Tunatar da mutum Allah da abin da ya hau kansa a wannan duniya domin ya samu rabauta a lahira wani aiki muhimmi da annabawan Allah (a.s) da wasiyyansu (a.s) suka sanya gaba. Wani lokaci mukan kawo maganganu masu daraja sai mu yi bayaninsu dalla-dalla domin amfana daga garesu kamar yadda ya dace, amma wani lokaci sai mu bar su ba tare da kawo sharhi ba.
Sai dai mun ga yawan kawo sharhin yana amfanarwa matuka, don haka sai mukan yi nuni a wasu wurare koda ba dalla-dalla ba ne. A wannan hikima zamu ga Imam Ali (a.s) ya kawo abubuwan da mutum zai wadatu da su da sun ishe shi duniya da lahira. Kafin mu kawo sharhinsu zamu bar mai karatu ya duba su tukun kamar haka:
Imam Ali (a.s) ya ce da wani mutum da ya tambaye shi ya yi masa wa’azi: "Kada ka kasance daga wadanda suke neman lahira ba tare da aiki ba, suke jinkirta tuba da dogon buri, suke Magana game da duniya da fadin masu zuhudu, suke kuma aiki a cikinta da aikin masu neman lada. Idan an ba shi wani abu daga cikinta ba ya koshi, idan kuwa aka hana shi ba ya wadatuwa, yana kasa godewa kan abin da aka ba shi, kuma yana neman ba shi abin da ya yi ragowa, yana hanawa shi ba ya hanuwa, yana umarni amma shi ba ya aikatawa, yana son salihai amma ba ya aiki irin nasu, yana kin masu zunubi amma yana cikinsu, yana kin mutuwa saboda yawan zunubansa, yana kuma kana bin da yake kin mutuwa saboda shi, idan ya yi rashin lafiya sai ya yi ta nadama, idan ya samu lafiya sai ya shagaltu, yana jiji da kansa idan aka ba shi yalwa, yana yanke kauna idan aka jarrabe shi, idan bala’i ya same shi sai ya yi addu’a yana mai raki, idan kuwa yalwa ta same shi sai ya kawar da kai yana mai ji da kai, ransa tana rinjayarsa kan abin da yake tsammani, amma ba ya iya rinjayarta kan abin da yake da yakini, yana ji wa waninsa tsoro da abin da bai kai zunubinsa ba, yana so wa kansa ladan da ya fi karfin aikinsa. Idan ya samu yalwa sai ya yi girman kai ya fitinu, idan kuwa ya samu talauci sai ya yanke kauna ya yi rauni, yana takaitawa idan ya yi aiki, yana azuzutawa idan ya roka, idan wata sha’awa ta zo masa sai ya gaggauta sabo ya jinkirta tuba, idan kuwa wata jarabawa ta fado masa sai ya fita daga cikin tabbata da hakuri, yana siffanta abin lura –ga wasu- amma shi ba ya daukar darasi, yana zuzutawa a cikin wa’azi amma shi ba ya wa’aztuwa, shi mai surutu ne a magana, amma mai karanta aiki, yana ta gogoriyo da gasa a kan abin da yake karewa, yana mai sakaci da baya-baya kana bin da yake wanzuwa, yana ganin samu ramuwa, ramuwa kuwa samu. Yana jin tsoron mutuwa amma ba ya gaggauta samun dammar shirya mata, yana girmama sabon waninsa da abin da yake karanta abin da ya fi shi muni na sabonsa, kuma yana yawaita girmama da’arsa da abin da yake rena da’ar waninsa da shi. Shi dai mai sukan mutane ne, mai yabon kansa, wasa da masu kudi ya fiye masa ambaton Allah tare da talakawa. Yana yi wa waninsa hukunci –ya ba shi laifi- don amfanin kansa, amma ba ya yi wa kansa hukunci -da rashin gaskiya- don amfanin waninsa, yana shiryar da waninsa yana halakar da kansa, shi ana bin sa amma yana sabo, yana neman a cika masa shi ba ya cikawa, yana tsoron halitta ba don ubangijinsa ba, amma ba ya tsoron ubangijinsa a kan halittarsa". Nahajul-balaga: Nahajul-balaga: Hikima: 142.
Muhammad Abduh yana cewa: Da babu wani abu a cikin wannan littafin sai wannan maganar da ta isa wa’azi mai amfani, da Nahajul-balaga: Hikima mai balaga, da basira ga mai neman ganin haske, kuma darasi ga mai lura mai tunani.
