Tarbiyyar Kame Farji

A cikin littafin Nahajul-balaga: Hikima ta 27- ya zo cewa: An tambaye shi game da imani sai ya ce yana kan ginshikai hudu ne: akan juriya, da yakini, da adalci, da jihadi: A- Hakuri yana kan rassa hudu: akan shauki, da tsoro, da zuhudu, da taka-tsantsan: wanda ya so aljanna zai fidiye (ya fita) daga sha’awaice-sha’awaice, wanda ya ji tsoron wuta zai nisanci haram, wanda ya yi gudun duniya zai ga saukin musibu, wanda ya yi sauraron mutuwa zai gaggauta zuwa aikata alherai…”.

Sannnan a cikin littafin sakon hakkoki na Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma kuma hakkin farjinka shi ne ka kare shi daga zina, ka kiyaye shi daga abin da bai halatta ba, ka taimaka a kansa da rufe idanuwa, domin shi ne mafi taimakon abu, da kuma ba shi kariya da yunwa da kishirwa idan ya yi nufi, da yawaita ambaton mutuwa, da kuma gargadi ga kanka saboda Allah, da tsoratar da ita da shi, kariya da taimako suna ga Allah ne, kuma babu dubara ko karfi sai da shi".

Farji wani bangare ne na gabar da ake yin amfani da ita domin samun haihuwa ta hanyar amfani da shi ga namiji ne ko mace, sai dai galibi ana kiran na mace da wannan kalma, amfaninsa shi ne kare samuwar nau'in mutum daga karewa.

Wannan bangaren shi ne ya fi kowanne hadari wurin halakarwa, kuma a sanadiyyarsa ne aka saba wa Allah dare da rana, da dan Adam ba shi da wannan bangaren da ma'anar ba a ma yi masa sha'awa ba, to da bai sha wahalar wannan gida na duniya ba, kamar yadda da ba a yi masa shi ba, da babu wani amfanin saukowarsa duniya domin yada zuriya.

Da farkon Imam Sajjad (a.s) ya yi nuni da cewa kare farji daga zina yana daga cikin hakkokin farji, sannan shari'a  ta sanya hanyoyin kare shi daga zina, sai ta sanya kariya ga farji da aure da'imi da kuma auren mutu'a, domin kada dan Adam ya fada cikin hadarin zina, sai tarbiyyar ruhinsa ta lalace, sannan a samar da 'ya'yan shego, sai aikata zunubi ya yi sauki, bala'o'I su faru a duniya barkatai.

Domin dan zina ya fi samun saukin aikata sabo a kan dan halal, don haka tarbiyyarsa tana bukatar himma matuka. Akwai wani wanda ya taba kashe wani babban wansu a watan azumi 1428, kuma lokacin da ya kashe shi da dutse da ya dauka mai nauyi ya kwankwatsa masa kai da shi, sai na ga ya yi daidai da lokacin da aka sari Imam Ali (a.s) da takobi wato sallar asuba 19 ga watan ramadhan.

A lokacin babu wani abu da ya zo mini sai cewa wannan anya kuwa ba dan shege ba ne. Ilai kuwa sai nan wani yake gaya mini cewa ai bayan babarsu ta fita daga gidan da ta haifi wan nasu da shi kanin ya kashe wanda a sanadiyar tabin hankali ne babansa ya sake ta. Sai aka rasa inda take domin wasu 'yan iska ne suka dauke ta ba su bar ta ba sai da ta yi cikin shegen da aka samu cikin wannan wanda ya yi kisan da shi da dan'uwansa 'yan tagwai.

Da yawa zamu ga wani rashin imani da babu kamarsa, idan mun bincika sai mu samu ba dan halala ba ne ya yi shi. Da sharrin zina ya tsaya kan haka ne kawai da ya isa sharri, domin yana hana kamalar dan Adam, hada da kazanta da take yawaita da yada cututtuka marasa iyaka a cikin al'umma, ga kuma hana ruwan sama da arziki da zai iya mamaye al'umma sakamakon zina.

