Daga Hudubar Farko ta littafin Nahajul-balga da take nuna mana girman Allah da kuma Kasawar Dan Adam Ga Sanin Zatin Ubangiji, da hikimominsa a ayyukansa.
"Godiya ta tabbata ga Allah wanda masu magana suka kasa fadar kalmar yabo wadda ta cancanta gareshi" Ubangiji madaukaki shi ne abin godewa da yabo a kowane hali ne, wannan yabon nasa yana iya kasancewa yabon zuci, ko na aiki. Sannan kuma dukkan halitta tana gode masa imma dai tana sane ko kuma ba ta sane, kuma wannan godiyar tana nuna mana yarda da furuci da ni'imomin Allah kan bayinsa ne.
Sannan duk inda muka kai domin mu kirga wannan ni'imar ta Allah ba zamu iya ba, kuma duk yadda muka yi kokarin sauke nauyin hakkin Allah a kanmu ba zamu iya ba, don haka ne Imam Ali (a.s) yake cewa: "sannan masu lissafi suka kasa lissafa ni'imominsa, kuma masu kokari suka kasa aiwatar da hakkinsa a kansu".
Mutum halitta ce mai ban al'ajabi, Allah ya yi mutum da tunani da hankali, Amma duk wani abu da zamu sawwala a cikin tunaninmu, ko mu kaddara a cikin saken tunaninmu Allah sabanin haka ne, domin babu yadda zamu sawwala wani abu sai mun ba shi iyaka a tunani. Sirrin haka kuwa saboda ita ranmu tana da iyaka, kuma ba ta iya riskar abin da ba shi da iyaka. Don haka ne Imam (a.s) yake cewa: "wanda masu zurfin tunani suka kasa sanin hakikanin zatinsa, kuma masu nutso a cikin kogin ilimi ba zasu taba isa zuwa ga zatinsa ba".
Sannan kamar yadda ba za a iya sanin zatin ubangiji ba sakamakon cewa ba shi da iyaka a samuwarsa da kamalarsa, haka nan siffofinsa suke, domin siffofi suna bin zatin da ta siffantu da su ne, don haka ne zamu ga Imam yana cewa: "wanda suffofinsa ba su da iyaka da aka iyakance, ko wata siffa ta samammu ko wani lokaci kididdigagge, ko wani ajali iyakantacce".
Sai ya yi nuni zuwa ga wasu abubuwa masu muhimmanci a nan da cewar, tunda mai wadannan siffofin ba shi da iyaka, to su ma ba su da iyaka, kuma tunda ba su da iyaka, to babu ma'anar kididdiga shi da kirga shi, domin kirga da kididdiga suna zuwa ne inda wani abu ya tuke, kamar idan aka samu na farko, to farkon inda ya tuke to nan ne zai kasance farkon mafarar na biyu. Kuma wannan yana nuna mana cewa; zamani bai kewaye shi ba balle a ce masa a yaushe? wuri bai tattaro shi ba balle a ce masa a ina?.
Wadannan siffofi na kamala da girman Ubangiji kowacce daga cikinsu tana kasance mafarar samar da wasu abubuwa ba tare da an samu kididdiga ko yawaita a cikin zatin Allah ba, domin kudurarsa ta wata fuskar iliminsa ce, haka ma akasin hakan. Sai dai kowace siffa tana aiwatar da abin da ya dace da ayyukanta, sai ya san abu don yana da ilimi, sai ya yi afuwa da gafararsa, sai ya halakar da kasancewarsa mai tsananin riko, sai ya yi halitta don yana da iko da kudura, kamar fadinsa (a.s) cewa: "Ya halicci halittu da kudurarsa, ya sanya iska yana kadawa da rahmarsa, kuma ya kafe duniya da duwatsu da ya sanya a bayan kasa".
Addini Da Sanin Ubangiji
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya shiga bayanin addini da sanin ubangiji yana mai bayyana farkon abin da ya dace daki-daki wanda ya hau kan mutane su kiyaye yana mai cewa: "Abu na farko a cikin addini shi ne sanin Allah, sannan kamalar sanin Allah shi ne gasgatawa da shi" sai ya sanya sanin Allah shi ne farko, amma kuma yana tare da gaskatawa da Allah, wannan yana nuna cewa duk wani sanin Allah da ba ya tare da gaskatawa da shi sani ne nakisi maras kamala.
