masu su karya, amma hankali ba ya yaudarar wanda ya yi wa nasiha".

273. Imam Ali (a.s) ya ce: "Tsakaninku da wa’azai akwai wani shamaki na gafala".

274. Imam Ali (a.s) ya ce: "Jahilinku mai shisshigi ne, masaninku kuwa mai jinkirtarwa ne".

275. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ilimi ya yanke uzurin masu kawo hanzari".

276. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda aka gaggautawa yana neman a saurara masa ne (zuwa wani lokaci) kuma duk abin jinkirtawa da saurarawa yana kawo dalilin sai wani lokaci ne".

277. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutane ba su ce wa wani abu madalla da shi ba, sai zamani ya tanadar masa wata rana mai muni".

278. An tambayi Imam Ali (a.s) game da kaddara, sai ya ce: "Hanya ce mai duhu kada ku shige ta, kuma kogi ne mai zurfi kada ku kutsa masa, kuma sirrin Allah ne kada ku kallafa wa kawukanku".

279. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan Allah ya kaskantar da bawa sai ya hana shi ilimi".

280. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da ina da wani dan’uwa aboki don Allah, kuma ya kasance karancin duniya a gunsa yana girmama shi a idanuwana, ya kasance ya fita daga ribacewar nan ta cikinsa, ba ya sha’awar abin da bai samu ba, kuma ba ya yawaita abin da ya samu, ya kasance mafi yawancin lokutansa mai shiru ne, idan kuwa ya yi Magana, sai ya yi fice ga masu Magana, ya kashe kishirwar masu tambaya, kuma ya kasance mafi yawan lokutansa shi mai rauni ne abin raunatawa! Idan kuwa yaki ya zo to shi ne zakin jeji, kuma macijin kwararo, ba ya kawo hujjarsa sai ya yanke dukkan wata hujja, kuma ya kasance ba ya zargin kowa kan abin da yake samun uzuri a irinsa har sai ya ji hanzarinsa, ya kasance ba ya kukan wani ciwo sai gun inda za a warkar das hi, ya kasance yana fadar abin da yake yi, ba ya fadar abin dab a ya yi, kuma ya kasance idan an yi galaba kansa kan yin Magana, to ba a galaba kansa kan yin shiru, kuma ya kasance ya fi kwadayin ya ji fiye da ya yi Magana, kuma idan wasu abubuwa biyu suka zo masa bagatatan, sai ya duba wanne ne ya fi kusa da son rai sai ya saba masa.

Na umarce ku da wadannan halaye ku lizimce su, ku yi rige a cikinsu, idan kuwa ba zaku iya ba, to ku sani yin kadan ya fi barin mai yawa".

281. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ba don Allah ya yi alkawarin azaba ga saba masa ba, da bai kamata a saba masa ba, don godiya ga ni’imarsa".

282. Imam Ali (a.s) ya ce: -a lokacin yana yi wa Ash’(a.s) dan Kais ta’aziyyar wani dansa- "Ya kai Ash’(a.s), idan ka yi bakin ciki a kan danka, hakika ya kusanci ya cancanci hakan daga gareka, amma idan ka yi hakuri to Allah yana maye gurbin kowace musiba, ya kai Ash’(a.s)! Idan ka yi hakuri sai kaddara ta gudana gareka kana abin ba wa lada, idan kuwa ka yi raki, sai kaddara ta gudana a kanka kuma kana mai zunubi, danka sirrinka ne, kuma shi bala’I ne da fitina da bakin cikinka, kuma shi lada ne da rahama".

283. Imam Ali (a.s) ya ce: -a gun kabarin annabi (s.a.w) yayin binne shi- "Hakika hakuri yana da kyau sai game da kai, kuma raki mummuna ne sai don kai, kuma hakika musibar rashinka mai girma ce, kuma shi kafinka da bayanka mai girma ne".

284. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka yi abota da wawa, domin shi yana kawata maka aikinsa, kuma yana son ka kasance misalinsa".

285. Imam Ali (a.s) ya ce: -an tambaye shi game da nisan da yake tsakanin gabas da yamma- "Tafiyar wuni ga rana".

286. Imam Ali (a.s) ya ce: "Masoyanka uku ne, makiyanka uku ne: Masoyanka: Masoyinka, da masoyin masoyinka, da makiyin makiyinka. Amma makiyanka su ne: Makiyinka, da makiyin masoyinka, da masoyin makiyinka".

287. Imam Ali (a.s) ya ce: -da wani mutum da ya gan shi yana kokkrin taimakon wani makiyinsa da abin da zai cutar da shi: - "Kai dai kamar mai sukan kansa ne (da makami), domin ya kashe wanda ya goya".

288. Imam Ali (a.s) ya ce: "Akwai yawan darussa matuka, sai dai akwai karancin daukar darussa matuka".

289. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya wuce gona da iri wurin gaba to ya yi sabo, wanda ya takaita kuwa ya yi zalunci, Kuma mai yin husuma ba ya iya jin tsoron Allah".

289. :   .

290. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wani sabo da aka jinkirta mini bayan yin sa bai bata mini rai ba, sai na yi salla raka’a biyu. (na roki Allah lafiya)".

291. An tambayi Imam Ali (a.s) game da yaya Allah yake yin hisabin halitta duk da yawansu? sai ya ce: "Kamar yadda yake arzuta su suna da yawa". Sai aka ce masa: Yaya zai yi musu hisabi kuma bas a ganin sa? Sai ya ce: "Kamar yadda yake arzuta su, kuma ba sa ganin sa".

292. Imam Ali (a.s) ya ce: "Manzon da aka aiko maka, shi ne mai bayanin hankalinka, kuma littafinka shi ne ya fi komai bayani game da kai".

293. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda aka jarraba da bala’i mai tsanani ba shi ne ya fi bukatar addu’a ba fiye da wanda yake mai lafiya wanda ba ya amintuwa daga bala’i!".

294. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutane ‘ya’yan duniya ne, kuma ba a zargin mutum kan son uwarsa".

295. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika miskini shi ne annabi (s.a.w), duk wanda ya hana shi to ya hana Allah ne, kuma duk wanda ya ba shi ya ba wa Allah ne".

296. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai kishi bai taba yin zina ba".

297. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ajali ya ishi mutum zama mai gadi!".

298. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutum yana bacci a kan rasa ‘ya’ya, amma ba ya bacci a kan wawasun (dukiya)".

Ma’anar hakan shi ne yana hakuri kan kasha ‘ya’ya, amma ba ya hakuri kan kwace masa dukiyoyi.

299. Imam Ali (a.s) ya ce: "Soyayya tsakanin iyaye, kusanci ne tsakanin ‘ya’ya, kusanci ya fi bukatar soyayya fiye da yadda soyayya take bukatar kusanci".

300. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku ji tsoron zaton muminai, Hakika Allah madaukaki ya sanya gaskiya kan harshensu".

301. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ba a gaskata imanin bawa, har sai ya kasance ya fi nutsuwa da abin da yake hannun Allah fiye da abin da yake hannunsa".

