Halayen Imam Ali (a.s) a Nahajul-balaga

Ya zo a cikin littafin Nahajul-balaga cewa; Imam Ali (a.s) ya ce: Da sannu wani zamani zai zo wa mutane da ba a kusantarwa a cikinsa sai annamimi, kuma ba a kayatarwa sai fajiri, kuma ba a raunatarwa sai mai adalci, suna ganin sadaka a matsayin abin biyan bashi, kuma sadar da zumunci a matsayin gori, kuma ibada domin neman fifiko a kan mutane! A lokacin ne sarauta (tafiyar da mulki) zata kasance da shawarar kwarkwarori, da jagorancin yara, da kuma tsarawar fidiyayyun mutane! A nan zamu so mu yi nuni da wasu dabi'u kyawawa da Imam Ali (a.s) ya gudanar da su a tarihin rayuwarsa mai daraja da albarka da adalcin da ya yi a jagorancinsa.

Imam Ali ya karbi jagorancin al置mma bayan kashe Usman dan Affan a wani tawaye da al置mmar musulmi suka yi masa suna kafirta shi, wannan lamarin bai yi wa munafukai dadi ba, don haka sai suka ga ya kamata su dora abin a wuyan Imam Ali (a.s) domin su samu jin dadin yakarsa da kashe shi da dukkan wani salihi, da kuma zuriyar manzon Allah (s.a.w) wanda shi ne babban makiyinsu.

Imam Ali (a.s) ya samu kansa a cikin wani yanayi maras dadi na rayuwar al置mma da tattalin arzikinsu na rayuwa, da dukkan abubuwan da ya kamata su mora, domin ya tarar da dukkan dukiyoyin musulmi wanda ya rigaye shi ya bayar da ita ga wasu tsurarun mutane da yawancinsu Banu Umayya ne da 惣an korensu wadanda suka shahara da gaba da manzon Allah (s.a.w).

Kuma wanda ya rigaye shi ya kebanci arzikin kasa ya bayar das hi ga wanda manzon Allah (s.a.w) ya tsine musu ya yi umarni da kashe su duk inda suke, sai ga shi sun kasance dukiyar al置mma gaba daya ta koma hannunsu. Suna fasin da dukiyar Allah kamar dai yadda Imam Ali (a.s) ya siffanta a cikin hudubarsa ta Shakshakiyya a littafin Nahajul-balaga.

Sai ya daidaita dukiya da kyauta tsakanin mutane, ya daidaita su kamar yadda yake a lokacin manzon Allah (s.a.w) wanda wannan lamari ne da an dade da mantawa das hi tun lokacin manzon Allah (s.a.w). Imam Ali (a.s) yana cewa: Kuraishawa sun tsorata ni ina karami, sun dasa mini gaba ina babba.

Kuma rashin jin dadin canje-canjen da yake yi shi ne ya sanya aka kafa masa gaba mai tsanani kamar yadda yake a tarihi musamman wasu da ake gani a matsayin manya kamar Dalha da Zubair da A段sha, sannan kuma ga munafukai a Sham su kuma da tasu gabar ta kin musulunci.

Imam Ali (a.s) ya yaki kuraishawa suna kafirai, kuma ya yake su suna munafukai, kamar yadda ma'aikin Allah (s.a.w) ya yi masa alkawarin hakan.

Game da tafiyar da dukiya kuwa ya yi wa musulmi jagoranci ne irin na lokacin manzon Allah (s.a.w), ya kasance yana cewa: "Da dukiyar nan tawa ce da na daidaita tsakaninsu, yaya kuwa, alhalin wannan dukiya ta Allah ce, kuma bayar da dukiya ba bisa hakkinsa ba barna ne, kuma yana daukaka mai yin haka a duniya, kuma ya kaskantar da shi a lahira, ya girmama shi gun mutane, ya kaskantar da shi gun Allah. Don haka ne ya yi kokarin samar da al'ummar da masu hannu da shuni ba su mamaye arzikin kasa ba, kuma ba a samu danniyar gurguzu ba.

A kasashenmu an samu wannan lamari ya yi kamari matuka da gaske, mai daraja shi ne wanda ya fi kowa satar kudin al'umma da danne hakkinsu yana raba wa sauran ashararan da suke jagorancin mutane tare, ana kashe mu raba da dukiyar al'umma, da wannan ne sai matsayinsa ya karu gun masu jin dadin kasa, girmansa ya karu gun masu danne hakkokin al'umma, amma wurin Allah kaskancin wulakantuwa a wuta yana jiran sa!.

Amma a siyasar Imam Ali (a.s) ta karbar haraji muna ganin yadda yake gaya wa Malik Ashtar kan cewa: "Dubanka wurin gyaran kasa ya fi yawa kan dubanka kan karbar haraji, domin ba a samun wannan sai da gyara kasa, kuma duk wanda ya nemi haraji ba tare da gyaran kasa ba to ya rusa kasa, kuma ya halaka bayi, kuma lamarinsa ba zai wanzu ba sai kadan".

Sai ya yi nuni da cewa karbar haraji ba tare da gyara kasa ba yana daga cikin abin da yake rusa kasa gaba daya. Wannan lamarin ya sanya masu kin gaskiya kyaram wannan hukumar adalci ta Imam Ali (a.s), suka yi kokarin ganin gaba da ita ta kowane hali.

Game da lamarin tafiyar da lamurran al'umma kuwa Imam Ali (a.s) ya yi siyasar daidaito tsakanin kowane mutum ba tare da nuna bambancin matsayi ko kabila ko waninsu ba, ya daidaita mutanen ta fuskancin:

1.  Hakkokin wajibi

2.  Kyauta da baiwa

3.  Dokokin kasa

Sannan ya tilasta gwamnonisa yin hakan a tsakanin al'ummarsa, yana mai duba lamurransu domin kada su kauce wa hanya.