Amma fadinsa (a.s) cewa: "kuma cikar gasgatawa da shi, shi ne kadaita shi, sannan kamalar kadaita shi, shi ne tsarkake shi, cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) daga gare shi", nuni ne da cewa wanda duk bai kore siffofin halitta ga Allah ba, to hakika bai tsarkake shi a zatinsa, da siffofinsa, da bautarsa, da tafiyar da lamurran bayi.
Domin idan ya ba wa Ubangiji madaukaki siffar bayi, kamar ya siffanta shi da cewa jiki ne, ko kuma yana tafiya yana saukowa kamar mutum, ko yana kan al'arashi ko kursiyyu, kamar yadda jahilai suka dauka, ko ya siffanta da mahalli ko zamani, ko ya sanya shi iyakantacce ta yadda har ma ana iya hango shi, ko ya karanta kamalarsa kamar ya sanya shi yana jahiltar abubuwa ko ya yi fada da kokawa da bayinsa, to wannan mutumin ya kafirce wa Allah madaukaki.
Da wannan kuma sai mu fahimci cewa, tun da ya siffanta Allah da siffofin tawaya na bayinsa, kuma ya suranta shi a tunaninsa, ya ba shi iyaka da bukatuwa ke nan. Kuma tun da ya ba shi irin wadannan siffofi na tawaya, to sai ya bauta wa wani abu mai wannan surar da take cikin kwakwalwarsa, sai ya kasance ke nan abin bautarsa ya zama tamkar wani gunki ne a tunaninsa da ya saka shi, sannan sai ya bauta masa. Bambacinsa da kafiran Kuraish shi ne su sun saka nasu gumakan da katako da tabo, shi kuwa ya saka nasa da tunanin zucinsa.
Da wannan ne muka ce bai tsarkake Allah ba, domin bai tsarkake shi daga dukkan tawaya ba, tawaya daya ce ko suna da yawa, a game da siffanta Allah wajibi ne a yi taka tsantsan, domin tawaya daya da aka jefa masa tana mayar da shi daga cikin nakasassu ba kammalallu ba, da wannan ke nan sai ya kasance daya daga cikin masu tawaya da suke bukatar kamala da mai kammala su, sai ya tashi ke nan ba shi ne Allah madaukaki ba.
Idan mun fahimci wannan sai mu gane a fili yake cewa lallai sai an kore masa siffofin tawaya sannan za a tsarkake shi, sannan kuma zamu gane cewa ashe ke nan sai an tsarkake shi za a kadaita shi kamar yadda ya gabata. Sannan sai an kadaita shi za a gaskata shi, kuma sai an gaskata shi za a san shi, wannan ne ya sanya zamu ga abin da yake shi ne madogara ga mai biye masa ya zamanto kamalarsa kamar yadda Imam (a.s) ya fada cikin maganarsa mai daraja.
Amma fadinsa cewa: "saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba shi ne abin siffantawar ba". Yana nuni ne zuwa ga cewa duk wata siffa da abin halitta yake siffantuwa da ita ta koru ga Allah, saboda cewa shi ubangiji ba shi ne mai wannan siffar ba, kuma masu siffantawa sun yi sheda da cewa wannan siffar ba ita ubangiji ba.
Idan muka duba zamu ga an yi sabani game da siffofin Allah madaukaki, da cewa shin Allah yana da siffofi ko kuma ba shi da siffofi. Wato shin siffar ilimi da muke siffanta Allah da ita tana nufin Allah masani ne, kuma ya siffantu da siffar sanin, ko kuwa siffar ilimi suna ne daga sunayen Allah ta yadda ba ma fahimtar komai sai dai kawai lafazin ne muke da shi da yake nuna mana wani suna daga sunayen Allah madaukaki?
A gaskiyar magana a nan ita ce Allah yana da siffofi, kuma wadannan siffofin nasa na kamala ne da suke tabbatar masa da matsayinsa na kamala maras iyaka. Domin idan muka kore wadannan siffofi na Allah to zamu cire masa dukkan wata kamala, misali idan muka cire masa siffar ilimi sai mu mayar da shi jahilci, alhalin Allah shi ne ainihin ilimi maras iyaka. Haka nan sauran siffofin da suka hada da iko, da gani, da ji, da magana, da sauransu.