302. Imam Ali (a.s) ya ce wa Anas dan Malik, lokacin da ya aike shi zuwa ga Dalha da Zubair yayin da suka zo Basara, domin ya gaya musu wani abu da ya ji daga manzon Allah (s.a.w) game da su, sai Anas ya dawo ya ki zuwa, ya koma wa Imam Ali (a.s) ya ce: Ni na manta wannan lamarin (da annabi ya fada). Sai imam Ali (a.s) ya ce: "Idan dai karya kake yi (da ka ce ka manta alhalin ba ka manta ba) to Allah ya jarrabe ka da kuturta mai walwalniya a fuskarka, rawaninka bai isa ya boye tab a". (Sai kuwa kuturta ta samu Anas da wannan addu’a a fuskarsa, koda yaushe yana kokarin rufe ta da wani mayafi a kansa).

303. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zukata suna da gabatowa da juya baya, idan suka gabato sai ku yi ta nafilfili, amma idan kuwa suka juya baya, sai ku takaitar das u kan yin farilloli".

304. Imam Ali (a.s) ya ce: "A cikin Kur’ani akwai labarin magabatanku, da labarin na bayanku, da hukuncin abin da yake tsakaninku".

305. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku mayar da dutse ta inda ya zo, hakika sharri ba abin da yake kare shi sai sharri".

(Wannan zai kasance ne idan an kasa raddin mai sharri ta hanyar alheri).

306. Imam Ali (a.s) ya ce da sakatarensa Ubaidullah dan Abi Rafi’u: "Sanya tawadarka, ka tsawaita fikar alkalaminka, ka rarraba tsakanin sadarori, ka matse tsakanin haruffa, wannan ne ya fi dacewa da kyawun rubutu".

307. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ni ne jagoran muminai, dukiya kuwa jagoran fajirai".

308. Wasu yahudawa sun ce wa Imam Ali (a.s): Ba ku binne annabinku ba har sai da kuka yi sabani kansa! Sai ya ce: "Ba mu yi sabani a kansa ba, sai dai kan abin da ya bari. Amma ku kafafunku ma ba su bushe ba daga kogin da kuka ketare har sai da kuka ce da annabinku: "Sanya mana Ubangiji kamar yadda suke da gunki, sai ya ce: Ku dai mutane ne masu jahilci".

309. An ce wa Imam Ali (a.s) da me ka yi galaba kan abokan yaki? Sai ya ce: "Ban taba haduwa da wani mutum ba har sai ya taimaka mini a kansa". (wato tun kafin mu hadu sai ya samu jin tsorona da kwarjini na a zuciyarsa).

310. Imam Ali (a.s) ya ce da dan Muhammad dan Alhanafiyya: "Ya kai dana! Ni ina ji maka tsoron talauci, ka nemi tsarin Allah daga gareshi, domin talauci tawaya ce ga addini, mai dimautar da hankali ne, mai jawo kiyayya ne!".

311. Imam Ali (a.s) ya ce da wani mai tambaya kan lamurra masu wuyar sha’ani: "Ka yi tambaya don neman sani, kada ka yi tambaya don shisshigi, domin jahili mai neman sani yana kama da malami ne, haka nan malami mai ??????? yana kama da jahili mai shisshigi".

312. Imam Ali (a.s) ya ce da Abdullahi dan Abbas yayin da ya yi masa nuni da wani abu da bai yi daidai da ra’ayinsa ba: "Kai naka shi ne ka ba ni shawara ni kuma in gani, amma idan na saba maka sai ka bi ni".

313. An ruwaito cewa yayin da Imam Ali (a.s) ya shiga Kufa yana mai dawowa daga Siffain, sai ya wuce wani wuri Shabamiyyin, sai ya ji kukan mata kan wadanda aka kasha a Siffain, kuma Harb dan Shurahbil Asshabbami wanda ya kasance daga shugabannin yankin ya zo wurinsa. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: "Ashe matanku suna rinjayarku kamar yanda nake ji? Ashe ba zaku hana su wannan gunjin ba?". Sai ya zo yana tafiya a kasa tare da Imam Ali (a.s), shi kuwa yana kan dokinsa. Sai Imam Ali (a.s) ya ce masa: "Koma, tafiyar misalinka a kasa tare da misalina fitina ce ga jagora, kuma kasakanci ne ga mumini".

314. Imam Ali (a.s) ya wuce wasu da aka kasha daga Khawarijawa ranar Nahrawan sai ya ce: "Kaiconku, wanda ya yaudare ku, ya cuce ku". Sai aka ce masa waye ya yaudare su ya sarkin muminai? Sai ya ce: "Shedan mai batarwa, da rayuka masu umarni da mummuna, burace-burace sun yaudare su, kuma sabo ya buda musu hanya, nuna kai ya yi musu alkawarin wofi, sai suka jefa su wuta".

315. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku ji tsoron Allah a boye, domin mai sheda shi ne mai hukunci".

316. Yayin da labarin kasha Muhammad dan Abubakar ya zo wa Imam Ali (a.s) sai ya ce: "Hakika bakin cikinmu a kansa yana gwargwadon farin cikinsu da haka ne, sai dai su sun rasa makiyi, mu kuma mun rasa masoyi".

317. Imam Ali (a.s) ya ce: "Shekarun da Allah yake yanke hanzari ga dan adam da su, su ne shekaru sittin".

318. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda sabo ya rabauta da shi bai rabauta ba, wanda kuma ya yi rinjaye da sharri shi abin rinjaya ne".

319. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika Allah madaukaki ya wajabta wa masu dukiya abincin talakawa daga dukiyarsu, babu wani talaka da zai ji yunwa, sai da abin da mai kudi ya hana ne, kuma Allah zai taimake su game da wannan".

320. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wadatuwa daga uzuri, shi ya fi girma daga gaskatawa da shi".

321. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi karancin abin da Allah yake wajabta muku shi ne kada ku nemi taimako da ni’imominsa a kan saba masa".

322. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika Allah madaukaki ya sanya biyayya a matsayin ganimar masu hankali yayin shisshigin masu gajiyawa (masu raunin zukata saboda sha’awarsu)".

323. Imam Ali (a.s) ya ce: "Shugabanni su ne masu taimakon hukuncin Allah a bayan kasa".

324. Imam Ali (a.s) yana fada game da siffofin mumini cewa: "Mumini farin cikinsa yana fuskarsa, bakin cikinsa yana zuciyarsa, yana da mafi yalwar kirji (hakuri), mafi kaskan da kai, yana kin a daga shi, yana kyamar jiyarwa, bakin cikinsa mai tsayi ne, tunaninsa mai nisa ne, shirunsa mai yawa ne, lokacinsa mai shagaltuwa ne, mai godiya, mai juriya, mai shagaltuwa da tunaninsa, mai boye bukatuwarsa ne, mai saukin dabi’a, mai taushin hali, ransa ta fi dutse tsauri, kuma shi ya fi bawa kaskantar da kai".

325. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da bawan ya ga ajalin da yadda yake zuwa, da ya ki buri da rudinsa".

326. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kowane mutum yana da masu tarayya biyu a cikin dukiyarsa: Mai gado, da abubuwan da suke faruwa yau da gobe".

327. Imam Ali (a.s) ya ce: "Abin tambaya mai zabi ne, har sai ya yi alkawari".

328. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai kira ba tare da aiki ba, kamar mai harbi ne babu baka".

329. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ilimi guda biyu ne: mai shiga jiki da na ji, kuma na ji ba shi da amfani idan bai shiga jiki ba".

330. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kyawun ra’ayi da yalwa ne, idan ta gabato sai ya gabato, idan ta tafi sai ya tafi".

331. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kame kai shi ne adon talauci, kuma godiyar wadata ne".

332. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ranar adalci a kan azzalumi, ta fi tsanani fiye da ranar zalunci a kan wanda aka zalunta".

333. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi girman wadatuwa ita ce yanke kauna daga abin da yake hannun mutane".

334. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zantuttuka abin kiyayewa ne, sirrori abin jarrabawa ne, kuma "Kowace rai za a jingina mata abin da ta yi", mutane abin tauyewa (hankali) ne, masu matsalar halayen zuci, sai dai wanda Allah ya kare, mai tambayarsu mai shisshigi ne, mai amsa musu mai kallafawa kai ne kawai, mafi kyawunsu ra’ayi yana kusan ya kasance yarda da fushi suna mayar da shi daga kyawun ra’ayinsa, kuma mafi karfinsu riko da addini kallon sha’awa yana zubar da hawayensa yana sanya masa miki, kuma kalma daya tana iya canja shi daga abin da yake kansa.

Ya ku Mutane! Ku ji tsoron Allah, sau da yawa mai burin da ba ya iya isa ga burinsa, kuma abin da yake zaune cikinsa ya nisanta, kuma ya tara abin da zai bari, tayiwu ya tara shi ta hanyar banza ne, ko wani hakki da ya hana ne, ya same shi ta hanyar haram, ya dauki zunubansa, sai ya koma da zunubansa, ya zo wurin ubangijinsa yana mai jin takaici da haushin kansa, (ya rasa duniya da lahira, lallai wannan ita ce hasara bayyananniya)".

335. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da isma ne sabo yake koruwa??????".

336. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ruwan fuskarka sandararre ne, roko ne yake sanya shi digowa, ka duba wanda zaka digo da shi gunsa".

337. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yabo sama da cancanta maula ce, kuma takaita yabo ga mai cancanta gajiyawa ce ko hassada".

338. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi munin zunubi shi ne wanda mai yinsa ya karanta shi".

339. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya duba aibin kansa zai shagaltu daga aibin waninsa, wanda kuwa ya yarda da arzikin Allah ba zai yi bakin ciki a kan abin da ya kubuce masa ba, wanda kuwa ya wasa takobin shisshigi to za a kasha shi da ita, wanda kuwa ya yi wa abubuwa shigar burtu to zai kasa ya gajiya, wanda ya shiga zurfafan lokuna to zai nutse a ciki, wanda ya shiga mashigar muni za a tuhumce shi, kuma wanda maganarsa ta yawaita to kuskuransa zai yawaita, wanda kuwa kuskurensa ya yawaita to kunyarsa zata karanta, wanda kuwa kunyarsa ta karanta kaskan da kansa zai karanta, wanda kuwa kaskan da kansa ya karanta zuciyarsa zata mutu, wanda kuwa zuciyarsa ta mutu zai shiga wuta, wanda kuwa ya duba aibobin mutane sai ya munana su sannan ya yarda da kansa to wannan shi ne ainihin wawa. Wadatar zuci dukiya ce maras karewa, wanda ya yawaita tuna mutuwa sai ya yarda da kadan daga duniya, wanda ya san cewa zancansa daga aikinsa ne to zancensa zai karanta sai kan abin da yake da ruwansa".

340. Imam Ali (a.s) ya ce: "Azzalumi daga maza yana da alamomi uku: Yana zaluntar na samansa da sabawa, na kasansa kuwa da nuna karfi, sannan yana taimakon mutane azzalumai".

341. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yayin da tsanani ya kare ne ake samun farin ciki, kuma yayin da mamayar bala’i ta yi kunci sai a samu yalwa".

342. Imam Ali (a.s) ya ce da wani sahabinsa: "Kada ka sanya mafi yawan shugulin zuciyarka ya kasance na iyalinka da ‘ya’yanka: Idan iyalinka da ‘ya’yanka sun kasance daga masoya Allah, to Allah ba zai tozarta masoyansa ba, idan kuwa sun kasance daga makiya Allah ne, to me ye naka na bakin cikinka da shagaltuwarka da makiya Allah?!".

343. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi munin aibi shi ne aibata abin da kai ma kana da irinsa".

344. Wani mutum ya taya wani murna saboda wani da da ya samu ya ce masa: Alfaris yana taya ka murna. Kuma Imam Ali (a.s) yana wurin, sai ya ce: "Kada ka ce haka, sai dai ka ce: Ka gode wa mai bayarwa Allah, kuma Allah ya sanya maka albarka cikin abin da aka ba ka, ya sanya shi ya girma, ya arzuta ka tarbiyyarsa".

345. Wani mutum daga ma’aikatansa ya gina wani gida mai girma, sai Imam Ali (a.s) ya ce: "Azurfa ta bayyana a nan! Kuma ginin yana nuna wadatarka ne".

346. An ce wa Imam Ali (a.s): Da za a toshe wa wani mutum kofar gidansa, a bar shi a ciki, yaya arzikinsa zai zo masa ne? sai ya ce: "Ta inda ajalinsa yake zo masa".

347. Imam Ali (a.s) ya yi wa wasu mutane ta’aziyyar wani mamaci nasu, sai ya ce: "Wannan lamarin bad a ku ya fara ba, kuma ba zai kare da ku ba, wannan mamacin naku ya kasance yana yin tafiye-tafiye da ma, to ku sanya wannan daya daga cikin tafiye-tafiyensa ce, idan ya dawo shi ke nan, idan kuwa bai dawo ba to ku zaku je ku same shi".

348. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya ku mutane! Allah ya gan ku masu jin tsorn ni’ima kamar yadda yake ganin ku masu jin tsoron azaba! Ku sani duk wanda aka yalwata masa arzikinsa kuma bai ga wannan a matsayin shigo ba zurfi ba, to ya amintu daga abin tsoro ne, wanda kuwa aka kuntata masa arzikinsa, bai ga wannan a matsayin jarabawa ba, to ya tozarta abin buri (na lada) ne".

349. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya ku ribatattun kwadayi, ku takaita, domin mai kwadayin duniya babu wani abu da yake tsorata shi daga gareta sai karar sautin taunar nan ta fikoki masu kaifi. Ya ku mutane! Ku dauki nauyin kula da tarbiyyar kawukanku, ku kautar da ita daga kutsawar nan ta abin da ta saba da shi".

350. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka yi mummunan zato ga Kalmar da ta fita daga bakin wani, alhalin kana da yadda zaka samar mata da wata mafita ta alheri".

351. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan kana da wata bukata gun Allah (s.w.t) to ka farad a yin salati ga annabi (s.a.w) da alayensa, sannan sai ka roki bukatarka, domin Allah ya fi karfin a roke shi bukatu biyu sai ya amsa daya ya hana dayar".

352. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda ya yi kariya ga mutuncinsa, to ya bar jayayya".

353. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yana da wauta mutum ya gaggauta kafin ya samu iko, da kuma yin jinkiri bayan samun dama".

354. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka tambayi abin da ba zai samu ba, domin akwai shagaltuwa ga abin da ya kasance naka ne".

355. Imam Ali (a.s) ya ce: "Tunani madubi ne mai tsafta, darasi kuwa mai gargadi ne mai nasiha, kuma ya ishe ka tarbiyyar kanka ka nisanci abin da kake ki ga waninka".

356. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ilimi an hada shi da aiki, duk wanda ya yi sani sai ya yi aiki, ilimi yana neman aiki ne, idan ya amsa masa shi ke nan, amma idan ya ki sai ilimi ya yi tafiyarsa".

357. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya ku mutane, jin dadin dunya itace ne mai halakarwa sai ku nisanci kiwo gunsa, barinta shi ya fi daga zama wurinta, kuma dibar iyakar guzuri shi ya fi daga tara dukiyarta, duk wani mai tara ta to shi mai rasa ta ne, kuma duk wanda ya wadatu daga gareta shi mai hutawa ne, duk wanda adon kawayenta ya kayatar da shi zata bar idanuwansa da makanta, duk wanda ya ji tsananin begenta to zata cika zuciyarsa da bakin ciki, kuma ita rawa ce a kokon cikin zuciyarsa: bakin ciki da zai shagaltar da shi, da bakin ciki da zai bata masa rai, haka nan har sai an rike shi da bakin cikinsa, sai a jefa shi cikin sarari, jijiyoyin wuyansa abin yankewa, kuma abu ne mai sauki wurin Allah ya bata das hi, kuma ya hau kan ‘yan’uwa su jefar da shi (kabari).

Munini yana duban duniya ne da kallon daukar darasi, kuma yana tanadi daga gareta da cika ciki gwargwadon lalura, kuma yana sauraronta da kunne mai ki da kyama, idan aka ce tara dukiya sai a ce zabi talauci! Idan kuma aka faranta masa da wanzuwa sai a bakanta masa da karewa! Wannan ke nan, alhalin ranar da ake dimautar da su ba ta kai ga zowa ba".

358. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah madaukaki ya sanya lada kan biyayyarsa, azaba kuwa kan saba masa, hani ga bayi daga fadawa ukubarsa, da kuma kora su zuwa ga aljannsarsa".

359. An ruwaito cewa zai yi wahala Imam Ali (a.s) ya hau kan mimbari bai ce: "Ya ku Mutane! Ku ji tsoron Allah, babu wani mutum da aka halitta da wasa balle ya shagaltu, kuma ba a bar shi sakakai ba balle ya shagaltu! Kuma duniyarsa da ta kayatu gunsa ba zata kasance matsayin lahirar da yake wa mummunan gani ba, kuma wanda ya yaudari kansa da ya samu duniya da mafi girman himmarsa, bai fi wanda ya samu lahira da mafi karancin rabonsa ba".

360. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu daukakar da ta kai musulunci, babu izza kamar izzar takawa, babu dabaibayi da ya kai tsantseni, babu mai ceto da ya kai tuba, babu taska da ta kai wadatar zuci, babu dukiyar da ta fi kawar da rashi kamar yarda da (isuwa da) abinci, duk wanda ya takaita ga guzurin da ishe shi to ya tsara wa kansa hutu, ya kuma tanadi yalwa da walwala, kwadayi kuwa shi ne mabudin wahala, kuma mahayin wuya, kwadayi da girman kai da hassada su ne masu jawo kutsawa cikin zunubi, kuma su ne mafi sharrin matattarar aibobi (sabo)".

361. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zamani zai zo wa mutane da babu wani abu na Kur'ani da zai wanzu a cikinsu sai zanensa, kuma babu wani da zai rage ga musulunci sai suna, masallatansu a wannan lokacin an raya su da gini, amma rusassu daga shiriya, mazaunansu da masu raya su, su ne mafi sharrin mutanen duniya, daga cikinsu ne fitina take fita, zuwa garesu ne kurakurai suke komawa, suna mayar da wanda ya yi niyyar barinta cikinta, suna kora wanda ya yi nesa da ita zuwa gareta, Allah madaukaki yana cewa: (Na rantse da kaina! Sai na aika wadannan fitinar da mai hakuri zai kasance ya dimauce a cikinta, kuma na yi hakan. Mu muna neman yafewar gafala daga Allah".

362. Imam Ali (a.s) ya ce da Jabir dan Abdullahi Al'ansari: "Ya kai Jabir! Addini ya tsayu kan abubuwa hudu ne: Malami mai aiki da iliminsa, da jahilin da ya dage wurin neman sani, da mai kyauta da ba ya rowa da dukiyarsa, da talakan da ba ya sanar da lahirarsa da duniyarsa, idan malami ya tozarta iliminsa, sai jahili ya kame ya ki neman sani, idan mai kudi ya yi rowa da dukiyarsa sai talaka ya sayar da lahirarsa da duniyarsa".

Ya Jabiru, wanda ni'imomin Allah suka yawaita gareshi bukatun mutane zasu yawaita gunsa, kuma duk wanda ya yi abin da Allah yake so da ita, to zai sanya ta mai wanzuwa da dawwama, amma duk wanda bai tsayar da abin da Allah yake so da ita ba, to zai sanya ta mai gushewa da karewa.

363. Ibn Jarir Addabari ya ruwaito a cikin tarihinsa daga Abdurrahamn dan Abi Laili al'fakih, ya kasance daga cikin wadanda suka fita domin yakar Hajjaj tare da dan Ash'(a.s) cewa ya fada cikin abin da yake kwadaitar da mutane da shi a kan su yi jihadi, cewa na ji Imam Ali (a.s) a ranar da muka hadu da mutanen Shama yana cewa: "Ya ku muminai, Duk wanda ya ga wani zalunci da ake yi da wani mummuna da ake kira zuwa gareshi, sai ya yi musun sa da zuciyarsa to ya kubuta ya fita, wanda ya yi musun sa da harshensa to ya samu lada kuma ya fi na farko, amma wanda ya kawar da shi da takobinsa domin kalmar Allah ta kasance ita ce mafi daukaka, kalmar azzalumai kuwa ta kasance mafi kaskanci, to wannan shi ne wanda ya dace da tafarkin shiriya, kuma ya tsayu kan tafarki, kuma yakini ya haskaka a cikin zuciyarsa.

364. Imam Ali (a.s) ya fada a cikin wata magana mai kama da wannan cewa: "Daga cikinsu akwai mai musun mummuna da hannunsa, da harshensa, da zuciyarsa, to wannan shi ne wanda ya cika kyawawan halaye duka, daga cikinsu akwai mai musun mummuna da harshensa da zuciyarsa ba tare da hannunsa ba, to wannan shi ne mai riko da kyawawan halaye biyu daga kyawawan ayyukan alheri, sai dai ya rasa guda daya, daga cikinsu kuma akwai wanda ya ki mummuna da zuciyarsa, bai sanya hannunsa da harshensa ba, to wannan shi ne wanda ya tozarta mafi kyawawan halaye biyu daga cikin uku, sai ya yi riko da daya kawai, amma daga cikinsu akwai wanda ya bar kin mummuna da harshensa da zuciyarsa da hannunsa, wannan shi ne mataccen da yake cikin rayayyu.

Ayyukan alheri dukkaninsu da jihadi a tafarkin Allah, idan an hada su da hori da kyakkyawan aiki da hanin mummunan aiki sai kamar wani tofin yawu ne a gefen wani gogi mai ambaliyar ruwa, kuma hakika horo da kyakkyawa, da hani ga mummuna ba sa kusantar da ajali, kuma ba sa hana wani arziki, kuma abin da ya fi dukkan wannan shi ne kalmar adalci a gaban wani jagora azzalumi.

365. Daga Abi Juhaifa ya ce: Na ji sarkin muminai Imam Ali (a.s) yana cewa: "Farkon abin da za a rinjaye ku a kan sa shi ne barin jihadi da hannayenku, sannan sai da harsunanku, sannan da zukatanku, duk wanda bai so kyakkaywa da zuciyarsa ba, bai kuma ki mummuna da da ita ba, to hakika an juyar da samansa ya koma kasansa, kasansa kuma ya koma samansa".

