Wasika Ta  12

Goma Sha biyu
Daga nasiharsa ga Mu’ukal dan Kais arriyahi yayin ay a aika shi zuwa Sham da jama’a dubu uku domin su share fage

Ka ji tsoron Allah (S.W.T) wanda ba makawa zaka hadu da shi, kuma babu inda zaka guje masa, kuma kada ka yaka sai wanda ya yake ka, ka tafi da mutane lokacin sanyin yanayi, ka kuma dakata su huta idan zafi ya yi, ka sukaka tafiya, kada ka tafi farkon dare. Ku sani Allah ya sanya shi mazauni, kuma ya sanya shi mataya ba tafiya ba, kuma ka hutar da jikinka, ka kwantar da bayanka (ka kwanta), idan ka tsaya yayin da alfijir zai yi, ko lokacin da yake bullowa, to sannan sai ka tafi da albarkar Allah, idan ka hadu da makiya to ka tsaya tsakiyar mutanenka, kada ka yi kusa da mutanen kusancin wanda yake son ya yi yaki, kuma kada ka nisance su, nisan wanda yake jin tsoron yaki, har sai umarnina ya zo maka, kada laifinsu ya sanya ku yakarsu kafin kiran su da yanke musu uzuri.