Don haka ne sai musulunci ya zo da hanayr aure domin ya tarbiyyantar da al'umma, ya samo mata hanyar mafita domin kada a yi zina, mu sani sau da yawa samari da 'yan mata suka lalace saboda rashin aure. Don haka ne Allah mai hikima domin kada maza su fada cikin bala'in zina sai ya sanya ikon dukan matan da suke kin su a kwanciya a hannunsu, bai kuma sanya ikon dukan mace ba sai a wannan kawai.

Sannan Allah mai hikima bai bar wannan lamarin ba sai da ya sanya auren mutu'a domin ya sawwake alakar cakudar maza da mata, wannan auren yana iya kasancewa mafita daga zina, kuma tun da Allah ne ya sanya shi a matsayin doka babu wani wanda zai iya hana shi ya hanu.

Sai dai abin takaici a kasashenmu an yi mummunar fahimta ga wannan auren, domin ma ba a san shi ba, sai zinace-zinace suka yawaita, yana da kyau mu sani auren mutu'a halal ne daga Allah kamar auren da'imi, kuma a littafinmu na auren mutu'a mun yi bayani a ciki dalla-dalla bisa sharuddansa da dokokinsa.

Sarkin muminai Imam Ali (a.s) ya kawo hana auren mutu'a da halifa na biyu ya yi a matsayin dalilin da ya sanya yawaitar zina a cikin duniyar musulmi, domin da manzon Allah (s.a.w) ya zo da shari'a ya shimfida duk abin da zai hana mutum sabo a cikinta, idan kuwa ba haka ba, idan wani ya yi zina aka yi masa haddi zai kasance zalunci ne.

Don haka duk wanda ba shi da ikon yin auren da'imi, ya samu mace wacce sharuddan yin auren mutu'a da ita suka cika, kamar kasancewarta ba matar aure ba, ba kuma budurwa ba, da sauransu, sannan sai ya yi zina, lallai wannan ya cancanci dukkan ukubar Allah. Amma idan da babu irin wannan doka, sai aka kama shi da sunan shari'a aka yi masa ukuba, to ya zama zalunci, domin ba yadda Allah zai halicci mutum, sannan sai ya hana shi hanyar mafita kan halittar sha'awa da ya yi masa.

Ibn Abbas yana cewa: "Mutu'a rahama ce da Allah ya tausaya wa wannan al'umma da ita, ba domin Umar ya hana ta ba, da babu wanda zai bukaci yin zina sai tababbe".

Jabir dan Abdullah yana cewa: "Mun yi auren mutu'a lokacin manzon Allah (s.a.w) da lokacin Abubakar, da wani bangare na lokacin Umar, sai Umar ya ce: Kur'ani dai shi ne Kur'ani, Manzon Allah dai shi ne manzon Allah, kuma dai wadannan mutu'o'in guda biyu ne da suke lokacin manzon Allah (s.a.w), wato hajjin tamattu'i, da kuma auren mutu'a" (Masnad Ahmad bn Hambal: 1 / 52). Sai dai a nan Ahmad bn Hambal ya cire karshen maganar ne, domin Umar yana cewa: Ni na hana ne kuma ina yin ukuba a kan duk wanda ya yi su. (Masnad Ahmad bn Hambal:398).

Suyudi yana cewa: "Farkon wanda ya hana auren mutu'a shi ne Umar" (TarikhulHulafa: 137).

Jabir dan Abdullah yana cewa: "Mun yi auren mutu'a lokacin manzon Allah (s.a.w) da lokacin Abubakar, da wani bangare na lokacin Umar, sai Umar ya hana" (Bidayatul Mujtahid, na Hambalawa: 2 / 63).

Mash'huriyar maganar Imam Ali (a.s) ta shahara cikin musulmi cewa: "Ba don Umar ya hana auren mutu'a ba, da babu wanda zai yi zina sai ya tabe". Wasu suna fassara shi da cewa: "Ba don Umar ya hana auren mutu'a ba, da babu wanda zai yi zina sai tababbe" (Tafsirul Fahrurrazi: 10 / 51).

Wannan lamarin a fili yake yana nuna cewa zina ta yawaita cikin al'ummar musulmi ta yadda ta shiga kowane lungu da surkukiya, domin wannan hanin da Umar ya yi wa auren mutu'a. Wannan magana ce da malaman Sunna da Shi'a suka yi ittifaki a kanta.