366. Imam Ali (a.s) ya ce: "Gaskiya tana da nauyi da kyakkyawan karshe, karya kuwa tana da sauki da mummunan karshe".

367. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka amintar da azabar Allah daga mafifitan wannan al'umma, saboda fadin Allah madaukaki cewa: (Babu mai amintuwa da makircin Allah sai mutane masu hasara) kuma kada ka yanke kaunar rahama ga mafi sharrin wannan al'ummar, saboda fadin Allah madaukaki: (Hakika babu mai yanke kauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai)".

368. Imam Ali (a.s) ya ce: "Rowa ita ce ta matattarar dukkan munanan aibobi, kuma shi ne jagora da ake jan komai da shi zuwa ga mummuna".

369. Imam Ali (a.s) ya ce: "Arziki guda biyu ne: Arziki da ake neman sa, da arziki da yake neman sa, idan ba ka zo masa ba, to zai zo maka, kada ka dora bakin cikin rayuwar shekararka a kan na wuninka! Abin da kake samu a kowace rana ya ishe ka a cikinta, idan wannan shekarar tana daga cikin shekarunka to Allah zai zo maka abin da ya raba ya ba ka a kowace rana, idan kuwa ba zaka rayu a wannan shekarar ba, to me ye naka na yin bakin ciki da abin da ba naka ba ne, kuma babu wani mai neman da zai taba rigon ka zuwa ga arzikinka, kuma mai galaba ba zai taba cin galaba a kanka game da shi ba, kuma abin da aka kaddara maka ba zai taba jinkirtuwa ga barin ka ba (balle ka rasa shi)".

370. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da yawa abin da yake gabatowa ba zai juya ba, da yawa wanda ake burin samun ni'imarsa a farkon dare sai ga masu yi masa kuka a karshensa".

371. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zance yana cikin daurin igiyarka muddin ba ka yi magana da shi ba, amma idan ka yi magana da shi to kai ne kake cikin daurinsa, don haka ka taskace harshenka kamar yadda kake taskace zinarenka da azurfarka, kuma da yawa kalma da ta cire ni'ima [ta jawo azaba]".

372. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka fadi abin da ba ka sani ba, [kai kada ka fadi dukkan abin da ka sani ma] domin Allah ya sanya wa gabobinka dukkansu wajibai da zai kafa hujja da su a kanka ranar kiyama".

373. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka ji tsoron Allah ya gan ka gun sabonsa, ya rasa ka gun biyayyarsa, sai ka kasance daga masu hasara, idan zaka karfafa to ka karfafa a kan biyayyar Allah, idan kuwa zaka yi rauni, to ka yi rauni kan sabon Allah".

374. Imam Ali (a.s) ya ce: "Karkata zuwa ga duniya tare da abin da kake gani daga gareta jahilci ne, kuma takaitawa wurin kyakkyawan aiki da ka samu yakinin samun lada a kansa yaudara da hasarar kai ne, kuma nutsuwa da dogara zuwa ga kowane mutum kafin zabi (zabar wanda zai zama madogara) gajiyawa ne".

375. Imam Ali (a.s) ya ce: "Daga cikin kaskancin duniya gun Allah shi ne ba a sabonsa sai a cikinta, kuma ba a samun abin da yake gunsa sai da barinta".

376. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya nemi wani abu zai same shi duka ko wani sashe nasa".

377. Imam Ali (a.s) ya ce: "Alherin da bayansa wuta ce ba alheri ba ne, sharrin da bayansa aljanna ce ba sharri ba ne, kuma dukkan ni'ima in banda aljanna wulakantacciya ce, kuma duk wani bala'in da ba wuta ba ce lafiya ne".

378. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku sani talauci yana daga cikin bala'I, kuma rashin lafiyar jiki yana daga mafi tsananin rashi, kuma cutar zuciya tana daga mafi girman rashin lafiya jiki. Ku sani yalwar dukiya tana daga cikin mafi girman ni'ima, sai dai lafiyar jiki ta fi yalwar dukiya, takawar zuci kuwa tafi lafiyar jiki".

379. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda aikinsa ya mayar da shi baya, to nasabarsa ba zata sanya shi gaba ba. A wata ruwayar yana cewa: wanda darajar kansa ba ta amfana masa ba, to darajar iyayensa ba zata amfane shi ba".

380. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mumini yana da awowi uku: Awar da yake munajati da ubangijinsa a cikinta, da awar da yake neman abincinsa, da awar da yake hana kansa jin dadinta cikin abin da ya halatta yake kawata. Kuma bai kamata ba ga mai hankali ya kasance sai a kan abubuwa uku: Neman abin rayuwarsa, da kuma takawa zuwa ga makomarsa, da jin dadi a abin da ba haram ba".

381. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka guji duniya sai Allah ya nuna mana sirrorinta, kuma kada ka gafala domin kai ba a gafala daga kai ba".

382. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku yi magana za a san ku, domin mutum abin boyewa ne karkashin harshensa".

383. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka riki abin da ya zo maka da ga duniya, ka juya daga abin da ya juya daga gareka, idan kuwa ba ka yi ba, to ka kyautata nema".

384. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da yawa maganar da ta fi shiga fiye da sanya karfi".

385. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk abin da aka takaita a kansa ya isa ne".

386. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutuwa, ko kaskanci, ko karantawa, ko tawassuli, wanda duk ba a ba shi yana zaune ba, to ba za a ba shi yana tsaye ba. Zamani biyu ne: da naka da wanda yake kanka; idan ya zama naka (ka same shi), to kada ka yi takama, amma idan ya kasance a kanka (ka rasa shi), to ka yi hakuri!".

387. Imam Ali (a.s) ya ce: "Madalla da turare almiski, mai sauki dauka, mai dadin kashi".

388. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka ajiye alfaharinka, ka sauke girman kanka, ka tuna kabarinka".

389. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da yana da hakki kan uba, kuma uba yana da hakki kan da, daga hakkin uba a kan da, ya bi shi a komai sai dai cikin sabon Allah, kuma hakkin da a kan uba shi ne ya kyautata sunansa, ya kyautata ladabinsa da koyar da shi Kur'ani".

390. Imam Ali (a.s) ya ce: "Maita gaskiya ce, tofi gaskiya ne, sihiri gaskiya ne, camfi gaskiya ne, shu'umci ba gaskiya ba ne, daukar tasiri da wani abu ba gaskiya ba ne, turare kuwa yaduwa ne tsari (kariya da tofi) ne, zuma ma tsari (kariya da tofi) ne, hawa ma tsari (kariya da tofi) ne, duban koraye (kamar itatuwa da shuke-shuke) tsari (kariya da tofi) ne".

391. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kusantar mutane tare da halayensu, kariya ne daga munanansu (gabarsu da sharrinsu)".

392. Imam Ali (a.s) ya ce da wani mai magana da shi, yayin da ya yi wata magana da ake kaskantar da wanda yake kamarsa idan ya yi irinta:  "Hakika ka tashi sama kana dan tsako, ka kuma gangaro (kiwo ko kutsawa sahara da sauransu) kana dan karamin dan rakumi".

Wato ya kayar da girmansa, bai kamata ba ya yi wannan maganar mai zubar da kimarsa.

393. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi nuni (wato ya nemi bukata) gun na nesa, to dubaru zasu kubuce masa kuwa".