Sannan Imam Ali (a.s) bai taba tilasta mutane kan wani abu ba, yana ganin mutane suna da 'yancinsu hatta da a zabensa da yi masa bai'a, kuma ya sha fada wa masu gaba da shi cewa su sani fa cewa yi masa bai'a ba bisa tilas ko kuskure ba ne, sabanin bai'a wasu halifofin.

Don haka ne zamu ga hatta da abokan hamayya Imam Ali (a.s) bai taba hana su nasu 'yancin fadin ra'ayinsu ba, ya sakarwa kowanne 'yancin fadin albarkacin bakinsa, hatta da hawarijawa ya ba su 'yancin komai har na neman ilimi da aminci bai dauki mataki kansu ba duk da abin da suka yi har sai da suka far wa al'ummar musulmi da kisa sannan sai ya dauki mataki kansu domin magnain barnarsu a cikin al'umma, da kariya ga al'umma daga sharrinsu domin sanya aminci cikin al'umma.

Ba a samu wani mutm da ya kai kiran mutane zuwa ga hadin kai ba tun bayan manzon Allah (s.a.w) ba kamar Imam Ali (a.s), ya yi matukar kokarin ganin ya samu dinke barakar al'ummar musulmi sai dai munafukai sun yi kokarin ganin rarraba ta matukar gaske, hatta da munafukai irin su AbuSufyan da suka nemi taimaka masa da makamai da dawakai domin ya karbi hakkinsa na jagoranci daga hannun Abubakar sai ya ki yarda domin gudun kada al'umma ta fada cikin yaki, sannan kuma ya gane cewa hadafin munafukai shi ne tarwatsa musulunci. Don haka ne ya ce masa: Bari wannan lamarin, ka dade kana neman sharri ga musulunci.

Imam Ali (a.s) ya sanya himma matukar wurin yakar fatara da talauci daga cikin al置mma, ya zo cewa ya aika da wani gwamna Afrika, bayan wani lokaci sai ya aiko masa da wasika yana cewa dukiya ta yi yawa gunmu, me zamu yi da ita? Sai Imam Ali (a.s) ya ce masa ka ba wa talakawa ita domin su wadata, sai ya sake aiko da wata wasika wani lokaci zuwa ga Imam (a.s) cewa talakawa sun wadatu kuma har yanzu akwai dukiya mai yawa me zamu yi da ita? Sai Imam Ali (a.s) ya aiko masa da cewa ka aurar da gwagwarensu da wannan dukiya, sai ya aurar da gwagwarensu, sannan sai ya aika da ragowar dukiya zuwa ga Imam (a.s).

Dukkan wannan yana iya sanya dukkan dan Afrika mai 'yanci yin tunani da zarar ya tsinkayi mazhabar Ahlul Baiti ya san abin da yake cikinsa sai mu ga ya karbe shi, kuma ya yi riko da shi ba tare da wani kokwanto ba, domin yana ganin arzutar duniya da lahira a cikinsa fiye da yadda yake gani a waninsa. Don haka ne ma a wannan gomomin karshe na rayuwar jama'ar Afrika zamu ga miliyoyin jama'ar Afrika sun rungumi mazhabar Shi'a domin sun sami kofar birnin ilimi a cikinsa a wannan mazhaba, da kuma rayuwa mai sauki, musamman ga wanda ya samu dacewar bin sa bisa hukunce-hukuncensa, domin kuwa mun karanta yadda halin yalwa da rayuwa mai dadi ya kasance a hukumar shugaban masu kadaita Allah Imam Ali (a.s).

Haka ne yayin da tunanin Ali da aikin Ali ya yi hukunci da koyarwar Ali to al'umma zata rayu rayuwa mai dadi, domin aikinsa aikin Allah ne da ilimin da Allah ya ba shi, kuma shi Imam Ali shi ne tafarki madaidaici, kuma hujjar Allah a kan mutane gaba daya.

Mu sani Ali (a.s) rahamar Allah ce kan talikai wacce wannan rahamar ta gangaro daga manzon Allah (s.a.w) wanda ubangiji madaukaki yake cewa game das hi: "Ba mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai" (Anbiya: 107), sai wannan rahamar ta biyo ta hannunsa. Rahamar Allah ita ce abu na farko da ya bayyana ga bayinsa bayan bayyanar sunansa Allahu, don haka ne ma rahamarsa ta yalwaci kowane abu. Rahamar Allah a nan ta mamaye dukkan janibin halitta a samuwarta, da kuma tsarin rayuwarta da aka fi sani da Shari'a.

Manzon Allah (s.a.w) rahama ne a Shari'a da ma'anarta mai fadi da ta shafi siyasa, tattalin arziki, zaman tare, tsaron al'umma, yalwar al'umma[1], rayuwar auratayya, hakkokin yara da na mata, da raunanan mutane, hukunce-hukuncen ibadoji da mu'amaloli, kawar da talauci da fatara daga cikin al'umma, ilmantar da al'umma gaba daya ta yadda ba za a samu jahili ko da daya ba, samar da mazauni da matsuguni ga kowane mutum. Rahama ce ga dukkan talikai da tsarin da zai samar da adalci a cikin al'ummu duk duniya baki daya, da ta yalwaci kowane abu, balle kuma dan Adam mai kima da daraja. Don haka ne yayin da duniya ta kasance cikin duhu sai garinta ya waye da wanda Isa dan Maryam (a.s) ya yi wasiyya da zuwansa Muhammad (s.a.w).