Sannan fadin Imam Ali Sajjad cewa "ka kiyaye shi daga abin da bai halatta ba", yana karfafa mana hanyar nan ta nisantar sha'awar da zata kai ga fadawa cikin haram da wannan amanar da Allah ya yi mana ita. Wasu mutane sau da yawa suna son su hole kamar yadda suke so ba tare da la'akari da haramcin Allah ko kiyaye huruminsa ba, don haka ne Imam (a.s) ya nuna musu cewa hakki ne da shi kansa farji yake da shi a kan mutum ya kiyaye shi daga fadawa cikin halaka.

Sannan Imam Sajjad (a.s) ya yi nuni da wasu hanyoyin taimaka wa farji samun kariya daga sabon Allah da fadawa cikin halaka, sai ya yi nuni da kawar da duk wani abu da yake share fage ne zuwa ga kaiwa ga sabawa, yana mai cewa: "ka taimaka a kansa da rufe idanuwa, domin shi ne mafi taimakon abu", wannan magana ce da ta tattaro dukkan hikima. Domin masu hikima suna cewa: Kallo, sai magana, sai haduwa, sai auka wa juna.

Wato wanda ya hadu da wata mace farkon abin da yake faruwa tsakaninsu shi ne kallon juna, sai kuma su yi wa juna magana, sai su sanya inda zasu hadu, sai kuma su hadu kan sabon Allah. Wannan su ne matakai da suke kai wa ga saba wa Allah da keta huruminsa, da cin amanar farji da rashin kiyaye hakkinsa, sai Imam (a.s) ya yi umarni da yanke asasin farko shi ne kallon sha'awa da kawar da kai daga kallon juna.

Sai kuma ya gindaya wasu hanyoyi masu muhimmanci da zasu iya zama hanyar ladabtar da farji ya shiga taitayinsa, domin kawar da shi daga saba wa Allah da kutsawa cikin haram, yana mai cewa: "da kuma ba shi kariya da yunwa da kishirwa idan ya yi nufi, da yawaita ambaton mutuwa, da kuma gargadi ga kanka saboda Allah, da tsoratar da ita da shi, kariya da taimako suna ga Allah ne, kuma babu dubara ko karfi sai da shi".

Sai ya ginda ya masa wadannan hanyoyi masu kima da daraja da maganin taurin kan sha'awa wacce ba ta jin maganar hankali ba ta bin umarninsa, kuma ba ta jin gargadinsa. Sai ya fara da hanyar jiyar da ciki yunwa makoshi kuwa a shayar da shi magagin nan na kishirwa domin sha'awa kada ta tashi, domin idan ciki ya samu koshi ya cika, makoshi ya jike ya samu gamsuwa, to a lokacin ne ita kuma sha'awa zata motsa. Don haka ne hadisi madaukaki daga manzon rahama (s.a.w) kakansa (a.s) ya yi umarni da yin azumi domin rage kaifin sha'awa da maganin taurin kanta da takamarta, domin kada ta jefa samari cikin bala'in sabo.

Sannan ya yi nasiha da yawaita ambaton Allah domin zukata su samu nutsuwar biyayya ga Allah fiye da yadda suke samun nutsuwa da cin abin ci da shan abin sha, ko yin jima'i. Wanda duk ya dadani dadin ambaton Allah (s.w.t), to tabbas babu wani abu da zai nema a matsayin makwafinsa, domin dadin da rai take samu da nutsuwa da ubangijinta babu wani dadi da ya fi shi. Don haka ne ake iya sallamawa a bar duk wani dadi idan dai ya ci karo da kisa, amma sau da yawa ba a sallama wa dadin ambaton Allah koda kuwa za a fuskanci kisa.

Sai kuma mai aminci ya bi da ambaton sauran hanyoyi da suka hada da gargadin kai da yi mata fada don kada ta keta hurumin Allah, da tsoratar da ita wutar Allah da zafinta mai radadi idan ba ta ji ba, da kuma yin addu'o'in cewa Allah ya taimaka mana kan kare kawukanmu da iyalanmu daga wannan hari na sha'awa, kuma wannan ita ce mafi muhimmancin hanya da tafi sauran hanyoyi, domin babu wanda ya fi wanda Allah ya ba shi kariya karfi da tsayawa gaban harin sha'awarsa.

