Wasu daga zantuttukansa (A.S) akan abinda ya wajaba ‘yan’uwant- aka saboda Allah ta kasance akansa.
Imam (A.S) yana cewa: mutane ‘yanuwa ne, duk wanda ‘yanuwantakarsa ba ta kasance saboda Allah ba to gabace, wannan kuwa saboda fadin Allah madaukaki: “ma’abota a wannan rana makiyan juna ne sai dai masu tsoron Allah”. Surar Zuhuruf: 67.
Imam (A.S) yana cewa: Ka kyautatawa danuwanka nasiha, kyakkyawa ce ko mummuna, ka taimaka masa a kowane hali, ka karkata tare da shi duk inda ya karkata, kada ka nemi sakamako wajansa, domin wannan yana daga alamar kaskanci.
Imam ali (A.S) bai gushe ba shi ne alamin adalci mai girma, sunan sa mai tsarki ya gwamu da kalmar adalci, ya kasance adili da yake debe kewa da adalci yake kuma himmantuwa da shi.
Imam Ali (A.S) Bai taba yarda da kaucewa daga tafarkin adalci ba da aiwatar da shi koda da kiftawar ido komai wahalar da sakamakon haka zai haifar, ya ki yarda koda kuwa domin ya karfafa hukumarsa ne ya kaucewa hanyar adalci da gaskiya.
Game da hukuma da kare hakkin Dan adam, wata rana Abdullahi dan Abbas ya shiga wajansa yana gyara takalminsa sai Abdullahi dan Abbas ya yi mamaki kamar imam Ali a matsayinsa na Amirul muminina mai mulkin wannan daula mai fadi yana gyara takalminsa, sai imam ya tambaye shi cewa, menene kimar wannan takalmin a wajanku? Sai Dan Abbas ya ce: Ba shi da wata kima, sai imam Ali (A.S) ya ce: Wallahi ya fi soyuwa zuwa gareni fiye da shugabancinku, sai dai kawai domin in tsaida gaskiya ko dauki-ba-dadi da barna da ma’abotanta. Mulki a wajansu yana nufin tsayar da gaskiya da fada da bata da mutanensa.
Imam ali (A.S) ya yi taka-tsantsan kwarai fiye da yadda sauran ma’aikata da masu mukamai suke yi, bai taba sanya wani aiki a wani yanki da yankin duniyar musulunci ko ya dora shi kan wani aiki sai ya tabbatar da amincewa da addininsa, da kuma isarsa wajan tafiyar da al’amuran yau da kullum. Ba ya sa wani aiki domin sonsa, kadai yana bayar da aiki ga manyan musulmi zababbunsu, kamar Malik Ashtari, da Muhammad dan Abibakar, da Sahl dan Hanif, da Abdullahi dan Abbasa, da makamantansu na daga wadanda suke da cikakkiyar masaniya kan al’amuran tafiyar da mulki. Ya cika su da guzuri na muhimman wasiku da ya yi bayanin sha’anin hukumci da siyasar kasa, kamar yadda ya iyakance musu ayyukansu da nauyin da yake kansu.
Ya kasance yana bibbiyar ayyukan ma’aikatansa da gwamnoninsa, yana aika masu bincike a kansu domin su duba ayyukansu, idan ya ga ha’inci ko takaitawa a ayyukan dayansu sai ya kawar da shi, ya kuma saukar masa da mafi munin ukuba.