Rahamar ba ta tafi ba don wafatinsa, domin rahama ce mai fadi da ta yalwaci kowane abu har alkiyama ta tashi, don haka ne ma ya zaba mata mahalli har goma sha biyu da zasu kasance bayyanar rahamar bayan wucewarsa. Ita siffa ce mafificiya ga Manzon Allah, Suna ne da Allah ya tsaga shi daga gareshi ya yafa masa shi, don haka ne ya zamanto rahama ga dukkan talikai da rahmaniyyarsa, rahama ga muminai da rahimiyyarsa da ta tsattsago daga rahamaniyyarsa.

Sai ya kasance yana da fifikon da babu wani mahaluki da ya taka shi, wannan matakin shi ne matakin "Hamd" wanda alaminsa shi ne "Tutar Hamd", sai ya sanya mai rikon wannan tutar shi ne wasiyyinsa Ali (a.s), yana cewa da shi: "Kai ne mai rikon tutata duniya da lahira". (Kanzul Ummal na Muttaki Hindi, Bahanife: J 13, Hadisi: 36476). Sai Manzon Allah ya taka matsayin "Hamd", Alinsa kuwa yana kan "Tutar Hamd", don ya yi nuni da cewa ga kofarsa nan da duk wani da ya wuce ba ta nan ba, to ba zai iso gunsa ba.

Kasancewarsa rahamar Allah ga bayi, kuma wanda ya taka mataki mafi girma na "Hamd=Godiya", don ya kasance mai yawan godiya ga Ubangijinsa, ibadarsa ba don tsoron wuta ko kwadayin aljanna ba, wannan ita ce ibadar bayi da masu kwadayi, amma ibadarsa ta kasance don godiya ce ga Allah. Sai ga tsokar jikinsa Zahara (a.s) take nanata cewa da Ubangiji ya azabtar da ita a wutarsa, da ta riki tauhidinta a hannu.

Imam Ali (a.s) kuwa wanda yake rike masa "Liwa'ul Hamd = Tutar Godiya" yana munajati da Allah yana cewa: Kuma wallahi! da ka sanya ni a cikin azaba tare da makiyanka, ka hada ni a wuta a tsakanin wadanda bala'inka ya fada wa, na rantse da girmanka ya madogarata jagorana, ina mai rantsuwa mai gaskatawa, matukar ka bar ni ina magana, to zan daga murya zuwa gareka tsakaninsu -'yan wuta- da muryar masu buri, kuma wallahi sai na kira ka ina kake ya masoyin muminai, ya matukar burin masana, ya mai taimakon masu neman taimako, ya masoyin zukatan masu gaskiya, ya Ubangijin talikai! (Muhasabutun Nafs: Kaf'ami; S: 187).

Sai manzon rahama (s.a.w) ya gadar da wannan rahamar ga wasiyyai, da wannan ne sayyidi Ali (a.s) yake cewa: "Ni bawa ne daga bayin Muhammad" (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449). Sai wadancan haskaka goma sha biyu da 'yarsa Zahara (a.s) suka kasance feshi daga rahamar Allah ta hannun Muhammad (s.a.w) bawansa, Rininsu da saninsu na Allah ne. (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449).

迭inin Allah waye ya fi Allah iya rini, kuma mu masu bauta ne gareshi (Bakara: 138). Sai Allah ya runa su da shiriyarsa da rahamarsa, sai suka runa mu da shiriyar da Allah ya yi musu, don haka ne Muhammad (s.a.w) ya kasance rahamar Allah ga talikai baki daya, a bayansa kuma Littafin Allah da Alayensa (a.s).

Sai aka wajabta salati gareshi tare da wadannan Alayen nasa goma sha uku, sai aka yi masa ni段momi da babu wanda ya same su. Mataki ne na 滴amd, da wajabcin yi masa salati. Da wasu ni段momi kuma da babu mai samun su sai ya roka kamar yadda aka yalwata masa kirjinsa, aka sanya masa Ali dan置wansa wasiyyinsa mai karfafarsa.

Babu wani addini da ya zo da rahama ga al置mma fiye da wannan addini na karshe, domin wanda aka aiko da shi yana dauke da rahamar Allah (s.w.t) tare da shi. Don haka ne ma ... Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai... (Anbiya: 107). Da wannan ne zamu ga addinin nan madaukaki na musulunci ya zo da lamunin rayuwar dukkan dan Adam wacce ba ta kebanta da musulmi ba. Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da daukar nauyin al'amuran al'umma da zamu kawo wasu kamar hakan:

Daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ni ne na fi cancanta da kowane mumini fiye da kansa kuma Ali (a.s) shi ne ya fi cancanta da shi bayana". Sai aka ce da shi Imam Ja'afar Sadik me wannan yake nufi? Sai ya ce: Fadin Annabi (s.a.w) wanda ya bar bashi ko kaya to suna kaina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce"(Tafsiri Nurus sakalain: mujalladi 4, shafi: 240).

A wata ruwaya ta Ali bn Ibrahim ya kawo a tafsirinsa daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Babu wani wanda yake bin bashi da zai tafi da wanda yake bi bashi wajen wani jagora na musulmi kuma ta bayyana ga wannan shugaban cewa ba shi da shi, to sai shi wannan talakan marashi ya kubuta daga bashinsa kuma bashinsa ya koma kan jagoran musulmi da zai biya daga abin da yake hannunsa na dukiyar musulmi"[2].

Bayan Imam Sadik ya fadi wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: "Babu wani dalili da ya sanya mafi yawan yahudawa musulunta sai bayan wannan magana ta Annabi (s.a.w), kuma sun yi imani da su da iyalansu"[3].