Babu wani abu da ya fi sha’awa karfi a cikin mariskai, idan ta kwashi mutum kai ka ce babu wani abu sai ita kadai, a lokacin jima’i dukkan wata gaba hatta da hankalin mutum yana koma wa zuwa ga wancan bangare na sha’awa ne, ta yadda dukkan wani abu na rayuwa zai kasance an manta da shi sai wannan bangaren kawai.

Sai dukkan gabobi su kasance sun tashi a wannan lokacin fiye da kowane lokaci, sai jinni ya rika gudana cikin sauri, fatar jiki ta tashi, lumfashi ya rika daukewa, kwayoyin halittar fushi su tashi, jin shafa ya kai kololuwarsa, sannan dukkan gabobin kasa su yankwane, jijiyoyi su motsa suna masu girgidi.

Sha'awa tana da hadari matuka a cikin ci gaban dan Adam, don haka ne addini ya yi nuni da hadarinta kuma ya tanadi maganinta, sai ya sanya hanyar aure har kala biyu: maras lokaci (da’imi har mutuwa) da na kayyadadden lokaci (mutu’a), kuma ya yi umarni da tsarkake farjin namiji da na mace bayan fitar abubuwa daga garesu kamar mani da bawanli da bayan gida, sabanin jiki kamar gumi da ba a sanya komai ba sakamakon fitarsa. Sannan kuma ita wannan sha'awa an sanya hukuncin haddi ga wanda ya biya mata bukata ba ta hanyar halal ba, sai aka sanya ukuba dukan dukkan jiki har sau dari ga wanda ya yi hakan, kamar yadda ya ji dadi da dukkan jikinsa ya yi sabawa.

Idan sha'awa mai karfi ta kama mutum takan sanya duk jijiyoyin jikinsa su tashi, jikinsa ya yi makyarkyata, hankalinsa ya makanci, zuciyarsa ta kurumci, don haka ne aka so toshe hanyoyin da zasu kai ga marhalar biyan bukatar haram da wannan sha'awar da wasu daga matakan da suka gabata. Bayan fitar mani sai jiki ya koma yadda yake a da, sai dukkan gabobin jiki su yi rauni, hankali ya kwanta, idanuwa su nemi yin bacci, sai jijiyoyi su nemi komawa yadda suke a da, don haka ne sai gajiya ta mamaye dukkan jiki.

A cikin maganar Imam Sajjad (a.s) zamu iya fahimtar samun wata alaka tsakinin gani da ciki da farji, domin su masu taimaka wa juna ne, idan aka rasa daya daga cikinsu, to bala'in sabo da yake faruwa sakamakon sha'awa yakan yi rauni ko ya mutu. Idan mun duba muna iya ganin cewa, sai an gani ake so, sai an koshi ake nema, sai da sha'awa ne ake aukawa. Don haka aka nemi kawar da gani, da neman taimako da rashin koshi, da kuma ambaton Allah da tuna mutuwa mai yanke jin dadi, domin a samu karayar sha'awa.

Zina ita ce samar da alaka kusaci da juna da jima'i tsakanin namiji da mace ba tare da aure ba, musulunci ya hana wannan alaka saboda muninta da samar da alaka maras karfi tsakanin namiji da mace, da haifar da yara da ba na shari'a ba da halacci wanda cutar hakan takan koma wa dukkan al'umma ne.

Al'ummu da yawa ne suke gaba da wannan lamari saboda muninsa, suke karfafar samar da alakar aure domin samun arzuta da rabautar al'ummarsu, da samar da aminci da zaman lafiya, da kawar da dukkan cututtukan da sukan iya haifuwa sakamakon alaka barkatai.

Har ila yau an hana zina domin mutane su fahimci kimar daukar nauyin iyali da yi musu hidima, domin idan da mutum namiji zai biya bukatarsa kawai sai ya kyale mace da daukar ciki da sauran wahalhalu da al'umma ta lalace, da an samu dora nauyi kan al'ummar mata wacce take ita ce mafi raunin rayuwa.