Kuma da yake siffofin sun kasu zuwa ga siffofin kamala tabbatattu da siffofin jalala korarru, sai masu tunanin kore siffofin Allah suka ce wadannan siffofin na kamala suna komawa siffofin jalala ne, ta yadda ida ka ce Allah masani ne, to wannan yana nufin ba jahili ba ne, amma a lokaci guda ba yana nufin masani ba ne.
Sai masu wannan tunani suka fada cikin babbar fitina ta hanyar kore duk wata kamala daga Allah, sai ya kasance yana bayar da kamala ga bayinsa alhalin shi bai siffantu da ita ba, sun mance cewa kore tawaya yana nufin tabbatar da kamala ne.
Misali idan muka ce Allah ba jahili ba ne, yana nufin Allah masani ne, idan muka ce Allah ba ajizi ba ne, wannan yana nufin Allah mai iko ne. Haka nan idan muka juya muka ce Allah mai iko ne, wannan yana nufin Allah ba ajizi ba ne, kuma idan muka ce Allah ba jahili ba ne yana komawa zuwa ga Allah masani ne. Don haka kore tawaya yana komawa zuwa ga tabbatar kamala, kamar yadda tabbatar kamala yana komawa zuwa ga kore tawaya ne.
Don haka bayan duk wannan bayanin sai mu ga akwai siffofi kala biyu da wata ma'anar, siffofin da ake siffanta Allah da su da ake kiransu da siffofi khabariyya, wadannan siffofi Allah madaukaki ne ya bayar da labarin cewa yana da su, sai dai suna daukar tawili ne kamar siffar nan ta hannu, da yake cewa: "… na halitta da hannuna…". Wadannan su ne siffofin da suke da ma'anar da ta zo a littattafan adabi na larabci, da take nuna idan aka ce hannu yana nufin karfi da iko, don haka sai ya kasance Allah da ikonsa ne ya halicci wannan halitta ta Adam (a.s), kuma a kan haka ne za a kiyasta sauran siffofin khabariyya.
Da kuma siffofin Allah da suke siffanta shi da kamala kamar sani, da iko da sauransu, tare da masu kore masa tawaya kamar masu kore masa jahilci da gajiyawa, wadannan siffofin su kuma an yi sabani kan yadda suke. Sai Ash'arawa suka tafi a kan cewa su wadannan siffofin daban, samuwar zatin Allah daban, wannan lamarin yana nuna cewa su kari ne ga zatin Allah, kuma da samuwarsu ne yake siffantuwa da su, kuma da za a yaye hijabi garemu da mun gan su.
Idan muka yarda da wannan tunani na Ash'arawa zamu kai ga kididdiga ubangiji, domin idan iko, da ilimi, da nufi, da sauransu suka kasance suna da samuwa daban bayan samuwar Allah, kuma Allah yana bukatuwa zuwa garesu domin siffantuwa da su, to mun halaka, mun sanya wa Allah ababan tarayya.
Amma idan muka ce su wadannan siffofin ainihin zatin ubangiji ne su, ba su da wata samuwa ta daban sai samuwar Allah madaukaki. Kamar dai mu ce akwai Annabi (s.a.w) wanda yake da siffofi kamar hakuri, ilimi, takawa, baiwa, kyauta, gaskiya, amana, idan muka duba zamu ga wadannan siffofin su ne ainihin zatisa, kuma sun bubbugo daga samuwarsa ne. Sai ya kasance shi kadai ne, babu wadannan siffofin a samuwa mai zaman kanta, domin samuwarsu duk ta dogara da samuwarsa ne.
Amma sabanin hakan da mun dauki maganar ash'arawa, da maganarsu ce, to da sai ya kasance ke nan wadannan siffofi suna da samuwarsu ta daban, kamar sai mu ga hakuri, da ilimi, da iko, da gaskiya, da amana da samuwarsu ta daban wacce ba siffa ce kawai ta wannan samamme Manzo mai daraja ba, da kuwa maganarsu ta kasance, da an samu yawan ubangizai.
