Wasika Ta 11

Sha daya Daga cikinsa wasiyyarsa da ya yi wa rundunar da ya aika zuwa ga makiya

Idan kuka sauka gun makiyi ko ya sauka gun ku, to rundunarku ta kasance daga gaba a waje mai tudu, ko kasan duwatsu, ko kuma tsakiyar kogi, domin ku samu wata kariya, kuma ku samu kariya. Mayakanku su kasance ta fuska daya ko biyu, sannan ku samu wasu kula a gefen dutse, ko saman tuddai, domin gudun kada makiya su bollo muku ta wata kusurwa don gudun tsoro ko neman kariya.

 Ku sani gaban mutane shi ne idanuwansu, kuma idanuwan gaba su ne masu leko musu asiri. Ku kiyayi rarraba, idan kuka sauka waje to ku sauka gaba daya, idan zaku tafi ku tafi gaba daya, idan dare ya yi muku ko ku sanya masu su gewaye ku, kada ku yi bacci sai mai sauki, ko kuma kuna yi kuna tashi.