Musulunci ya dauki dukkan matakai da zasu kai ga zina, sai ya nemi gyaran kai da cika rai da tsoron Allah da ambatonsa, sannan ya nemi mata su rufe kyawawansu tun daga gashi har kafa, kuma ya nemi karanta cakuda tsakanin maza da mata ba tare da wani dalili ba.

Babban abin da yake hana sha'awa da yin maganinta shi ne cikar hankali da amfani da shi kan dukkan abin da muke fuskanta. Hadisai masu yawa sun yi nuni da wannan lamari mai girma da aka yi nuni da shi a cikin littafin Mizanul Hikima na Raishahari, j 3, shafi: 2052, kamar haka: "Idan hakali ya cika sai sha'awa ta ragu". "Wanda hankalinsa ya cika zai wulakanta sha'awowi".

Mazon Allah (s.a.w) ya ce: "Wanda ya yi zina da wata mata musulma ko bayahudiya, ko kirista, ko bamajusiya, 'ya ce ko baiwa, sannan bai tuba ba, kuma ya ci gaba da hakan, to Allah zai bude masa kofofi dari uku a cikin kabarinsa da macizai da kunamun wuta zasu rika fitowa suna saran sa da cizon sa, yana konewa har a tashi kiyama, idan kuwa aka taso shi daga kabari to mutane zasu cutu daga warinsa, sai a gane shi da wannan a kuma gane me yake yi a duniya, har sai a yi umarni da shi zuwa wuta. (Ma'arijun yakin fi Usuluddin: Sheikh Sabzawari, s; 408).

An karbo daga sayyidi Ali (a.s) ya ce: Mai tsira da aminci yana cewa: "Na hana ku zina, domin a cikinsa akwai abubuwa shida, uku a duniya, uku a lahira: Amma na duniya su ne: Tana tafiyar da kwarjini, Tana yanke arziki daga sama, Kuma tana gaggauta karewa. Amma na lahira su ne: Mummunan hisabi, Da fushin Allah, Da kuma dawwama a wuta. (Ma'arijun yakin fi Usuluddin: Sheikh Sabzawari, s; 408).

Jikin Mutum

Bayanan da muka kawo na maganganu masu daraja na Imam Sajjad (a.s) sun bayar da muhimmanci an gabobin da aka kawo a baya da suka hada da: harshe, ji, gani, hannu, kafa, ciki, farji. Wadannan gabobi masu hadari kuma masu kima da daraja suna matsayin hanyoyin da rai take amfani da su domin samun daraja da daukaka, ko kuma samun kaskanci da wulakanci, don haka ne bahasi kansu yake da matukar muhimmaci. Sai dai a nan zamu kawo bayanai game da su ta fuskancin jiki gaba daya ne.

Muna ganin muhimmancin gabobin jikin dan Adam ta yadda suka kasance kofar da za a bi domin tarbiyyar ransa, imam Zainul-abidin (a.s) ya nuna mana wannan domin fu fadaka game da wadanna bangarori na jiki, mu san kirmarsu da muhimmancinsu, da kasancewar gyaran kawuka ya doru a kan kiyaye su.

Jikin mutum yana da abubuwan da yake bukata na rayuwa domin ci gaba da samuwa, wadannan abubuwan idan babu su to karshensa ya zo ke nan. Yana bukatar abubuwa biyu na ciki da na waje, da kuma wani abu na uku da ya shafi rayuwarsa a matsayinsa na dan Adam.

Na ciki sun hada da ci, da sha, da magani domin waraka daga cututtuka, sai kuma abin da jiki yake furzarwa wadanda suke fita daga gareshi domin samun sauki kamar kashi, da bawali, da amai, da mani, ko wadi da mazi, da gumi ko zufa, da hawaye, da majina, da daudar kunne, da yawun baki.

Na waje kuwa sun hada da wanke dauda, da sanya tufafi kamar riga da wando, da takalmi da hula, da sanya abu mai kanshi kamar turare, da kayan ado kamar sarka da dan kunne, da awarwaro, da mai domin shafawa, da mai domin gyaran gashi, da jan farce. Kamar yadda yake bukatar wurin zama da inda zai samu rayuwa mai kyau da shakatawa, sannan ya samu wani abu da zai rage masa wahalar cirata daga wuri zuwa wani wurin kamar mota ko babur.