A nan ne zamu kawo sharhin abin da ya gabata a takaice kamar haka; fadinsa mai aminci "Kada ka kasance daga wadanda suke neman lahira ba tare da aiki ba, suke jinkirta tuba da dogon buri, suke magana game da duniya da fadin masu zuhudu, suke kuma aiki a cikinta da aikin masu neman lada". Wadannan siffofi ne munana da babu wasu da suka kai su muni, domin duk sun doru a kan karyar aiki da zance, kuma babu wani sabo da ya kai karya muni.
Sannan wadannan dabi'u ne da suka kafu kan riya, da ha'intar kai, da neman suna da daukaka bisa karya, domin wanda yake nuna zuhudu alhalin dan duniya ne, ko yake nuna ayyukan alheri amma ba ahalinsa ba ne, babu mayaudari kamarsa. Sannan akwai wanda ya fi kowa yaudarar kansa a cikin wannan kalami, wannan kuwa shi ne mai jinkirta tuba, yana dauka cewa; za a jinkirta masa har sai sanda ya shirya mutuwa sannan sai ya tuba. Yana mai mantawa cewa Allah yana da nasa sha'anin shi kuma yana da nasa daban, Allah yana da sha'ani a kullum, a kowace awa, a kowane minti, haka nan dan Adam, kuma idan aka samu karo da juna to na Allah ne yake rigaya, domin shi ne ainihin sha'anin da aka shirya zai wakana a halittarsa, don haka jinkirta tuba fitina ce mai girma, halaka ce ta kusa.
Imam Ali (a.s) ya ci gaba da kawo wadannan siffofi munana yana mai cewa: "Idan an ba shi wani abu daga cikinta ba ya koshi, idan kuwa aka hana shi ba ya wadatuwa, yana kasa godewa kan abin da aka ba shi, kuma yana neman ba shi abin da ya yi ragowa, yana hanawa shi ba ya hanuwa".
Wadannan siffofi sun munana kwarai, domin rashin godiya da ruwa su ne asasin kashe addini da imani. Muhimmancin godiya ne ya sanya ubangini ya sanya abu na farko bayan kiran suanyensa shi ne a yi masa godiya kamar yadda muke karantawa a cikin surar Fatiha, domin bayan yarda da cewa akwai ni'imar samuwa, da rayuwa, da ni'imar abubuwan da rayuwa ta tsayu a kansu kamar ruwa da iska, da abin ci da abin sha, da tufafi, da kasa, da gida, da sama, da sauransu, sai godiya ga mai wannan ni'imar ta biyo baya.
Don haka ne ba a takaita wannan godiya ga ubangijin talikai ba, sai aka yi umarni da yin godiya ga dukkan wanda ya kasance wasidar ni'ima. Wannan godiya tana iya kasancewa ta aiki kamar fadin mutum "godiya ta tabbata ga ubangijin talikai, ko ta magana kamar yin sadaka da kyauta da rashin yin ruwar ni'imar Allah da arzikinsa da ya hore wa mutum, ko godiyar yarda da zuciya wacce take mafi muhimmancin duka kamar nutsuwa da dukkan abin da Allah ya hore wa mutum da wadatar zuci, ta yadda yakan samu nutsuwa da rashin da yake da shi fiye da nutsuwar mai wadata da wadatar da yake da ita, sai bakin cikinta ya tsaya a zuciya, amma farin cikinsa yana kan fuskarsa, ga shi da tarin matsaloli amma mutane sukan dauka mawadaci ne.
Sannan nau'in godiya yana kasancewa ne gwargwadon wanda ya yi ni'ima da girman ni'imarsa, da kuma sanin wanda aka yi wa ni'ima da girman wannan ni'ima, domin da yawa jahiltar ni'ima ko jahiltar mai ni'ima yakan sanya rashin godiya ga mai ni'ima ko godewa wani maimakon mai yin ni'ima kamar dai yadda mushrikai suke godiya ga gumakansu. Wani lokaci kuwa wannan jahilcin yakan sanya godewa wanda ya cutar da mutum a matsayin mai ni'ima, don haka ne ma a lahira yayin da za a yaye hijabi sai ga masoya na kut-da-kut sun koma makiya na faufau, wasu kuwa da suka kasance an yi gaba da su sai wannan gabar ta koma nadama.
A nan ne zamu ga babu wani wanda ya kai butulcin mai rowa, domin shi ya rasa godiyar zuci, da ta magana, da ta aiki, sannan ya munana zato ga Allah, ya kuma takura bayinsa. Allah ya sanya ni'imar wasu mutane ta hannun wasu ne, sai dai marowaci yana hana ni'imar isa ga wadanda aka sanya ta hannunsa ne ni'imarsu zata zo, don haka sai ya fadi a jarabawa, bai gode wa Allah ba, bai godewa mutane ba da shi ta shi ni'imar ta hannunsu ta iso masa, bai kuma kimanta Allah da ya ba shi ba, bai kuma kimanta hakkokin mutane da suke kansa ba.