Sakamakon wannan ne zamu ga Imam Ali (a.s) ya ci gaba da bayani kan wannan lamari mai muhimmanci na gyaran tauhidi da sanin Allah ga mutane yana mai cewa:"don haka duk wanda ya siffanta Allah to ya gwama Shi" ai wanda ya siffanta shi da siffofin da ya bayar da labarinsu bisa tawili da dogaro da yaren larabawa, kamar ya jingina masa ido, ko jiki, koda kuwa ya ce ba irin namu ba ne kamar yadda wasu daga ash'arawa suka yi don su kauce wa kamanta shi da bayi, to hakika ya gwama shi wato ya hada shi da waninsa, ya yi shirka da shi a siffofinsa, ya kamanta shi da waninsa.
Shi kuwa wanda ya gwama Allah Imam (a.s) yana cewa da shi: "wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi" domin duk wanda ya hada shi da waninsa tabbas ya sanya shi biyu. "wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya shi sassa-sassa" domin duk wanda ya sanya shi biyu kuwa to dole ne tsakanin wadannan biyun a samu wani abu da ya bambanta su da wani abu da ya hada su, sakamakon samun hauhawa a halittarsu su biyu, sai a samu kowanne yana da wani yanki da sashen da dayan ba shi da shi.
Wannan yankin da sashen kuwa yana iya kasancewa na dabi'a ne kamar halittar jiki ta zahiri, ko kuma na kaddarawa ne kamar wasu zarurruka biyu wadanda suke daurantar juna da suka mike babu karshe a tare da su, ko kuma yanki ne da sassa na hankali, kamar bangarori da kusurwowin jikin mantik (logical body) wanda yake a cikin tunanin dan Adam, to dukkan wadanna sassa da gabobi, da bangarori Allah ya barranta da su, kuma ba ya siffantuwa da daya daga cikinsu.
Wanda kuwa ya sanya ubangiji sassa to bai san Allah ba, domin ubangiji ba shi da gabobi da yanki-yanki, don haka ne zamu ga Imam (a.s) yana cewa: "wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi" kamar yadda a farko muka yi nuni da cewa duk sa'adda aka iyakance ubangiji madaukaki to an kirga shi, domin an sanya masa abokin tarayya, saboda daya bangaren zai fara ne inda madaukaki ya tuke.
Sannan sai nuni da cewa Ubangiji ba jiki ba ne, balle ya shiga cikin wani abu, ko ya kasance wajen wani abu, ko kuma ya cakuda da wani abu, ko ya ki cakuda da wani abu, ko kuma motsi ya same shi, sai ya siffantu da zamani da lokaci, ko kuma wani abu ya tattaro shi sai ya siffantu da kasancewa kan wani wuri, ko kasansa, ko a gefensa. Don haka ne Imam Ali (a.s) yake cewa: "wanda ya ce; a cikin me yake? to ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce; a kan me yake? to ya sanya shi ba ya wani wurin (alhalin shi yana ko'ina bai kebanta da wani wuri ba)".
Sannan sai ya siffanta Allah madaukaki da wasu daga siffofin kamala yana mai nuni da rasin farko da karshe ga hakikanin samuwa wato ubangiji madaukaki. Ubangiji samamme ne ba tare da farko ba, domin shi ne ainihin samuwa, da rashi ya riga shi da ba a samu komai ba, da ba a samu wani samamme ba, domin rashi ba ya iya samar da wani abu, shi kansa ba komai ba ne balle ya samar da wani abu. Da wannan ne aka yi nuni a cikin fadinsa: "Kasantacce ne ba tare da faruwa ba, samamme ne ba daga rashi ba".
Sannan tun da Allah madaukaki ba shi da iyaka wannan yana nufin yana tare da komai ke nan, domin duk inda samuwa ta sanya kafarta to Allah yana nan. Wasu hadisi da Arifai suka ruwaito shi da Sunna yana cewa: "Da za a zuro guga daga sama zuwa kasa ta bakwai da ta fada kan Allah" (Ainul Yakin: 305), don haka duk inda kuka juya to nan fuskar Allah ce.