Amma a bangare na uku yana bukatar wasu abubuwa da suka shafi zaman tare na al’umma, da hukumar da yake karkashinta, idan mun duba irin wadannan abubuwan zamu ga suna cikin bayanai kamar haka:

Mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta kamar wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa, kuma yana bukatar kare duk wani abu da ya shafi jininsa, ko mutuncinsa, ko dukiyarsa. Amma sama da hakan akwai ‘yancin fadin ra’ayi da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci. Fadin ra’ayi yana kama da amai ko atisshawa ne da idan ba su fito ba to suna kumewa a cikin jiki, haka nan ra’ayi yakan zama ya kume a cikin tunani sai ya kasance wani bakin ciki da yake taruwa a cikin zuciya.

Akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wanda shi ne akidarsa, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari’a ko na hankali.

 Idan mun duba sai mu ga kowane bangare sai da shari’a ta ba shi matsayi na musamman domin kamalar mutum. Don haka ne a nan zamu yi nuni da wasu daga ciki a dunkule, mai son duba bayanai masu fadi sai ya koma wa littattafan shari’a.

Idan mun duba bukatun jiki na ciki sai mu ga shari’a ta muhimmantar da su ta yadda ta hana ci ko shan wani abu da yake cutarwa ko lahantawa, da yawa ayoyin da suka yi bayani kan haka a cikin littafi mai tsarki na Kur’ani, wasu ayoyin sun yi nuni da cewa: “… kuma ba a sanya muku kunci a cikin addini ba...”[1], wasu kuwa sun yi nuni da cewa: “... kuma yana haramta musu mai muni -cutarwa- ...”[2]. A nan muna iya cewa hatta da abu mai sanya maye da aka haramta a shari’a yana komawa ga cutuwar mutum a hankalinsa ko jikinsa ne.

Sai shari’a ta haramta dukkan mai sanya maye da mai cutarwa domin ta kare tarbiyyar mutum ta jiki da ta rayinsa, da gujewa sanya masa kunci a cikin rayuwarsa, da kaucewa ransa ko jikinsa daga fadawa cikin wahala da halaka.

Dogaro da wannan maslahar ne shari’a ta sanya wajabcin yin magani ga wanda ba shi da lafiya domin ba ta halatta masa cutar da kansa ko wata gaba ta jikinsa ba, don haka ne ta hana sayar da wani bangare na jikinsa wanda zai kai shi ga cutar da ransa ko jikin, sai dai idan babu cutuwa a ciki kamar sayar da wani bangare na jininsa.

Sannan hikimar Allah ta sanya masa wasu dokokin da zai samu sauki a cikin jikinsa kamar furzar da majina ko miyau, ko amai, ko kuma fitar da dauda da dattin da ya taru a cikin jikinsa ta hanyar bawali da bayan gida, ko kuma fitar da maikon da yana iya daskarewa ta hanyar gumi da zufa. Da ba a sanya masa hanyoyin da zai samu sauki ba da ya halaka, da rayuwarsa ta kare, amma sai ya kasance an ba shi hanyoyin sararawa.

 Sannan aka sanya masa hanyar sanyaya ransa da zuciyarsa ta hanyar yin kuka abin da yake ni’ima ce babba ga bayi da Allah ya yi musu. Kuma iyakacin bala’in da ya fada wa mutum da nauyinsa a kan zuciya ne ransa take bukatar fesar da shi ta hanyar yin kuka domin samun lumfasawa.

Ruwaya ta zo cewa: “Masu kuka mutum biyar ne...”[3]. Kuka wani abu ne da ake son yin sa domin wasu abubuwa da suka hada da tsoron Allah ga wanda ya tuna zunubansa, ko yayin wata musiba kamar mutuwa. Wasu mutane sun so hana kuka yayin mutuwa, sai dai wannan ya taso daga rashin fahimtar maganar manzon Allah ne da wani sahabi ya yi, sai Ai’sha matar Annabi (s.a.w) ta gyara masa cewa ba haka ake nufi ba, sai dai abin da aka hana a kukan mutuwa shi ne fadin abin da ya saba wa shari’a.