A wata ruwayar Sheikh Mufid ya karbo daga majalisinsa da sanadin da muka ambata daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya hau kan mimbari sai fuskarsa ta canja kuma launi ya juya sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: "Ya ku jama'ar musulmi! Ni an aiko ni ne kusa da alkiyama -har inda yake cewa- ya ku mutane wanda ya bar dukiya to ta iyalinsa ce da magadansa, amma wanda ya bar wani nauyi ko rashi to yana kaina a zo gareni"[4].

Haka nan ya karbo daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Wanda yake da wata dukiya kan wani mutum da ya karba kuma bai ciyar da ita a barna ko sabo ba sai ya kasa biya, to wanda yake binsa dole ne ya jira shi har sai Allah ya arzuta shi sai ya biya shi, idan kuwa akwai jagora mai adalci to yana kansa ne ya biya masa bashinsa, saboda fadin Manzon Allah (s.a.w) cewa: "Duk wanda ya bar dukiya to ta magadansa ce, kuma wanda ya bar bashi ko wani rashi to yana kaina ku zo gareni, don haka duk abin da yake kan Annabi (s.a.w), yana kan jagora. (Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 492).

Da wdannan dokokin da ire-irensu masu yawa musulunci ya sanya talauci ya kawu daga dukkan daular da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya a wancan zamanin. Talauci ya kawu ta yadda kusan idan ka ga mai roko to zai kasance abin mamaki, musulunci ba ya son zama cikin kaskancin rokon mutane, don haka ne ya kawar da talauci, ya sanya dokokin lamunin rayuwar al置mma. Duba mamakin da Imam Ali ya yi yayin da ya ga wani yana bara a kwararon birinin Kufa.

Hurrul Amuli kuwa ya ambaci cewa: Imam Ali (a.s) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rokon mutane, sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wadanda suke tare da shi suna tambayarsa Mene ne haka? Sai ya ce: Ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara. Sai Imam Ali (a.s) ya yi fushi ya ce: Kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu na albashi daga Baitul-mali da zai rika rayuwa da shi (Wasa'ilus Shi'a).

Wanan kissa tana nuna cewa; Talauci ya kawu gaba daya har sai da ya kasance ba shi da wani mahalli a daular musulunci. Hatta Imam Ali (a.s) da ya ga talaka guda daya mai bara kuma ba ma musulmi ba sai da ya yi mamakinsa, ya gan shi wani abu bare da bai dace da al'ummar musulmi ba. Sannan ya yi umarni da a sanya masa albashi da zai rayu da shi tare da cewa shi kirista ne da ba ya riko da musulunci, domin kada a samu talaka a kasar musulmi ko da kuwa mutum daya ne. Kuma domin duniya ta san abin da musulmi suke a kai na yaki da talauci: da cewa kuma hukumar musulunci ita ce take yaki da talauci ta kuma daukaka matsayin talakawa ba kawai musulmi ba, har da wasunsu matukar suna karkashin daular.

Haka nan musulunci ya dauki dan Adam da kima matuka ko da kuwa bai musulunta ba, sai dai duk wanda ya taba musulmi ya kashe su to shi kadai ne musulunci ya yarda musulmi su taba, don haka ne zamu ga a rayuwar Manzon Allah (s.a.w) bai taba kai hari kan mutanen da ba su suka fara kai masa hari ba. Kuma idan mutanen wani gari suka kai masa hari to bai taba yakar wasunsu na wani garin daban ba ko da kuwa addininsu daya ne, sai dai ya rama kan wadannan dai da suka kai masa hari kawai.

Duk da a rayuwar musulunci an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame. Don haka ne ma adadin wadanda ake kashe wa bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu. Wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba. (Littafin Tafarkin Rabauta: Fasalin; Aiko Annabi Mai Daraja (s.a.w).

Musulunci bai taba yarda da zaluntar wani mutum ko wani mai rai ba, kai hatta da barnar abinci da lalata wuri da lalata kasa ya hana balle azabtar da dan Adam ko kashe shi, ya kuma sanya kalma mai dadi da zaka gaya wa dan'uwanka mutum ya yi farin ciki a matsayin sadaka. Don haka ne ya soki mai lalata kayan gona da dabbobi, ya kira shi mai yada fasadi da barna, balle kuma mai isar da cutarwa ga mutum. Saboda haka ne ma muka samu dukkan matsalolin da muke ciki a yau musamman a kasashenmu sun taso daga rashin fahimtar musulunci ne, sai dan Adam ya kasance ba shi da wata kima.

Mun rasa ilimi ta yadda yawancin mutanenmu suna rayuwa a matsayin masu karancin ilimi ko ma ba su da shi saboda kawai yarenmu ba a yarda ya zama yaren ilimi ba, sai wannan karancin ilimin da rashin lamunin rayuwar suka haifar mana da rashin ganin kimar dan Adam. Muna iya ganin yadda aka kashe mutane babu imani, ko tausayi, ko hankali, kamar yadda Aljazira ta nuna a rikicin da ya faru a Maiduguri, ta yadda aka kashe mutanen da su ba 添an boko haram ba ne, (kai ko da ma su ne ya kamata a kai su kotu domin doka ta zartar musu da hukuncin da ya dace ne). Har ma mai harbin ana gaya masa kada ya lalata bulet, kuma ya bar kai domin ana bukatar hular, wannan lamari mai ban takaici ya yi nuni da cewa; hatta da alburushi da hula sun fi dan Adam kima.

Sai ga ma誕ikacin da aka dauka aiki domin ya kare al置mma yana harbe su ba su ji ba su gani ba, ana biyansa albashi da kudin al置mma domin ya kare ta, amma sai ga shi hatta da raunanan mutane kamar guragu yana kamowa yana harbewa. Kuma idan dai ba a dauki mataki kan wadanda suka yi wannan ba, to tabbas wata rana shi wanda ya sanya su yin hakan zasu yi wa danginsa ko shi ma ta fada kansa. Domin idan rashin hankali, da rashin imani, da kekashewar zuciya, da rashin tausayi, da rashin doka, suka yi jagoranci, to babu makawa zasu shafi kowane mutum ne. Idan rashin tsoron Allah da tunawa da cewa za a mutu a koma ga Allah ya yi hisabin dukkan abin da muka yi ya mutu murus, to sakamakon da za a samu kenan.