Da wannan ne zamu ga munin rowa ya fito a fili, da rowa ne aka kashe addini, da rowa ne aka kashe mutunci aka jefa mutane cikin bara, da fatara da talauci, da rowa ne aka kafirce wa Allah aka jefa wasu barin addini yayin da suka ga godiya da kyauta ta wani addini, da rowa ne aka jefa miliyoyi barin kasashensu.
Sannan imam Ali (a.s) ya ci gaba da nuni ga wadannan miyagun halaye yana mai cewa: "yana umarni amma shi ba ya aikatawa” shi wannan mutum mai munanan halaye yana da kokari wurin ganin ya ba wa wasu umarni da kyakkyawa da hana su mummuna amma shi ba ya aiki da wannan.
Sannan yana “, yana son salihai amma ba ya aiki irin nasu, yana kin masu zunubi amma yana cikinsu”, wannan ma yana daga munanan halayensa, mutum ne wanda yake son salihai kamar yadda ya raya, kuma yana kin masu zunubi kamar yadda ya raya, amma karya yake yi, domin da ya kasance mai gaskiya da ya yi aikin salihai, kuma ya nisanci zunubi. Domin duk wanda yake da’awar wani abu to babu wata hanyar gane gaskiyarsa sai ta hanyar aiki da abin da yake da’awarsa, amma idan aka ga sabanin haka, to wannan mutumin karya yake.
Sannan sai imam Ali (a.s) ya ce: “yana kin mutuwa saboda yawan zunubansa, yana kuma kan abin da yake kin mutuwa saboda shi”, sau da yawa idan mutum ya fiye kin mutuwa ya wuce iyaka wurin tsoron saboda ya san abin da ya tanada ba shi da kyau ne, domin kowane mutum yana kin mutuwa, sai dai shi wannan kin nasa ya fita daban ne. Sabuban kin mutuwa suna da yawa amma shi nasa dalilin ba shi da madogara domin ya taso daga zunubai da yake yi kuma ya ki daina su, yana tsoron kada ya mutu ya sha kulki.
Sannan sai imam (a.s) ya ce: “idan ya yi rashin lafiya sai ya yi ta nadama, idan ya samu lafiya sai ya shagaltu”, wannan yana nuna tsananin butulcin wannan mutumin, domin idan ya samu lafiya mai makon ya ji tsoro sai ya shagaltu, amma idan ya samu rashin lafiya a lokacin yake jin tsoro. Sai ya kasance yana muhimmantar da duniya da kayanta a kan lahira da sakamakonta. Kamar dai yana ganin lafiya dama ce domin sabo, rashin lafiya kuwa tsayawar wannan damar ce.
Sannan sai Imam (a.s) ya ce: “yana jiji da kansa idan aka ba shi yalwa, yana yanke kauna idan aka jarrabe shi, idan bala’i ya same shi sai ya yi addu’a yana mai raki, idan kuwa yalwa ta same shi sai ya kawar da kai yana mai ji da kai”, shi mutum ne mai takama da kansa saboda abin da Allah ya ba shi, wannan kuwa ita ce siffar Karuna da yake takama da dukiyar da aka ba shi, har ya yi da’awar cewa iliminsa da dubararsa ne suka ba shi, amma idan kana son ka ji rakinsa to a lokacin ya samu wata fatara da talauci.
Sannan sai imam (a.s) ya ce: “ransa tana rinjayarsa kan abin da yake tsammani, amma ba ya iya rinjayarta kan abin da yake da yakini,”, wannan mutumin rashin adalcinsa ya yawaita, idan yana da yakini kan wata gaskiya sai ya boye, amma idan yana kin abu sai ya ki shi koda kuwa da tsammani ne. Wannan mutum halakakke ne kuma tababbe, shi mutum ne mai tsananin kin gaskiya da kauce mata, ba shi da wani amfani sai dai la’anar Allah ta hau kansa.
Sannan sai imam (a.s) ya ce: “yana ji wa waninsa tsoro da abin da bai kai zunubinsa ba, yana so wa kansa ladan da ya fi karfin aikinsa”, wannan mutumin yana da wauta matuka, domin yana ji wa wasu tsoron shiga wuta da zunubin da suke yi wanda bai kai nasa ba, sannan yana da zari domin yana so wa kasa sama da abin da yake cancanta na ladan aikinsa”.