Wata hanyar samun lafiya da Allah ya sanya wa bayinsa ita ce hanyar fitar wasu abubuwa da shari’a ta sanya wanka saboda fitarsu, wadannan abubuwan sun hada da mani, da jinin haila da na haihuwa, da na istihala idan yana da yawa sosai. Akwai kuma wasu ruwa masu fita daga mutum da ba a sanya komai a kansa ba don sun fita, wadannan su ne mazi da wadi, kuma shari’a a bisa mahangar Ahlul-baiti (a.s) ta yi musu hukunci da tsarki.

Wasu kuwa an sanya yin tsarki ne saboda fitarsu wadannan abubuwan sun hada da bawali da gayadi, wadannan idan sun fita sai mutum ya yi tsarkinsu. Akwai kuma wasu halaye su ma da ake son wanda ya yi su ya yi alwala, wadannan abubuwan sun hada da yin bacci ko suma.

Amma abubuwan da suke daga wajen jiki sun hada da tsarkin daudar jiki, shari’a ta sanya tsarkake jiki daga dauda domin kada ya yi wari ya cutar da kansa da mutane. Wata ruwaya tana cewa da mu: “An gina addini a kan tsafta ne”[4], wata kuwa tana cewa: “Tsafta tana daga imani ce”[5]. Kazamin mutum ba ya samun kima da daraja a cikin mutane, mutane suna wulakanta wanda suka gani cikin kazanta komai kimarsa.

Akwai kuma kayan sawa da suka hada da riga da wando, da takalmi, da hula, da turare, da gashin mata, da sauran kayan ado kamar sarka da awarwaro da dan kunne, ko jan farce da sauransu. Shari’a dukkaninsu ba ta hana su ba, sai dai a tufafin mace ta wajabta mata rufe dukkan jikinta in banda fuska da tafuka.

Wadannan tufafin kowace al’umma tana da nata yanayin shiga, kuma dukkan shigar al’umma ba ta da wata matsala a shari’a matukar dai ba ta saba wa waccen doka da aka sanya wa mace ba. Al’adun Hausa mace tana iya sanya atamfa da dan kwali da zane, da mayafi, sai ta rufe duk jikinta da wannan, tana iya sanya wando ko ta hada zane da wando.

 Muna iya ganin a wasu al’ummun namiji ne yake daura zane mace kuma wando, wannan yana nuna mana kowace al’umma tana da nata yanayin shiga, kuma babu wata shiga da musulunci ya hana sai dai kawai ga mace idan zai kai ga bayyanar da jikinta da ya hana.

Wasu jama’un namiji yakan iya sanya gajeren wando da ‘yar riga, mace kuwa ta sanya siket da riga. Musulunci bai hana su wannan shiga ba, sai dai mace idan zata yi siket ya ja har kasa ta yadda zai rufe dukkan kaurinta har kafarta babu wani haramci a kan hakan, kanta kuwa da jikinta ta sanya riga zuwa karshen hannunta, ta sanya kuma abin da zai rufe kanta.

Muhimmi a cikin tufafi shi ne kiyaye wancan ma’anuni da musulunci ya sanya, idan aka kiyaye wannan babu wani tufafin wata al’umma da ya fi na wata. Babu bambanci, babban tufafi da karami duka daya suke, babu bambanci tsakanin babbar riga da kot da wando a wurin shari’a wannan duk yana komawa ga tunanin al’adun mutane ne.

Muna iya ganin yadda hula take da muhimmanci a wata al’umma, a wasu al’ummu girman mutum yana kan hularsa ne, da zai je taro babu hula to da kimarsa ta fadi ke nan. Amma a wasu al’ummu hula ba ta da wata kima ta a zo a gani, wasu suna ganin cewa sanya hula da dare yana haifar da matsala a ganin mutum, wasu sun tabbatar da matsalar yawan rufe gashi kodayaushe.

Amma wasu al’ummu idan ba su sanya hula ba suna ganin kamar ba su kammala ba, kana iya ganin mutum yana rufe kansa da zafin rana, kansa yana ta yi masa kaikayi amma ba zai cire hular ba, mafi muni shi ne likita yana iya hana shi sanya hula amma don kada al’umma ta gan shi karamin mutum sai ya sanya, haka nan al’adu suke cutar da al’ummu daban-daban.