Musulunci ya sanya lamunin rayuwa ta hanyoyi masu yawan gaske, sai ya shimfida dokokin da zasu wadatar da dan Adam kamar zakka, humusi, sadaka, Baitul mali, kyauta, da ayyukan jin kai, sannan ya yi matukar gaba da jahilci da ba a taba samu ba a rayuwar dan Adam, sai ya tilasta neman Ilimi ko da kuwa a kasar Sin ne. Musulunci ya yi gaba da rashin ganin kimar dan Adam matuka, har ma ya 惣anta bawa saboda ubangidansa ya yanke masa al誕ura. Kai hatta da iradar yara da 惣an mata yayin zabin wanda zasu aura ya ba ta kariya. Sannan a fili yake hatta da addini bai tilasta kowa riko da shi sai wanda ya ga dama.

Sannan musulunci bai taba yarda da zubar da jinin mutum ya tafi a banza ba, don haka ne ma muke kira da gwamnati da ta biya diyya ga iyalan wadannan mutanen da aka kashe wadanda ba su ji ba su gani ba, kai hatta da kisan kare dangi da aka yi wa musulmi da sunan baki a Jos a watan Safar 1431 muna neman a biya su diyyar wannan bala段n da ya fada musu. Jinin mumini ba ya faduwa haka banza ya wuce sai an biya diyyarsa, kuma ya hau kan gwamnati ne ta mika diyya ga danginsa, duba wannan misali mai zuwa da zai nuna maka matukar kima da sakon Muhammad (s.a.w) yake bai wa dan Adam kamar haka:

Kulaini ya karbo daga Hasan ya ce: Yayin da Sayyidi Ali (a.s) ya rusa rundunar Dalha da Zubair (r) sai mutanen suka gudu suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi bari saboda tsoro, kuma dan nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu, sannan sai uwar ta mutu. Sai Imam Ali (a.s) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da danta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?. Sai suka ce: Tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yaki da rushewar mutane da gudunsu. Sai ya tambaya: Waye ya riga mutuwa a cikinsu?. Sai suka ce: Danta ya riga ta mutuwa.

Sai ya kira mijinta baban yaro mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar dansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga dansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da dari biyar, sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da dari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani da banda wannan da ta jefar da shi -barinsa- ya mutu. Ya ce: Wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara. (Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa'il, mujalladi 17, shafi: 446).

Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al'ummar musulmi da biyan bukatunsu, da bayar da hakkokinsu. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Hakkin mutum musulmi ba ya faduwa banza. (Manla yahaduruhul fakih, mujalladi 4, shafi: 100). Wani hadisin ya zo cewa: Jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al'umma da yalwa da arziki, da lamunce rayuwa, da adalci.

Musulunci ya zo da tsarin da ba shi da misali: ya haramta, ya wajabta, ya kwadaitar, ya karhanta, ya halatta. Duba abubuwan da aka wajabta a musulunci guda: 115, da kuma wadanda aka haramta guda: 97, da wasu: 112, da munanan halaye guda: 95, da kuma kyawawan halaye: 83, a littafin Tafarkin Rabauta.

Duk da yakin da daular Imam Ali (a.s) ta sha na kawo mata hari daga munafukai da makiya Allah da manzonsa (s.a.w) amma wannan bai hana samar da walwala da yalwata wa mutane ba, kuma yaki bai shagaltar da Imam Ali (a.s) daga maganin talauci da fatara daga al置mma ba, kuma bai hana shi aiwatar da adalci ba, bai hana shi ilmantar da mutane ba, bai hana shi dukkan wani abu da daular da ta fi kowacce zaman lafiya take yi ba!.

Imam Ali (a.s) shi ne ya fi kowane mutum jaruntaka a fagen fama kuma wannan lamari ne da ya shahara daga gareshi, ya kasance ya fi kowane mutum a duniya zuhudu bayan annabi (s.a.w), yana gyara takalminsa da kansa, yana dinke tufafinsa, yana gyara tsakanin mutane, yana ganin duniya ba ta kai kimar 惣ar majina da akuya take fyatowa daga hancinta ba, kimar duniya a wurinsa shi ne tsayar da umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, da tsayar da hukuncin Allah madaukaki.

Imam Ali (a.s) ya shahara da yin tsanani kan hakkokin mutane har sai ya kwata daga hannun azzalumai ya mayar da shi ga masu shi, ya kasance yana tsananta wa gwamnoninsa da wakilansa kan al誕muran mutane, yana yi musu hisabi mai tsanani kan dukiya da amana da hakkokin mutane na jini da na dukiya da mutunci.

Wasu mutane suna ganin idan sun yi umarni da kyakkyawa ko hani daga yin mummuna to wannan zai hana su wani arziki, ko ya kai ga jefa su cikin kunci, ko ma kisa, amma Imam Ali (a.s) yana ganin sabanin hakan, yana ganin cewa; umarni da kyakkyawa ko hani daga mummuna ba sa hana mutum arziki, kuma ba sa kusanto da azalinsa.