Don haka Allah madaukaki yana tare da komai da kowa, sai dai kasancewarsa tare da su ba ya sanya haduwarsa da su domin shi ba jiki ba ne. "yana tare da komai ba tare da sun hadu ba". sai dai kuma wannan ba ya nufin wadanda ba su fahimci wadannan kalamai masu zurfi ba su yi wasa da su, don haka idan ba su gane ba sai su ajiye shi inda suka gan shi.
Sannan kasancewarsa ba shi da iyaka yana nuna mana cewa ba shi ne sauran halittu ba, domin akwai tsananin tazara da bambaci maras iyaka tsakanin mai iyaka da maras iyaka. Sai dai kasancewarsa ya bambanta da su ba ya sanya shi ya kasance ba su ba, don haka ne Imam (a.s) ya ce: "kuma shi ba shi ne sauran samammu ba, ba tare da sun bambanta ba".
Sannan kamar yadda siffofinsa suka bambanta da na bayi da nisa maras iyaka, haka ma ayyukansa suka bambanta matuka da na bayinsa, musamman bayinsa masu jiki, ma'abota jiki kamar mutane da sauran halittun kasa suna motsi domin aikata wani aiki, kuma suna amfani da kayan aiki kamar fatanya, ko alkalami, domin ayyukansu sabaninsa madaukaki, don haka ne Imam (a.s) ya yi nuni da cewa Ubangiji "mai aiki ne amma ba da motsi ko amfani da kayan aiki ba".
Ubangiji madaukaki ba jiki gareshi balle ya kasance yana da sauran siffofin da suke bujurowa masu jiki, don haka babu wata siffa ta masu jiki da yake siffantuwa da ita a tasiri ko a tasirantuwa, don haka ne ba ya iya kasancewa abin gani ga wata halitta, amma shi yana riskar dukkan halittarsa. "shi mai gani ne yayin da babu wani mai ganinsa daga halittarsa".
Amma fadinsa (a.s) cewa: ""makadaici ne yayin da babu wani wanda yake samun nutsuwar (debe kewa) da shi, ba ya kuma samun dimautuwa da fita daga hayyaci saboda rashinsa", nuni zuwa ga cewa dukkan wanda yake shi kadai yakan samu damuwa a cikin kadaitarsa, wannan ne yakan kai shi ga samun dimautuwa cikin kadaicinsa, don haka ne yake neman wanda zai debe masa kewa. Amma mahalicci mai daukaka sabanin haka ne, yawa da karaci duk ba su da bambanci a tare da shi, ya kasance ba tare da wani abu ba, kuma zai kasance a haka har abada yana shi kadai.
Sanin Allah Madaukaki
Sanin Allah madaukaki shi ne muhimmin hadafin halitta na farko kamar yadda ruwayoyi masu yawa suka yi nuni da shi, don haka ne Imam (a.s) wanda yake shi ne malamin kowa bayan manzon rahama (s.a.w) ya ci gaba da wannan huduba yana mai nuni da hanyoyin sanin Allah (s.w.t).
Sai ya fara da hanya ta farko mai nuni da samuwar Allah saboda samuwar halittar duniya da sauran halittu, wannan dalili ne da yake nuna mana cewa dukkan wani abin halitta da aka samar to akwai wanda ya samar da shi, domin ba zai ba wa kansa samuwa ba tun da rashi ba samuwa ba ne balle ya samar da kansa ko waninsa. Imam (a.s) ya yi nuni da wannan yana mai cewa: ya samar da komai mai cewa: "Allah Madaukaki ya kago halittarsa da kagowarsa, ya fare ta fararwa", yana mai nuni da cewa ita wannan samuwar akwai wanda ya yi ta.
Sannan domin kada wani ya yi tunanin cewa samarwar Allah tana kama da irin samarwar bayi ga abubuwan da suka kagowa na da kere-kere ne sai ya yi nuni da cewa lamarin sabanin haka ne. Domin bayi idan suna son yin wani abu sukan yi tunani a farko sai su suranta shi a tunaninsu, sannan sai su ba shi fasaloli a cikin hankalinsu, sai kuma su aiwatar da shi a zahiri. Kamar dai magini da yake tunanin gina gida sai ya suranta shi ya kuma zana shi a hankalinsa, sannan sai ya zana shi da biro kuma ya aiwatar da gina shi a zahiri.