Musulunci yana son tufafi ne na takawa, don haka kowace irin shiga al’umma take da shi ba shi da muhimmanci a wurinsa, abu muhimmi a nazarinsa shi ne takawar mutum, mutumin da yake sanya gajeren wando da karamar riga yana mai jin tsoron Allah da kiyaye dokokinsa shi ne abin so wurin Allah, amma mutumin da ya sanya rawani da alkyabba, ga babbar riga da mota mai tsada ba shi da wata kima wurin Allah sai idan shi ma yana da takawa.

Wannan ne ya sanya ma’aunin Allah da yake kallon bayinsa da shi ya saba da ma’aunin da mutane suke kallo da shi. Ma'aunin Allah ya doru bisa ganin dukkan halittarsa a daidai a cikin al'adunsu matukar ba su saba wa dokokinsa, amma tsukakken tunanin mutane yana girmama dan Adam ta cikin al'adu da abin duniya ne.

Idan muka waiwayi kayan adon mata haka nan babu wani ado da musulunci ya hana mace kowane iri ne, sai dai bai halatta ta bayyanar da adonta ga wasu mazaje ba sai dai ga mata ko mutane da suke muharramai kamar 'yan'uwanta, babu wani dan kunne ko sarka, ko man shafawa, ko karin gashi, ko rina gashi, ko jagira, ko jan farce, da sauran kayan ado da addini ya hana mace.

Sai dai namiji yana da dabaibayi da shari'a ta yi masa na cewa bai halatta ya sanya zenare ko azurfa ba, ko alhariri, don haka mace tana iya sanya zinare amma namiji bai halatta ya sanya shi ba. Zai iya yiwu wata al'ummar ya kasance namiji yana yin kitso ko ya sanya dan kunne da sarka ko awarwaro don adon namiji, shi ma a nan musulunci ya hana namiji sanya sarkar zinare, wannan haramcin na zinare ga namiji ba shi da bambanci a cikin al'ummu.

Game da wurin zaman rayuwa kamar gida, ko kuma wani abin hawa kamar mota, babu wani wanda Allah ya yi wa haramcinsa kamar namiji ko mace, a irin wannan abubuwan shari'a ba ta hana komai ba sai idan na haram ne. Idan gida ya kasance na kwace, ko filin kwace, to sai shari'a ta haramta zama da yin salla a cikinsa, kamar yadda ta haramta hawa motar sata ko ta kwace.

Wasu masu daskararren tunani game da musulunci sai suka hana mace tuka mota bisa jahilci, irin wannan jahilci ana yin sa a wasu kasase abin takaici da sunan musulunci. Kamar yadda zamu ga wasu kasashen ko kungiyoyi, ko ma wasu masu bayar da fatawa bisa tsukakken tunaninsu sun takaita kaya da irin na al'adarsu suna masu daukar cewa shi kadai ne na musulunci.

Amma a bangare na uku mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta da ya hau kan hukumar da yake rayuwa karkashinta ta samar masa da su, irin wadannan abubuwan sun hada da wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa.

Aminci wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam, idan babu shi to al’umma ba ta samun sukunin ci gaba. Don haka yana bukatar mai kare masa jininsa, da mutuncinsa, ko dukiyarsa. Kamar yadda yake matukar bukatar wanda zai kare masa ‘yancin fadin ra’ayinsa, da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci.

Sannan akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wato ‘yancin akida, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari’a ko na hankali. Kuma wannan akida wani abu ne da ya kafu a ransa, ya yi rassa a gabobinsa, don haka ne ba a tilasta mutum ya bar akidarsa, idan ana son gamsar da shi cewa akidarsa batacciya ce, to ya zama ta hanyar hankali ko hujjar shari'a.

Hafiz Muhammad Sa’id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Wednesday, June 16, 2010


[1] Hajji: 78.

[2] A'afar: 157.

[3] Almajalisul Fakhira: Sayyid Sharafuddin;s 150.

[4] Jami'us Sa'adati: Naraki; j 3, s 248.

[5] Annizamus Siyasi fil Islam: Bakir Sharif; s 295.