Imam Ali (a.s) shi ne shugaban masu hikima da ilimi, kuma littafin da ya tattaro bayanai game da hudubobinsa da hikimominsa, da wasikunsa sheda kan hakan. Ya kasance makoma ga dukkan sahabbai wurin sanin abin da suka jahilta bayan wucewar manzon rahama (s.a.w), sannan kuma ayoyi sama da 300 ne suka sauka game da falalarsa kamar yadda Ibn Abbas yake tabbatar da hakan. Sannan hatta da makiyansa kamar su Mu誕wiya da Amru dan Asi sun yi masa sheda da babu kamarsa.

Idan zai zabi wanda zai kasance gwamnansa ko wakilinsa yana zaba daga mutane ne masu hankali da takawa da ilimi, bai taba zaba don son mutum ba ba tare da ya cancanta ba.

Tarihin Imam Ali (a.s) shi ne Ali dan Abu Dalib (a.s) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar Asad (a.s) shi dan ammin Manzon Allah ne kuma mijin 'yarsa kuma wasiyyinsa halifansa a kan mutane bayansa wato; Amirul muminin mahaifin imamai (a.s).

An haife shi a Ka'aba mai girma a Makka ranar juma'a daren sha uku ga watan Rajab bayan shekaru talatin da haihuwar Annabi (s.a.w) kuma ya yi shahada daren juma'a a masallacin Kufa a mihrabi da takobin ibn muljam muradi 謀aga cikin hawarijawa- wannan kuwa a daren sha tara ga watan Ramadan ne kuma bayan nan da kwana uku ne a daren ishirin da daya na Ramadan ya yi wafati yana da shekaru sittin da uku, Imam Hasan da Husain (a.s) sun shirya janazarsa kuma suka binne shi a Najaf inda kabarinsa yake yanzu da wasiyyarsa (a.s) domin ya kubuta daga sharrin hawarijawa da Hajjaj daga tone kabarinsa, kuma wannan ya amfane shi[5], kuma Imam Ja'afar Sadik da Imam Musa Kazim (a.s) su ne suka nuna wa mutane inda kabarinsa yake (a.s).

Yana da falaloli da darajoji da ba zasu kirgu ba, ya kasance farkon wanda ya yi imani da Manzon Allah (s.a.w) kuma bai yi shirka da Allah ba koda sau daya, bai yi sujada ga gunki ba, don haka ne ma ake ce wa da shi; Allah ya girmama fuskarsa. Kuma yana tare da nasara a dukkan yakokinsa, bai taba gudu ba koda sau daya, shi mai kai hari ne ba mai gudu ba, bai taba ba wa yaki bayansa ba, bai taba gudu ba, kuma kyakkyawan hukuncinsa ya kai matuka har Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mafi iya hukuncinku shi ne Ali (a.s)[6].

Kuma saboda yawan iliminsa ne Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ni ne birnin ilimi Ali kuwa shi ne kofarta"[7]. Kuma saboda lizimtarsa ga gaskiya ya ce: "Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da Ali"[8].

Ya kasance mai adalci ne a jagorancinsa ga al'umma, mai rabawa mutane arziki da daidaito, mai nisantar kwadayin duniya. Ya kasance yakan zo Baitulmali sai ya duba abin da ya taru cikinta na zinare da azurfa yana cewa: "ya ke yalo! Ya ke fara! Ku yaudari wanina"[9]. Sannan sai ya rarraba wa mutane har sai babu abin da ya rage, yana tausaya wa miskinai, yana zama da talakawa, yana biyan bukatu, yana fadar gaskiya, yana hukunci da adalci, yana hukunci da abin da Allah ya saukar.

Yana aiwatar da hukunce-hukuncen Allah, yana kuma tafiyar da ayyukan Manzon Allah (s.a.w) har sai da alheri da albarka da yalwa suka mamaye kowa, da dukkan kasashe da dukkan garuruwa.

A takaice, ya kasance kamar Annabi (s.a.w) a dukkan siffofi da kyawawan halaye sai dai a wahayi da annabta, don haka ne Allah ya sanya shi kamar Annabi yake a komai banda annabta kamar yadda ya zo a ayar nan ta mubahala[10].

Imam Ali ya samu tarbiyya a gidan Annabi Muhammad (s.a.w) tarbiyyar da Annabi (s.a.w) a cikinta ya tanadar masa daukan nauyin da誕warsa ta Musulunci, da kuma daukar sakonsa mai tsarki.

Imam Ali (a.s) ya musulunta ne a lokacin da Annabi (s.a.w) ya kiraye shi zuwa Musulunci, a sa'ilin da Annabin ya dawo daga (kogon hira) yana dauke da sakon Musulunci zuwa ga mutane gaba daya.

Kuma addinin musulunci ya kasance addini na farko wanda Imam Ali (a.s) ya karba, domin kafin Musulunci bai karbi wani addini ba daga cikin addinan jahiliyya da kuma kafirci.

Kuma bayan musuluntar Imam Ali (a.s) sai Annabi (s.a.w) ya shiga shirya shi domin daukan nauyin da誕wa, musamman ma nauyin da誕wa na tunani da ilimi. Hakan kuwa a tsakanin lokaci mai tsayi na rayuwar da誕war a matakinta na sirri.

Hakika rayuwar Imam Ali (a.s) gaba dayanta Musulunci ce. Ta yadda ya bayar da dukkan abin da yake da shi har karfinsa a tafarkin da誕war Musulunci.

Ayyukansa (a.s) a wajen yada da誕wa sun kasance tare da gaba dayan kwanakin rayuwarsa daga farkonta har ya zuwa karshenta.

Daga cikin ayyukansa mafi shahara akwai:

1. Kwanansa a kan shimfidar Annabi (s.a.w) domin ya fanshi Annabi (s.a.w) daga kisan gillar da mushirikan Kuraishawa suka shirya.

2. Jagorantar tawagar masu yin hijira daga Makka zuwa Madina.

3. Jarumtakarsa a cikin yakokin Musulunci mafi shahara kamar: Badar, da Uhud, da Khandak, da Hunain, da Khaibar, da kuma yakin Bude Makka.