Amma Allah madaukaki aikinsa ba haka yake ba, ba ya tuna abu domin ba ya gafala faufau, ba ya suranta shi a kwakwalwa domin shi ba ya jahiltar abu kafin samuwarsa, saninsa da abu kafin da bayan samuwarsa duk ba shi da bambanci. Abu yana faruwa ne da zarar ya yi nufinsa, don haka ne yake cewa: "… idan ya yi nufin wani abu sai ya ce da shi kasance, sai ya kasance"[1].
Da wannan ne fadinsa (a.s) yake nuni cewa: "ba tare da wani tunani ba da ya kokkoma masa, ko wani gwaji da ya amfana daga gareshi, ko wani motsi da ya farar[2], ko wani tunanin rai da ya kai-kawo a cikita. Sai ya kore masa tunani da kaikawo wato suranta abu a tunani, kuma ya kore masa gwaji da kiyastawa, ya kora masa saken zuci da taraddudin kan yaya zai yi wani aiki da ya yi nufi, ya kore masa dukkan zato da shakku kan yadda ya kamata a farar da wani abu, sannan ya kore masa duk wani nau'i na jahilci.
Don haka ne babu wani abu da ya yi nufi bai kasance ba, domin babu wani karfi da ya isa ya sha gaban abin da ya yi nufi. Sai dai nufinsa iri biyu ne, nufinsa a halittawa wannan shi ne ake nufi a nan, wato idan Allah ya so wani abu ya faru kamar ya so arziki ga wani, ko ya so masa lafiya, to babu wanda ya isa ya hana shi arziki ko ya kwace masa lafiya.
Amma idan so na shari'a ne, wannan ana ce masa umarni, Allah ya yi umarni ga bayi da su yi imani da shi, su yi salla, su yi zakka, idan ba su yi ba to wannan yana kansu, domin Allah ya ba su zabi kuma bai tilasta su ba. Don haka ne Allah yakan yi musu nufin wani abu ya so musu shi, amma sai ya ki faruwa saboda an sanya sharadin faruwarsa da zabinsu babu tilasci, don haka ne ya so wa shedan ya yi sujada amma ya ki.
Amma fadinsa cewa: "Ya jingina al’amura bisa lokacinta, ya kuma daidaita tsarin tsakanin masu sabawarta, sannan ya sanya wa kowace halitta dabi’ar da ta dace ita, ya lizimta mata makamancinta[3]". Nuni ne zuwa ga cewa mahalicci ya san komai da gwargwadon bukatun tsarin da zai tafiyar da halitta bisa tsari kamar yadda ya dace, don haka ne tun da ya kasance mafi sanin komai, sai tsarinsa ya kasance mafificin tsari kan komai, ta yadda da za a zo da wani tsari da ya kasance bai dace ba.
Duba misalin tsarin halittar mutum, ina ne za a sanya wata gaba inda ya fi dacewa fiye da inda mahalicci mai hikima ya sanya ta. Misali idan aka sanya hannu a wurin kafa, kafa kuma a wurin hannu, ko a canja wuraren da idanuwa suke da inda kunnuwa suke, ko kuma canja wurin da baki yake da cibiya, ko a dawo da hanci a kirji ko wurin baki, duk sai mu ga tsari ya watse ya tarwatse.
Allah yana da taskar komai a hannunsa, kuma wannan taskar ba ta karewa, sannan ba a gudun gubucewa domin kowa yana da rabosa. Wallahi da dan Adam ya fahimci haka da bai yawaita bakin ciki ba, amma rashin sanin hakan sai ya sanya shi yana mai tsananin tsoron gobensa. Sai dai wannan taskar yana sauko da ita daidai gwargwado, wani lokaci domin an roke shi, wani lokaci domin mahallin falala da baiwar kyautarsa ya dace sai ya ba shi, wani lokaci kuwa domin ya jarrabi wasu sai ya ba su, kuma kowanne ya jingina shi bisa lokacinsa.
