Wasika Ta 10

Daga Wasikarsa (A.S) Zuwa Gareshi (Mu’awiya) Kuma

Me zaka yi idan tufafin (sirrin) abin da kake cikinsa na duniya ya yaye maka a fili, kuma ta ci adonta da kyale-kyalinta, kuma ta yi yaudara da dadinta, kuma ta kira ka sai ka amsa mata, ta ja ka, sai ka bi ta, ta umarce ka sai ka amsa mata, kuma ya kusata wani mai tsayawa ya tsayar da kai (ga hisabi) akan abin da garkuwa ba ta isa ta kare ka daga gareshi ba, ka nisanta daga wannan al’amarin, ka riki tanadin yin tunani, ka lissafa abin da ya sauka kanka, kada ka mika wa batattu kunnuwanka, idan kuwa ba ka yi ba, zan sanar da kai abin da ranka ta gafala daga kanta da shi, kai mai yaudarar kai da takama ne, shedan ya riga ya samu abin da ya samu gunka, kuma ya ci burinsa da kai, kuma ya gudana a gareka gudanar nan cikin ruhi da jini.

Ya kai Mu’awiya yaushe ne ka zama mai jagorantar jama’a, mai tafiyar da al’amuran al’umma? Ba tare da wani rigon kirki ba, ko wata daukaka mai daraja ba. Muna neman tsarin Allah daga lizimtar mummunan rigon tabewa, kuma ina mai yi maka gargadi da kada ka ci gaba cikin dimuwar takamar gurinka, wanda (kuma kai ka kasance mutum ne da) zahirinsa ya saba da badininsa.

Kuma kai ka yi kiran mutane zuwa ga yaki, to ka kyale mutane daban ka fito mu buga da ni da kai, ka hutar da bangarori biyu wannan yakin, domin mu san wane ne mai tsatsa a zuciyarsa, wanda basirarsa ta toshe! Ni ne Abul-Hasan (A.S) wanda ya yaki kakanka da dan’uwan babarka da dan’uwanka ina saurayi a ranar Badar, kuma wannan takobin tana tare da ni har yanzu, da wannan zuciyar nake haduwa da makiyina, ban taba canja wani addini ba, ban kuma taba sake wani annabi ba, kuma ni ina kan tafarkin nan da kuka bar shi kuna masu zabin sonranku, kuma kuka shiga cikinsa kuna masu tilas.

Ka raya cewa ka zo ne kana neman fansar jinin Usman, hakika ka san inda jinin Usman yake, sai ka neme shi a can idan kana nemasa, al’amarin da zai kasance kai ka ce ni a wata rana ina ganinka kana ihu irin na rakumi da ya ji nauyin kaya saboda yaki yayin da zai cije (mamaye) ka, kamar dai wata rana ina ganin jama’arka sun zo suna masu raki saboda yawan duka da suke sha akai-akai na saran takubba, da kuma mutuwa mai faruwa, da kuma faduwa bayan faduwa, suna masu kira zuwa ga littafin Allah alhalin suna masu kafirce masa masu musunsa, ko kuma suna masu kira zuwa ga bai’a karkatacciya.