Halifancin Imam Ali (a.s) ya kasance ne bayan rasuwar Annabi (s.a.w) nan take (ba tare da wata tazara ba), hakan kuwa a saboda dalilai masu zuwa:

1. Saboda Nassosi a fili wadanda Annabi (s.a.w) a cikinsu yake nuna khalifa bayansa, kuma yake karfafa halifancin nasa a cikinsu.

Kuma daga cikin Nassosi mafi shahara: Hudubarsa (s.a.w) a Ranar Gadir a lokacin dawowarsa daga hajjin bankwana.

Kuma saboda Imam Ali (a.s) shi ne ya fi Musulmai dacewa da daukan nauyin halifanci bayan Annabi (s.a.w), saboda samun sharudda guda biyu na Imamanci a tare da shi.

Shi dai ya kasance Ma誕sumi ne, saboda dalilai masu zuwa:

a- Kasantuwarsa shi mutum ne musulmi tsantsa cikakke tun daga farko, domin bai bi wanin Allah ba, kuma bai kauce daga aikata hukunce-hukuncen shari誕r musulunci ba a cikin rayuwarsa, ya aikata su cikakkiyar aikatawa.

b Saboda shaidar da Kur誕ni mai girma ya yi masa a game da Isma a cikin aya mai zuwa (Allah yana son ya tafiyar da dauda daga kanku Ahlul-Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa)[11] Imam Ali (a.s) shi ne na biyun Ahlul bait (a.s) wadanda aka ambata a cikin wannan aya mai girma.

c Saboda shaidar da Annabi (s.a.w) ya yi masa a game da Isma a cikin hadisai, kamar: "Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da Ali. Kuma har abada ba zasu rabu ba har sai sun zo sun same ni a tafki (a gefen alkausara".

Kuma ya kasance wanda ya fi dukkanin Masulmi sanin shari誕, hakan kuwa saboda shaidar da Annabi (s.a.w) ya yi masa a game da hakan a cikin irin wadannan hadisai nasa masu zuwa:

1. Ni ne birnin ilimi Ali kuma kofarsa

2. Wanda ya fi ku sanin hukunci shi ne Ali

Sai dai cewa wasu dalilai na tarihi sun hana shi karbar mulki, sai ya fuskanci tafiyar da harkar wayar da kan mutane da kuma daidaita tafiyar da sha誕nonin daula a duk lokacin da maslaha ta gaba daya ta bukaci hakan. Hakan kuwa saboda kiyaye hadin kan Musulmi da rashin rarrabuwarsu. Kuma saboda tallafa wa al置mmar addinin Musulunci.

Bayan kashe Usman dan Affan a shekara ta (35 bayan hijira) Imam Ali (a.s) ya karbi halifanci. Kuma daga cikin muhimman ayyuka na gyara wadanda ya yi su akwai abubuwa masu zuwa:

1. Tsige gwamnonin da suka gabata (na lokacin Usman) da hukunta su, saboda ayyukan da suka aikata wadanda suka saba wa shari誕.

2. Yin watsi da tsarin raba dukiyar haraji wanda Umar dan Khaddab ya kirkire shi kuma Usman ya tabbatar da shi, Mayar da tsarin kamar yadda yake a lokacin Annabi (s.a.w), ta yadda rabon dukiya ya kasance a bisa asasin daidaitawa da rashin bambanta mutane a wajen rabon.

3. Dawo da gaba dayan abin da aka karba na dukiya a bisa tsarin rabo wanda aka kirkira.

4. Yin fada da kungiyoyi azzalumai wadanda suka soke shi a kan aikata tsarin Musulunci wanda ya yi a yakokin: Basara, da Siffin, da Nahrawan.

Imam Ali (a.s) ya rasu a cikin watan ramadhan shekara ta (40 bayan hijira) mutuwar kisan gilla a sakamakon zartar da shirin khawarijawa: wanda yake nufin kawo karshen shugabannin masu yin fada da khawarijawa.

Daga cikin shiryarwarsa: Ku sani bayin Allah (s.w.t) cewa fa shi mumini a wannan shekarar yana halatta abin da ya halatta a shekarar farko. Kuma a wannan shekarar yana haramta abin da ya haramta a shekarar farko. Kuma ku sani fa cewa mutumin da ya fi kowa haifar da bakin abubuwa ba zai halatta muku wani abu ba daga cikin abin da aka haramta muku. Shi dai halal shi ne abin da Allah ya halatta. Kuma haram shi ne abin da Allah ya haramta. Hakika kun gwada al誕mura, kuma kun wa誕zantu da wadanda suka kasance kafinku. Sannan an buga muku misalai, kuma an kiraye ku zuwa ga al誕mari bayyananne. Don haka babu mai rufe kunnensa daga hakan sai kurma, kuma babu mai rufe Idonsa daga hakan sai Makaho. Kuma duk wanda Allah bai amfanar da shi ba ta hanyar bala段 da tajrubobi, to bai amfana da wani abu daga cikin wa誕zi ba. Kuma takaitawa ta zo masa, har sai ya san abin da ya musa, kuma ya musa abin da ya sani. Su dai mutane guda biyu ne: mai bin tafarkin gaskiya da mai bin tafarkin bata babu wani dalili na Sunna daga Allah a tare da shi, kuma babu hasken wata hujja.

Kuma Allah (s.w.t) bai yi wa wani wa誕zi ba da, makamancin wannan Kur'anin domin shi igiyar Allah ne mai kwari, dalilinsa ne amintacce, kuma a cikinsa ne tsayuwar zuciya wajen tunani take, da kuma mabubbugar Ilimi. Kuma zuciya ba ta da abin da yake tafiyar mata da bakin ciki da kokwanto ban da shi. Duk da cewar masu wa誕zantuwa sun riga sun wuce sai masu mantuwa ne suka rage.

