Game Da Nahjul Balaga

Menene Nahajul Balagha Ya Kunsa?

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai. Wannan da Ya halicci wadansu nau'i na bayin Allah Salihai, Ya kuma hore masu hikima da luraswa da kuma shiryarwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban Manzanni, Muhammad Dan Abdullah (S.A.W) da Alayen gidansa tsarkaka da kuma sahabbansa managarta.

Mutane da dama daga cikin al'ummar musulmi na wannan bangaren na wannan nahiyar ta duniyar musulmi, a sabili da wadansu dalilai da za a iya fahimta, idan suka ci karo da wannan rubutun za su so su yi tambaya, shigen irin wannan; Menene Nahajul Balagha? Wannan kuwa zai iya kasantuwa haka a sabili da cewa mafi yawa daga cikin irin wadannan mutanen da muke nufi a nan kila a wannan dan lokacin ne da muke a ciki yanzu suka soma jin wani abu mai suna Nahajul Balagha a karon farko daga bakunan ma'abota addini ko kuma kilan ma wasunsu daga shigen irin wadannan rubuce-rubucen ne suke soma cin karo da wannan suna.

To a takaice dai, Nahajul Balagha sunan wani littafi ne wanda Sayyid Sharif Abul Hasan Radi Bin Al-Husaini Al-Musawi (R.A) ya rubuta fiye da shekaru dubu da suka shige, inda ya har-hada wadansu daga cikin zababbun zantukan hikima na Amirul Muminina, Imam Ali Ibn Abi Dalib (A.S) wadanda ya furta a wurare da kuma lokuta daban-daban na tsawon rayuwarsa. Duk da yake kuwa cewa an har-hada littafin ne kashi uku a matsayin hudubobi da wasiku da kuma kalamomin hikima na Imam Ali (A.S), amma kari a kan wannan, bincike ya nuna cewa littafin kuma ya hada har da hadisai, wasiyyoyi, wa'azozi, jawabai, nasihohi, gargadi da kuma sauran zantukansa masu alfarma.

A duk fadin rubuce-rubucen addinin Musulunci da aka yi tun farkon tsawon shekarun Musulunci, bayan Alkur'ani mai tsarki da hadisan Manzon Allah (S.A.W), babu wani littafi a bayan kasa wanda yake kunshe da shiryarwa da hikimomi da basira da luraswa da kuma fahimtarwa kamar Nahajul Balagha. Nahajul Balagha littafi ne da yake tattare da bayanai da fahimtarwa kan Alkur'ani mai tsarki. Da bayanai da fassara kan hadisan Annabi (S.A.W) da kuma bayanai da luraswa kan al'ummomin da suka gabata, da makamantansu.

Kai littafin Nahajul Balagha ma ya fi kowane littafi kusanci da Alkur'ani mai tsarki, ya kuma fi kowane littafi kusanci da hadisan Annabi (S.A.W). Domin ba komai bane ke a cikin Nahajul Balagha face zantukan Imam Ali (A.S) masu alfarma wanda yake shi ne Manzon Allah (S.A.W) aka ruwaito yana cewa game da shi; “Ali huwal-qur'anun nadik” wato “Ali shi ne Alkur'ani mai Magana”. Wannan ya nuna cewa a zamanin Manzon Allah (S.A.W), bayan Manzon Allah (S.A.W) ba wanda ya san Alkur'ani sani na hakika kamar Imam Ali (A.S). Kamar kuma yadda a wani wuri aka ruwaito Manzon Allah (S.A.W) yana cewa game da Imam Ali (A.S); "Ana madinatul ilmi wa Aliyyun babuha" wato "Nine birnin ilimi, kuma Aliyyu shi ne kofarta." Ka san kuwa duk mai son shiga birni, in dai ba keta ka'ida zai yi ba, to dole ne ya bi ta kofar birnin. Har wala yau kuma an ruwaito Manzon Allah (S.A.W) yana cewa game da Imam Ali (AS); "Ba wanda ya san Allah kamar Ni da Aliyyu. Ba wanda ya san Ni kamar Allah da Aliyyu. Ba kuma wanda ya san Aliyyu kamar Allah da Ni." Ka ga kenan Imam Ali (A.S) shi ne kadai na biyun Manzon Allah (S.A.W) a sani na ilimin addinin Musulunci.