Sannan ya daidaita tsarin da yake tsakanin wadannan samammu, domin hikimar Allah shi ne ya halitta su mabambanta sannan sai ya daidaita “tsakanin masu sabawarta, sannan ya sanya wa kowace halitta dabi’ar da ta dace ita, ya lizimta mata makamancinta[4]". “Yana mai sane da ita kafin ya fare ta, yana mai kewaye da sanin iyakokinta da karshenta, ya san hakikaninta da sasanninta. Sannan sai Ubangiji ya keta sasannin sarari, ya tsaga nahiyoyi, da magudanar iska, ya kuma gudanar da ruwa da tunkudarsa mai ambaliya ce, daduwarsa (karuwarsa) da mikuwarsa (da kwaranyarsa) masu hauhawa ne, Ya dora shi a kan iska mai karfi, mai girgiza kowane abu tana tunbukewa, ya umarce ta da dawo da shi, ya dora ta akan tsananinsa, (wato; ya sallada iska akan igiyoyin ruwa) ya gwama ta zuwa iyakarsa (domin haka ne iska take juya shi yadda ta so), iska ce da ya sanya ta daga karkashinta mai rarrabawa da fatattakawa, ruwa yana daga sama mai tunkudar juna[5]. Sa’annan Ubangiji (s.w.t) ya tayar da wata iska mayofinciya[6], ya lizimta mata matabbatarta, ya tsananta magudanarta, ya nisantar da mafararta, ya umarce ta da sirka ruwa, da tayar da ambaliyar kogi (teku), sai ta kada shi kadawa mai tsanani irin kadawar gajimare, ta yi watanda da shi a sararin samaniya, tana mayar da na farkonsa zuwa karshensa, tana mayar da na karshe farko, tana kuma hada kan mai zuwa da mai dawowa (mai kaiwa da mai komowa) har ya makala malalarsa, ambaliyarsa kuma ta fitar da kumfa[7], ya daukaka shi a cikin iska mai daidaitawa, da sarari mai yalwa, sai ya daidaita sammai bakwai daga gareshi, ya sanya kasansu ambaliyya maras kaikawo da kwarara, samansu kuma rufi abin kiyayewa, rufinta madaukaki ne, ba tare da amudi (dirka) da yake rike ta ba, babu wata kusa da take tsarata. Sannan ya kawata ta da adon taurari, da haske mai hudowa, ya gudanar da fitila mai haskakawa a cikinta, da wata mai haske: a falaki mai kewayo, da rufi mai wanzuwa, da falakin rakimi mai juyawa”. Allah ya girmama mafi kyautata halitta.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Wednesday, June 16, 2010
[1] Yasin: 82.
[2] - Domin Allah ba jiki ba ne balle ya yi motsi.
[3] - Mutum yana neman mutum dan’uwansa, zaki da zaki kamar yadda kowannensu ya san abincinsa da makwancinsa da yadda kuma zai yi tarbiyyar zuriyarsa da makamancin haka.
[4] - Mutum yana neman mutum dan’uwansa, zaki da zaki kamar yadda kowannensu ya san abincinsa da makwancinsa da yadda kuma zai yi tarbiyyar zuriyarsa da makamancin haka.
[5] - Karkashin kadawar iska mai karfin gaske, wato ya bai wa iska ikon kada ruwa yadda take so, ta kuma mayar da shi zuwa fuskar da yake so, Sannan ya sanya iska a matsayin mai kula da ruwan ta yadda yakan sanya masa iyakoki, ya sanya sarari a karkashin iska ya kuma sanya ruwa yana motsi a samansa.
[6] - Mai kanjamawarwa da busarwa, ba ta barbara ga ‘ya’yan itace, ko tsakanin gajemare da giragizai.
[7] - Wato ya sanya ruwa yana ambaliya sannan igoyoyin ruwa suna gamuwa da junansu, iska mai karfi takan auku ta yadda yakan fara daga wani wuri mai nisa, sannan ya sanya ruwa ya tafiyar da igiyoyin kogina zuwa bangarori daba-daban, kuma kamar yadda iska yake da karfi a cikin sarari haka yake kaiwa kogi hari ta yadda yake kwasar farkon kogi ya aika shi zuwa karshensa, sanna ya sanya ruwan da yake zaune a wuri guda zuwa mai motsi sama da kasa, ta yadda yakan hada ruwa da junansa, ya haifar da tudu kamar tsaunuka.