Lakabinsa: Amirul munin, Sayyidul muslimin, Imamul muttakin, Ka’idul gurril muhajjalin, sayyidul ausiya, sayyidul arab, Almurtada, Ya’asubuddini, Haidar, Al-anza’al badin, Asadul-Lah.
Alkunyarsa: Abul Hasan, Abul Hasanain, Abul Sibtain, Abu Raihanatain, Abu Turab.
Mahaifinsa: Abu Talib (Baffan Annabi) Imran ko kuma Abdu manaf dan Abdul Mutallib.
Mahaifiyarsa: Fatima Bintu Asad.
Ranar Haihuwarsa: Ranar Juma' a 13 ga Rajab.
Gurin Haihuwarsa: Cikin Ka'aba Dakin Allah mai alfarma.
Shekarar Haihuwarsa: Shekara talatin bayan Shekarar Giwaye.
Adadin ‘ya’yansa: masu tarihi sun yi sabani kan yawan ‘ya’yansa amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyin daban daban. Wasu na cewa, `ya'yansa: 36, 18 da cikinsu maza ne 18 kuma mata, Mazan su ne:
1) Al- Hasan Mujtaba
2) Husain
3) Muhammad Bin Hanafiyya
4) Abbas Akbar wanda ake yi wa alkunya da Abul Fadli
5) Abdullahil Akbar
6) Ja'afarul Akbar
7) Usmanul Akbar
8) Muhammad Asgar
9)Abdullahil Asgar
10)Abdullah wanda ake yi wa Alkunya da Abu Ali.
11) Aun
12) Yahya
13) Muhammadul Awsat
14) Usmanul Asgar
15) Abbasul Asgar
16) Ja'afarul Asgar
17) Umarul Akbar
18) Umarul Asgar
1 ) Zainabul Kubra,
2) Zainabul Sugra wadda ake kira Ummu Kulsum,
3) Ramlatal Kubra
4) Ummul Hasan
5) Nafisatu
6)Rukayyatus Sugra
7) Ramlatul Kubra
8) Rukayyatul Kubra
9) Maimunatu
10) Zainabus Sugra
11 ) Ummu Hani
12) Fatimatus Sugra
13) Imamatu
14) Khadijatus Sugra
15) Ummu Kulsum
16) Ummu Salama
17) Hamamata
18) Ummu Kiram
1-Fadimatuz-Zahra’yar manzon Allah (A.S)
2- Amama ‘yar Abil Asi
3-Ummul banin Alkilabiyya
4-Laila ‘yar Mas’ud
5-Asma’u ‘yar Amis
6-Assahba’u ‘yar Rabi’a (ummu Habib)
7-Khaula ‘yar Ja’afar
8-Ummu Sa’ad ‘yar Urwa
9-Makhba’a ‘yar Imru’ul kais.
Hatiminsa: Almulku Lillahi Wahidul Kahhar (Mulki na Allah ne Shi kadai mai cikakken rinjaye).
Haihuwar Imam Ali (A.S): Imam Ali (A.S) shi ne na farko cikin jerin imaman gidan Annabta kuma shi ne wasiyyin manzon Allah (S.A.W). An haife shi ne a cikin dakin Allah mai alfarma watau ka'abah a daidai ranar 13 ga watan Rajab shekara ta 23 kafin hijira. Yanzu haka dai kabarinsa yana Najaf dake kasar Iraki.
Yakokinsa: ya yi musharaka a yakokin manzo (S.A.W) gaba daya banda yakin Tabuka da manzo ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al’amuranta amma yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin halifancinsa su ne: Aljamal da Siffaini da Annahrawan.
Dalilin Rasuwarsa: Ibn Muljam ne ya kashe shi sakamakon harin ba zata da ya kai masa yana salla a cikin masallacin Kufa.
Tsawon rayuwarsa: shekar 63.
Tsayin imamancinsa: shekara 30.
Tarihin shahadarsa: Daren jumma’a 21 ga watan azumi 40H.
Wurin da ya yi shahada: Masallacin Kufa.
Dalilin shahadarsa: Saran takobin nan na la’ananne Abdurrahman dan maljam yana mai sujada a mihrabin masallacin kufa.
Inda aka binne shi: Yankin nan na gariyyi a garin Najaf madaukaki.