Duk da yake kuma cewa ana samun littafin Nahajul Balagha jefi-jefi a wadansu zaurukan karatun ilimi a cikin wannan al'umma da muke a ciki, amma za a tarar da cewa mafi yawan Malaman da ke amfani da littafin sun takaita ne da bincike-bincikensu kan wadansu fagage na ilimin Larabci, kamar ilimin adabi da sauransu, wadanda su ma suke tattare a cikin littafin. Ba kasafai suke kula da bincike a kan hadisai masu yawa da kuma bayanai na shiryarwa wadanda littafin ya kunsa ba. Ba kuma kasafai suke kula da kalamomin hikima da kuma fadakarwa da littafin ya kunsa ba, musamman kuma a gaba daya, ba a kula da bincike a kan wadansu fade-fade na wadansu abubuwa da za su auku a nan gaba a cikin gewayen Musulunci da kuma a duniya baki daya wadanda littafin ya fada ba. Hakika da yawa daga cikin wadannan abubuwa da ya fada a cikin littafin Nahajul Balagha sun auku a zamanin Imam Ali (A.S), da yawa kuma sun auku bayan shahadarsa, sannan kuma da yawa suna nan suna aukuwa a wannan zamanin namu.

Nahajul Balagha ya kunshi mas'aloli daban-daban wadanda suka hada da manya-manyan matsalolin falsafar zamantakewar jama'a, ilimin kalami, ilimin fikihu, ilimin tafsir, ilimin hadisi, ilimin Annabtaka, ilimin Imamanci, ilimin halayen kirki (Akhlak), ilimin tarihi, ilimin siyasa, ilimin shugabanci, ilimin tafi da jama'a, ilimin iya magana, ilimin rubutattun wakoki, ilimin adabi da sauransu. Mafi yawan bayanai a kan matsalolin ilimin kalami da fahimce-fahimcen falasafa daban-daban a Musulunci suna da asali a cikin wannan littafi. Haka nan kuma dukkanin zantukan sarari a kan matsalolin zamantakewar siyasa a cikin al'ummar musulmi da kuma Hukuma sun bar gurbinsu a cikin Nahajul Balagha, ko kuma suna da dangantaka da kalaman Imam Ali (AS).

A takaice, Nahajul Balagha littafi ne wanda yake a matsayin wata hanya ta sanin Allah Madaukakin Sarki (S.W.T), da sanin kasantuwa ta duniya da muke ciki, da sanin tsare-tsaren hukumomi da al'ummomi, da sanin hukunce-hukuncen shari'a, da sanin halayen kirki, da kuma sanin tarihi, da makamantansu.

A wannan dan rubutu a matsayin gabatarwa na wannan littafin mai alfarma, muna son ne mu dan gabatar da maudu'ai wadanda suka hada da: Wanene marubucin Nahajul Balagha, da takaitaccen tarihin Imam Ali (AS), da wasu daga cikin hudubobi da wasiku da kuma kalamomin hikima na Nahajul Balagha wadanda Imam Ali (AS) ya furta kan Ubangiji (S.W.T), da Manzon Allah (S.A.W), da Iyalan gidan Manzon Allah (A.S), da wasu daga cikin shahararrun hudubobi da jawabai da kuma wasiku na Nahajul Balagha, da sauransu.

Sannan kuma da wadansu daga cikin shahararrun zantukan Imam Ali (AS) wadanda suke da nasaba da fannonin kimiyya da fasaha da kuma sauran nau'o'in ilmomi daban-daban da ake da su a wannan zamani. Da kuma littafan da aka tsamo zantukan Imam Ali (AS) na Nahajul Balagha. Sannan da rubuce-rubuce da kuma sharhohin da aka yi wa Nahajul Balagha da dai sauran bincike-bincike masu amfani.

Manufarmu a wannan dan bincike shi ne gabatar da dan rubutu a matsayin gabatarwa na littafin Nahajul Balagha domin wannan al'umma su amfana da dan abin da za a gabatar masu a wannan dan rubutu. Sauran binciken kuma ga mai bukatar karin bincike, sai a nemi gundarin littafin da sharhihohinsa domin karin bayani.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria
Hfazah@yahoo.com