394. Yayin da aka tambayi Imam Ali (a.s) game da ma'anar (Babu dubara babu karfi sai ga Allah) sai ya ce: "Mu ba ma mallakar komai tare da Allah, kuma ba ma mallaka sai abin da ya mallaka mana, kuma duk sa'adda ya mallaka mana abin da shi ne ya fi mallakarsa fiye da mu sai ya kallafa mana, kuma duk sa'adda ya karbe shi daga gunmu sai ya sauke mana nauyin takalifinsa daga kawukanmu".

395. Imam Ali (a.s) ya ce da Ammar dan Yasir yayin da ya ji shi yana mayar wa Mugira dan Shu'uba da wata magana: "Kyale shi Ammar, ka sani shi ba ya karbar wai abu na addini sai abin da duniyar ta kusantar, kuma da gangan ya rikita kansa domin ya sanya shubuha (rikirkitattun lamurra) a matsayin uzurin munanansa".

396. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kaskan da kan masu kudi ga talakawa domin neman abin da yake wurin Allah ya kyautata matuka! Mafi kyawu daga gareshi shi ne dagawar talakawa kan masu kudi dogaro ga Allah".

397. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah bai ba wa wani mutum hankali ba, sai ya cece (tseratar da) shi da shi wata rana!".

398. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi fada da gaskiya an kayar da shi".

399. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zuciya ita ce shafin fuskar gani".

Wato; Duk abin da gani ya hanga to yana zama a zuciya ne.

400. Imam Ali (a.s) ya ce: "Tsoron Allah shi ne jagoran kyawawan halaye".

401. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka sanya kaifin harshenka kan wanda ya sanya ka magana, ko fasahar maganarka kan wanda ya gyara ka (ya ilmantar da kai)".

402. Imam Ali (a.s) ya ce: "Nisantar abin da kake ki wani ya yi maka shi, ya ishe ka tarbiyyantarwa ga kanka".

403. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi hakuri, to ya yi hakurin 'yantattun bayi, in ba haka ba, zai yi faduwa, irin faduwar nan ta jahilai marasa tajriba".

404. A wani labarin da aka karbo daga Imam Ali (a.s) ya ce da Ash'ass dan Kais yana mai yi masa ta'aziyya: "Idan ka yi hakuri irin hakurin masu daraja, in ba haka ba, to ka yi halin kaskantuwa kamar na dabbobi".

405. Imam Ali (a.s) ya fada game da siffanta duniya cewa: "Tana yaudara, tana cutarwa, tana daci, Allah bai yarda da ita a matsayin lada ba ga masoyansa, ko ukuba ga makiyansa, kuma mutanen duniya kamar matafiya ne, da suna cikin tafiya sai mai jan su ya yi musu tsawa sai suka tafi".

406. Imam Ali (a.s) ya ce da dansa Imam Hasan (a.s) cewa: "Ya kai dana! Kada ka bar wani abu na duniya a bayanka, domin zaka bar shi ga dayan mutane biyu ne: Ko mutumin da zai yi aiki da shin na biyayya ga Allah, sai ya rabauta da abin da ka wahala kansa, ko mutumin da zai aiki da shi da sabon Allah, [sai ya tabe da abin da ka tara masa] sai ka kasance mai taimakonsa kan sabonsa, kuma bai kamata ka zabi dayan wadannan a kanka ba".

Kuma an ruwaito wannan maganar da wani lafazi kamar haka: "Amma bayan haka, wannan abin da kake da shi a duniya da can ya kasance na wasu ne kafin kai, kuma zai kasance na wasu bayanka, kuma kai mai tara shi ne ga dayan mutane biyu: Mutumin da ya yi aiki da abin da ka tara masa cikin biyayyar Allah, sai ya rabauta da abin da ka wahala kansa, ko mutumin da ya yi sabon Allah da shi, sai ya tabe da abin da ka tara masa, kuma daya daga cikin wadannan bai kamata ka zabe shi a kanka ba, ka daukar masa wannan a bayanka. Don haka ka nema wa wadanda suka wuce rahamar Allah, wadanda kuma suka rage arzikin Allah".

407. Imam Ali (a.s) ya ce da wani mutun da ya ce: (Ina neman gafarar Allah) a wurinsa: "Kaiconka, shin ka san ma'anar me ye istigfari kuwa? Ka sani istigfari darajar madaukaka ne, kuma shi suna ne da yake da ma'ana shida:

Na farkonta: Nadama kan abin da ya wuce.

Na biyu: Niyya a kan barin sake yin sa har abada.

Na uku: Ka mayar wa mutanen hakkokinsu har sai ka hadu da Allah babu nauyin wani a kanka.

Na hudu: Ka duba duk wani wajibi da ka tozarta sai ka bayar da hakkinsa.

Na biyar: Ka duba naman da ya tofu da haram sai ka narkar da shi da bakin ciki, har sai fatar ta damfaru da kashi, sannan wani sabon nama ya tofo tsakaninsu.

Na shida: Ka dandana wa jiki zogin biyayya kamar yadda ka jiyar da shi dadin sabo.

Yayin nan ne sai ka ce: Ina neman gafarar Allah".

408. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakuri jama'a (dangi) ce".

409. Imam Ali (a.s) ya ce: "Dan Adam miskini ne: Ajalinsa boyayye ne, dalilan rashin lafiyarsa a boye suke, aikisan an kiyaye shi, sauro ma yana jiyar da shi zafin zogi, shakewar shan ruwa tana kashe shi, gumi yana sanya shi wari".

410. An ruwaito cewa ya kasance yana zaune wata rana da sahabbasan sai wata mata kyakkyawa ta wuce su, sai wasu mutane suka kalle ta da gefen idanuwansu. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika idanuwan wadannan mazaje ta fiye kwadayi, wannan ne kuma ya sanya ta jin sha'awa, idan waninku ya ga wata mace da ta kayatar da shi to ya koma ya shafi matarsa, ita fa (dai wannan ita ma) mace kamar saurarn mata. Sai wani mutum daga Hawarijawa (makiya Imam Ali) ya ce: Allah ya la'anci kafiri! ya fiye ilimi! Sai mutane suka tashi domin su kashe shi. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: Ku saurara, ku sani zagi ne da (sakamakonsa) zagi kawai, ko rangwame daga zunubi (wato ko in yafe masa)!".

411. Imam Ali (a.s) ya ce: "Abin da y anuna maka hanyar batanka da shiriyarka ya ishe ka yin hankali".

412. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku aikata alheri kada ku wulakanta wani abu daga gareshi, domin kadan karaminsa babba ne, kadan dinsa mai yawa ne, kada wani ya ce: wane ne ya fi cancanta ya yi aikin alheri fiye da ni, sai ya kasance haka ne, hakika alheri da sharri suna da mutanensu, kuma duk wani abu da ba ku yi ba daga garesu, to ma'abotansu zasu wadatar da ku yin su".

413. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya gyara badininsa, to Allah zai gyara masa zahirinsa, kuma wanda ya yi aiki ga addininsa to Allah zai wadata da shi lamarin lahirarsa, kuma wanda ya kyautata tsakaninsa da Allah to Allah zai isar masa tsakaninsa da mutane".

414. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakuri labule ne mai suturtawa, hankali takobi ne mai yankewa, to ka suturta raunin hankalinka da hakuri, ka kuma yaki son ranka da hankalinsa".

415. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah yana da wasu bayi da ya kebance su don ni'imomi saboda amfanar bayi, sai ya tabbatar da ita gunsu matukar sun bayar da ita, idan kuwa suka hana ta, to sai ya cire ta daga garesu, sannan sai ya juya ta zuwa ga wasunsu".

416. Imam Ali (a.s) ya ce: "Bai kamata ba wani ya amintu da abubuwa biyu: Lafiya da Wadata: ta yiwu ka gan shi mai lafiya alhalin ba shi da lafiya, ko mawadaci alhalin talaka ne".

417. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda duk ya kai kukan wata bukata zuwa ga wani mumini, kamar ya kai kukan ta wurin Allah ne, wanda ya kai kukanta zuwa ga wani kafiri to kamar ya kai kukan Allah ne".

418. Imam Ali (a.s) yana fada a wani idi ya ce: "Shi idi ne ga wanda Allah ya karbi azuminsa kuma ya gode wa sallolin darensa, kuma duk ranar da ba a saba wa Allah a cikinta ba to ita idi ce".

419. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi girman hasara ranar lahira ita ce hasarar mutumin da ya tara dukiya ba a bin Allah ba, sai ya gadar da ita ga wani mutum da ya yi ciyar da ita wurin bin Allah (s.w.t), sai ya shiga aljanna da ita, shi kuwa na farkon ya shiga wuta da ita".

420. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi hasarar mutane a ciniki, kuma mafi tabewarsu, shi ne mutumin da ya tsofar da jikinsa a cikin neman bukatunsa da burinsa, kuma kaddara ba ta taimaka masa samun burinsa ba, sai ya fita daga duniya da hasararasa, ya zo wa lahira da zunubansa (a kansa akwai hakkokin Allah da na mutane da ake bin sa su)".

421. Imam Ali (a.s) ya ce: "Arziki biyu ne: Mai nema, da wanda ake nema, wanda ya nemi duniya to mutuwa zata neme shi har sai ya fita daga duniya, wanda ya nemi lahira duniya zata neme shi har sai ya samu arzikinsa daga gareta".

422. Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika masoya Allah su ne wadanda suke duba zuwa ga badinin duniya yayin da mutane suka duba zahirinta, suka shagaltu da ajalolinsu yayin da mutane suka shagaltu da kayan duniya, sai suka kashe abin da suke jin tsoron ya kashe su (Kamar fushi, da sha'awa) a cikinta, sai suka bar abin da suka san zai rabu da su (kamar kayan duniya) a cikinta, sai suka ga yawaitawar wasunsu ga duniya shin gashin kai ne (kamar wanda yake ganin ya dogara da kansa sabanin Allah), kuma riskar wasunsu ga duniya rashi ne (wato wadanda suke ta bibiyar duniya don kada ta kubuce musu wannan su ne masu rashi), makiyan abin da mutane suke so (na duniya ne), masoyan abin da mutane suke ki (na lahira ne)! da su ne aka san littafi, da shi ne suka sani, da su ne littafi ya tsayu kuma da shi ne suka tsayu, ba sa ganin wani abin bukata sama abin da suke bukata, ko wani abin tsoro sama da abin da suke tsoro".

423. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku tuna yankewar jin dadi, da wanzuwar laifuffuka (hakkokin Allah da na mutane a kanku)".

424. Imam Ali (a.s) ya ce: "Jarraba ka ki". (wato ka jarraba mutum kafin ka zama abokinsa ta yiwu ka ki shi saboda wani abu sai ka ki kulla abota da shi).

Akwai kuma mutanen da suke ruwaito wannan daga manzon Allah (s.a.w), sai dai abin da yake karfafa cewa daga maganar Imam Ali (a.s) ce, shi ne abin da Sa'alab ya ruwaito cewa: Ibnul A'arabi ya gaya mana ya ce: Ma'amun ya ce: Ba don Imam Ali (a.s) ya ce: "Jarraba ka ki" ba, da sai in ce: Ki ka jarraba.

425. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah ba zai bude wa wani mutum kofar godiya ba, sannan sai ya rufe masa kofar dadi, kuma ba zai bude masa kofar addu'a ba sannan sai ya rufe masa kofar amsa, kuma ba zai bude masa kofar tuba ba sannan sai ya bude masa kofar gafara".

426. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya fi cancanta da karimci, shi ne wanda aka san masu karimci da shi".

427. An tambayi Imam Ali (a.s) game da cewa Adalci ne ya fi ko kyauta? Sai ya ce: "Adalci shi ne sanya komai a mahallinsa, kyauta kuwa shi ne fitar da su daga inda suke, adalci shi jagora ne na kowa, kyauta kuwa mai bujurowa ne na musamman, don haka adalci shi ne mafifici, mafi fifikonsu".

428. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutane makiya abin da suka jahilta ne".

429. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zuhudu dukkaninsa yana cikin kalmomi biyu ne na Kur'ani: Allah yana cewa: (Domin kada ku yanke kauna daga abin da ya tsere muku, kuma kada ku yi farin ciki da abin da ya ba ku), duk wanda bai yanke kauna daga abin da ya gabata ba, kuma bai yi farin ciki da abin da ya samu ba, to ya yi riko da zuhudu da dukkan geffansa".

430. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wilaya (Jibintar lamari ko soyayya) ita ce madaurar (garken) mazaje".

431. Imam Ali (a.s) ya ce: "Sau da yawa bacci ya rusa (hana) himmar (ayyukan) wuni".

432. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wani gari bai fiye maka wani garin ba, mafificin gari shi ne wanda ya karbe ka".

433. Yayin da labarin mutuwar Malik Ashtar ya zo wa Imam Ali (a.s) sai ya ce: "Malik lallai Malik ya bunkasa! Wallahi da ya kasance dutse ne da ya kasance kurman dutse, [da dutse ne da ya kasance fakon dutse], mahayin duke ba ya iya hawansa, kuma tsuntsu ba ya iya kamo shi".

434. Imam Ali (a.s) ya ce: "Dan kadan da aka dawwama kansa, ya fi mai yawa mai kosarwa".

435. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan mutum yana da wata dabi'a mai kyau, to ka saurari sauran dabi'un masu kama da ita".

436. Imam Ali (a.s) ya ce da Galib dan Sa'asa'a baban Farazdak a wata magana da ta gudana tsakaninsu: "Ina rakumanka masu yawa? Sai ya ce: Ai zakka da sadaka sun karar da su. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: Wannan ita ce mafi kyawun hanyar karar da ita".

437. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi kasuwanci ba tare da ilimi ba, to ya fada wa cin riba".

438. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya girmama kananan bala'o'i to Allah zai jarrabe shi da manyansu".

439. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ransa ta girmama, to sha'awar ransa zata wulakanta gunsa".

440. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu wani mutum da zai yi raha, sai ya fita daga hankalinsa ficewa".

441. Imam Ali (a.s) ya ce: "Gudunka ga abin da yake son ka, karancin rabo ne, sonka ga abin da yake kin ka kuwa, kaskancin kai ne".

442. Imam Ali (a.s) ya ce: "Zubairu bai gushe ba tare da mu Ahlul-bait har sai da dansa Abdullahi mai shu'umi ya girma".

443. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mene ne dan Adam yake alfahari da shi: Farkonsa mani, karshensa gawa ce, kuma ba ya arzuta kansa, kuma ba ya ture mutuwarsa".

444. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wadata da talauci bayan zuwa wurin Allah ne (wato a ranar kiyama ne talauci da wadata na hakika suke)".

