[Babin zababbun wasikun Amirulminin Ali (A.S) da wasikunsa zuwa ga makiyansa da amiran garuruwansa, kuma ya hada da abin da aka zaba na wasikunsa zuwa ga ma’aikatansa da wasiyyoyinsa ga iyalansa da sahabbansa]
[Wasikunsa zuwa ga mutanen Kufa, yayin da ya tafi daga Madina zuwa Basara]
Daga bawan Allah Ali Amirulminin zuwa ga mutanen Kufa, masu matsayin Ansar[1] (mutane Madina) kuma tozon kololuwar daukakar larabawa.
Bayan haka ina mai sanar da ku al’amarin Usman domin jinsa ya zama kamar ganinsa, Mutane sun soki al’amarin Usman, kuma ni na kasance daya daga cikin Muhajirun (Mutane makka da suka yi hijira zuwa madina) da na yawaita neman yardar da shi, na kuma karanta zarginsa, Dalha da Zubairu sun kasance mafi saukin tafiyarsu zuwa gareshi shi ne gaggautawa, mafi saukin abinda kafafunsu suka yi masa shi ne tsanantawa[2].
Ya kasance Aisha ta dauki gaba da fushi mai tsanani ta dora masa, sannan aka ba wasu mutane dama suka kashe shi, aka fusata su, aka in giza su, aka ba su dama kuma suka fusata suka kai hari suka kashe shi, Sannan mutane suka yi mini bai’a ba tare an takura su ba ko an tilasata su, A’a, sun yi bai’a suna masu biyayya masu zabi.
Ku sani, Gidan Hijira -Garin Madina- ta fito da mutanenta sun fito tare da ita, ta kuma raurawa da su kamar raurawar tafarfasar tukunya, fitina kuma ta tashi a sasanni, -Rikici ya yi kamari kuma fitina ta baibaye mutane- don haka ku yi gaggawa zuwa ga Amirinku, ku gaggauta zuwa yakar makiyanku, in Allah ya so.
[1] - Wani abu ne wanda kowa ya sani cewa Ansar sun taimaka wa Manzon Allah (S.A.W) shi ya sa imam Ali (A.S) ya kamanta su da su.
[2]Mutane sun kasance sun kosa da Usman, wanda ni kadai na kasance cikin Muhajirun wanda nake jawo hankalin mutane, sannan ni ne wanda na fadi kadan daga cikin aibunsa. Amma Dalha da Zubair mafi saukin aikin da suka yi shi ne suka yi masa tawaye kuma suka kai masa hari sannan ba su cece shi ba, kuma ba su tseratar da shi ba.