Sannan fadin imam (a.s) cewa: “Idan ya samu yalwa sai ya yi girman kai ya fitinu, idan kuwa ya samu talauci sai ya yanke kauna ya yi rauni, yana takaitawa idan ya yi aiki”, wannan mutumin yana da mai ha’inci ne, domin idan aka ba shi aiki sai ya yi coge, sai ya ki yin sa yadda ya dace da shi”.
Sannan sai imam (a.s) ya yi nuni da wasu munanan halaye kamar raki ta hanyar zuzuta abu, da jinkirta tuba ta yadda idan ya ga sabo sai ya ce bari in yi in ya so sai in tuba, da gajarcin hakuri ta ydda da wani abu ya faru gareshi sai ya ki hakura, yana mai ganin cewa shi kamarsa ba a isa a yi masa wani abu ya bari ba, wannan kuwa yana nuna girman kansa a lokaci guda, sannan duk wani abu da ya gani ya faru kan wasu shi ba ya daukar darasi. Fadin imam Ali (a.s) yana nuni da wannan yayin da yake cewa: “yana azuzutawa idan ya roka, idan wata sha’awa ta zo masa sai ya gaggauta sabo ya jinkirta tuba, idan kuwa wata jarabawa ta fado masa sai ya fita daga cikin tabbata da hakuri, yana siffanta abin lura –ga wasu- amma shi ba ya daukar darasi”.
Amma fadinsa (a.s) cewa: “yana zuzutawa a cikin wa’azi amma shi ba ya wa’aztuwa, shi mai surutu ne a magana, amma mai karanta aiki”. Daga cikin mummunan halin wannan mutum shi ne ya fiye karadi da surutu marasa amfani, amma a aiki yana ziro ne.
Sannan fadin imam (a.s) cewa: “yana ta gogoriyo da gasa a kan abin da yake karewa, yana mai sakaci da baya-baya kan abin da yake wanzuwa, yana ganin samu ramuwa, ramuwa kuwa samu”. Nuni da cewa mai wannan mummunar siffa bai damu da lahirarsa ba, ba shi da wani abu da yake muhimmi da ya sa gaba sai neman duniyarsa, don haka ne duk inda ya sa kokari to kan mai karewa ne, duk inda ya ja baya to kan mai wanzuwa ne.
Sannan sai Imam (a.s) ya fadi cewa: “Yana jin tsoron mutuwa amma ba ya gaggauta samun damar shirya mata, yana girmama sabon waninsa da abin da yake karanta abin da ya fi shi muni na sabonsa, kuma yana yawaita girmama da’arsa da abin da yake rena da’ar waninsa da shi”. Nuni da wasu abubuwa da suka gabata ne a takaice na sakaci da lahira da muhimmantar da duniya, da kuma duba wasu mutane ya yi wa ayyukansu hukunci kamar shi ne ubangijinsu alhalin ya mance da nasa ayyukan.
Haka nan fadinsa (a.s) cewa: “Shi dai mai sukan mutane ne, mai yabon kansa, wasa da masu kudi ya fiye masa ambaton Allah tare da talakawa”. Wannan yana nuna cewa wannan mutumin dan duniya ne, mai son rai da son kai, domin shi ba ya ganin kansa da wani aibi, amma sauran mutane su masu aibi ne da tawaya. Sannan kasancewar wasa da masu kudi ya fiye masa zama da talakawa domin ambaton Allah yana nuna mana cewa wannan mutumin dan duniya ne ba dan lahira ba ne.
Sannan fadin Imam Ali (a.s) cewa: “Yana yi wa waninsa hukunci –ya ba shi laifi- don amfanin kansa, amma ba ya yi wa kansa hukunci -da rashin gaskiya- don amfanin waninsa”, yana nuna gaskiyar magana kan cewa shi mutum ne mai tsananin son kai.
Amma a lokaci guda kuma wannan mutum jahili mai jahiltar kansa da mutuncinsa, duba fadin Imam Ali (a.s) game da shi yayin da yake cewa: “yana shiryar da waninsa yana halakar da kansa, shi ana bin sa amma yana sabo, yana neman a cika masa shi ba ya cikawa, yana tsoron halitta ba don ubangijinsa ba, amma ba ya tsoron ubangijinsa a kan halittarsa". Tabbasa wadannan mugayen siffofi da halaye na son rai, da son zuciya, da jahilci, da riya, da zamu samu cikin wadannan kalmomi babu wata siffa ko hali da suka kai su muni.
Don haka ne zamu ga magana mai muhimmanci daga Muhammad Abduh yayin da yake cewa: Da babu wani abu a cikin wannan littafin sai wannan maganar da ta isa wa’azi mai amfani, da hikima mai balaga, da basira ga mai neman ganin haske, kuma darasi ga mai lura mai tunani.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Wednesday, June 16, 2010