445. An tambayi Imam Ali (a.s) cewa: Waye ya fi kowa iya waka, sai ya ce: "Mutane ba su yi gudu (tsere) ba a wani fili zuwa wata alamar da aka sanya kaiwa gunta, idan kuwa babu makawa (sai na bayar da amsa duk da  kuwa ba a taba tara duk mawakan kowane zamani a wuri daya ba an yi gasa) to sarkin bata ne". (yana nufin Imru'ul Kais ne).

446. Imam Ali (a.s) ya ce: "Shin babu wani 'yantacce da zai bar wannan kazantar baki (wato duniya) ga masu ita ne? ku sani rayukanku ba su da wani kudi da za a biya su da ya kai aljanna, don haka kada ku sayar da ita sai da ita (aljanna)".

447. Imam Ali (a.s) ya ce: "Masu zari biyu ba sa koshi: Mai neman ilmi da Mai neman duniya".

448. Imam Ali (a.s) ya ce: "Alamar imani shi ne ka zabi gaskiya koda kuwa zata cutar da kai a kan karya koda kuwa zata amfanar da kai, kuma maganarka ta kasance daga gwargwadon saninka, kuma ka ji tsoron Allah a magana kan waninka".

449. Imam Ali (a.s) ya ce: "Kaddara tana galaba kan gwargwadon kiyasi, har sai lafiya (dacewa) ta kasance cikin juya lamurra". (Wato; mu muna tsara wani abu, amma kaddara tana farar da wani abin, har sai an samu dacewar tafiyar lamurran bayi).

450. Imam Ali (a.s) ya ce: "Juriya da bi sannu tagwaye ne, da daukakar himma take haifar da su".

451. Imam Ali (a.s) ya ce: "Yi da wani shi ne makamin gajiyayye".

452. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da yawa wanda aka fitina da fadin magana mai kyau game da shi". (wani mutumin yabonsa yakan jawo masa munanan halaye).

453. Imam Ali (a.s) ya ce: "An yi duniya ne don waninta ba don kanta ba".

454. Imam Ali (a.s) ya ce: "Banu Umayya suna da magangarar da zasu gangara mata, da sun yi sabani tsakaninsu, sannan sai kuraye suka yi musu makirci da sun ci nasara kansu". (wato duk raunin da suka yi ba zasu rushe ba sai wannan lokacin na karewarsu ya cika).

455. Imam Ali (a.s) ya fada game da mutanen Madina cewa: "Su ne wallahi suka reni musulunci kamar yadda ake renon 'yan tumaki a garkensu, da hannayensu masu baiwa da kyauta, da harsunansu masu kaifi".

456. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ido shi ne madaurin dubura".

457. Imam Ali (a.s) ya ce: "Majibincin lamurransu (wato manzon Allah) ya tsayu da kula da lamurransu (na zaman tare da na jagoranci) sai ya tsaya kyam ya daidaitu, har sai da addini ya dora wuyansa a kasa (wato ya kafu daram)".

458. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wani zamani mai wahala zai zo wa mutane, mai yalwa zai cije abin hannunsa (wato ya yi rowa da shi), alhalin ba a umarce shi da yin haka ba (wato rowa haram ce), Ubangiji madaukaki yana cewa: (Kada ku manta da falala a tsakaninku), ana daga ashararan mutane a cikinsa, ana kaskantar da zababbu, ana zama gun masu kallafa wa kai (jahilai masu rigar malamai), alhalin manzon rahama (s.a.w) ya hana zama gun masu kallafa wa kai".

459. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutum biyu ne zasu halaka game da ni: Mai so mai shisshigi, da mai ki mai wuce iyaka".

Kamar dai fadinsa ne cewa: Mutum biyu zasu halaka game da ni: Mai so mai wuce iyaka, da mai ki mai kyama.

460. An tambayi Imam Ali (a.s) game da Kadaita Allah (s.w.t) da Adalci, sai ya ce: "Kadaita Allah shi ne kada ka sanya shi a saken zuci, Adalci kuwa kada ka tuhume shi".

461. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu alheri game da yin shiru kan hukunci, kamar yadda babu alheri game da magana da jahilci".

462. Imam Ali (a.s) ya fada game da addu'ar rokon ruwa yana mai cewa: "Ya Ubangiji ka shayar da mu gajemare mai kaskan da kai ba mai tsananinta ba". (wanda zai kasance rahama da jin dadi da yalwa, ba mai kawo wahala ba).

Wannan magana ce mai fasha da ya kamanta gajemare masu tsawa da walkiya da iska mai tsanani da rakuma masu wuyar hawa da sha'ani, su kuwa gajemare marasa wannan ya kamanta su da rakuma masu saukin hawa da biyayya da saukin tatsarsu.

463. An ce wa Imam Ali (a.s), da dai ka rina furfurarka ya sarkin muminai sai ya ce: "Rini ado ne, mu kuma mutane ne da muke cikin musiba!". Wato: yana nufin rashin manzon Allah (s.a.w)".

464. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai jihadi mai shahada a tafarkin Allah bai fi wanda ya samu iko (kan yin sabo) sai ya kame kansa lada ba, Mai kame kai ya kusa ya kasance mala'ika ne daga cikin mala'iku".

465. Imam Ali (a.s) ya ce: "Wadatar zuci dukiya ce da ba ta karewa".

466. Imam Ali (a.s) ya ce da Ziyad dan Babansa, a lokacin da ya maye shi da Abdullahi dan Abbas a yankin Farisa da ayyukanta, a cikin wata magana mai tsayi tsakaninsu da ya hana shi game da dada haraji-: "Ka aiwatar da adalci, ka guji tsanantawa (ba tare da hakki ba), da yin zalunci, domin tsanantawa tana jawo kaurace wa wuri, jalunci kuwa yana kawo yaki ne".

467. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi tsananin zunubi shi ne wanda mai yinsa ya rena shi".

468. Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah bai dora wa masu jahilci nauyin neman sani ba, har sai da ya dora wa masu ilimi nauyin sanarwa (koyarwa)".

469. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi munin aboki shi ne wanda aka kallafa wa kai saboda shi".

470. Imam Ali (a.s) ya ce: "Idan mumini ya fusata (ya kunyata) dan'uwansa mumini, to hakika ya rabu da shi". (domin wannan yana iya sabbaba rabuwarsu).


[1] - Wannan Magana tasa tana daga tausasan zattuttuka da fasaha, ma’anarsa ita ce: mu idan ba a ba mu hakkinmu ba sai mu zama cikin kaskanta, domin wanda aka goya a baya yana hawa kan duwainiyar rakumi ne, kamar bawa da ribatacce, da makamantansu.

[2] - Wato mai hankali baya Magana sai ya shawarci zuciyarsa, tunaninsa ya ba shi umarni, amma wawa furta maganarsa yana rigon tunaninsa, da tace ra’ayinsa.

[3] - Da sara irin na maciji.

[4] Hawarijawa.

[5] Qaranta ta wajen nema, domin ta girmama da biyan buqata, da kuma voye ta domin ta bayyana bayan biyanta. Kuma idan ta yi sannu-sannu sai a ji daxinta.

[6] Alami: da suke karantawa a asirce domin wa’aztuwa da xaukar darussa da tunani a cikin zurfafan ma’anoninsa.

[7] Tufari ne: saboda suna karanta ta a fili domin bayyanar da qasqanta da rusunawa ga Allah (S.W.T).