Don haka idan kuka ga abin alheri to ku taimaka a kan sa. Kuma idan kuka ga wani abin sharri to ku kauce masa.

Nahjul Balaga: Shi dai tarin hudubobi ne masu Kayatarwa na Imam Amirul mu置minina (a.s) da wasiyyoyinsa da wasikunsa da kuma gajerun kalmominsa na hikima.

Wanda ya tattara shi: Sayyid ash-sharif arradhi daga cikin malamai da masana adabi na karni na hudu bayan hijira.

Usulubinsa: Nahajul balaga bayan Kur誕ni da maganganun Annabi (s.a.w) kyawawa, sai shi a wajen daukakar usulubinsa na adabi. Ya fifita da zurfin tunani, da gaskiyar badini, da kayen bayani da adon zance, da kyawun ma誕na, da jan hankalin magana, da kuma babban tasiri ga mai karatu da mai sauraro.

Nahjul balaga ana kirga shi daga cikin muhimman littattafanmu manya wadanda suke a hannunmu a yanzu. Kuma ana fito da muhimmancinsa da abubuwa masu zuwa:

1. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen Ilimin harshen larabci da adabobinsa.

2. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen Ilimomin akidar Musulunci.

3. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen Ilimomin shari誕r Musulunci.

4. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen tarihin farkon Musulunci da Jahiliyya da al'ummomi na da.

5. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen da yawa daga cikin Ilimomi kamar; Tarbiyya, da Halaye, da Shugabanci, da Halayyar Mutum, da Zamantakewa, da kuma Siyasa.

Nahjul balaga yana kunshe da: Hudubobi da kuma abubuwan da aka ciro daga maganganun Imam Ali (a.s) guda 236, Wasiku guda 79, Maganganun hikima guda 480. Daga cikin kyawawan abubuwan da suke ciki akwai: hudubar tauhidi, da wasiyyar Imam Ali ga dansa Hasan (a.s), da kuma umarnin Imam Ali ga Malikul Ashtar gwamnansa a Masar (Misra).

Daga Nahajul Balaga; Daga cikin wasiyyar Imam ga dansa Hasan:

Ya kai dana ina yi maka wasiyya a game da tsoron Allah, da lazimtar umarninsa, da kuma gyara zuciyarka da ambatonsa, da kuma riko da Igiyarsa, kuma wace alaka ce mafi aminci tsakaninka da Allah idan ka yi riko da ita?

2. Daga cikin umarnin Imam ga Ashtar:

Wannan shi ne abin da bawan Allah Aliyyu Amirul mu置minin ya umarci Malik bn al-harith al-ashtar, a cikin umarninsa wanda ya yi masa a lokacin da ya nada shi gwamna a Masar: domin tattara harajinta, da yakar makiyinta, da gyara mutanen cikinta, da kuma gyara garuruwanta.

Ya umarce shi: da tsoron Allah: da fifita da'arsa, da bin abin da ya yi umarni da shi a cikin littafinsa na daga abubuwan da ya wajabta, da kuma sunnoninsa, wadanda babu wanda zai rabauta sai ta hanyar bin su. Kuma babu wanda zai tabe sai ta hanyar kin su da tozartar da su. Kuma ya umarce shi da ya taimaki Allah (s.w.t) da hannunsa da zuciyarsa da harshensa, domin shi madaukaki ya dauki nauyin taimakon wanda ya taimake shi, da daukaka wanda ya daukaka shi.

Kuma ya umarce shi da rike zuciyarsa a lokacin sha誕wance-sha誕wance, ya cire ta (ya kawar da ita) a lokacin sabo, domin ita zuciya mai yawan umarni ce da mummuna ban da wacce Allah ya yi wa rahama.

3. Daga cikin gajerun maganganun hikimarsa:

1. Ka gode wa wanda yake tsananta maka kuma yake yi maka wa誕zi, ba wanda yake tsarkake ka ba kuma yake yabon ka.

2. Ashararan mutane suna bin munanan ayyukan mutane su kyale kyawawan ayyukansu kamar yadda kuda yake bin gurare marasa tsafta.

3. Ka kiyayi mai aikata mummunan aiki, domin shi kamar takobi ne mai guba kallon sa yana faranta rai aikinsa kuma ya munana.

4. Ka guji bayar da uziri, domin takan yiwu wani uzirin ya tabbatar da hujja a kan ma誕bocinsa koda kuwa shi ba mai laifi ba ne.

5. Kada ka yi murna da faduwar waninka, domin kai kanka ba ka san abin da kake aikatawa ga wasu kwanaki naka ba.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Saturday, July 31, 2010[1] Shi rahama ce da kariyar al'umma daga dukkan musibu da sukan faru kamar gobara da girgizar kasa, da mamayar hamada da sahara, da kuma guguwar teku, da ambaliyar ruwa, da iska mai karfi.

[2] Wasa'ilus Shi'a, mujalladi 13, shafi: 151.

[3] Mustadrikul wasa'il, mujalladi 2, shafi: 490.

[4] Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 490.

[5] Ya zo a tarihi cewa: Hajjaj ya tone gabari dubu dari yana binciken kabarin Imam Ali (a.s).

[6] Kashful gumma: mujalladi 1, shafi: 263.

[7] Amali sheikh saduk, shafi: 345.

[8] Aljamal: shafi: 81. fusulul mukhtara: 97.

[9] Manakib, mujalladi 3, shafi: 257.

[10] Ali imrana: aya: 61.

[11]. Aya ta 33 daga Surar Ahzab.