Sha uku Daga wasikarsa zuwa ga shugabanni biyua n rundunoni mayakansa
Hakika na jagorantar Malik dan Haris Al’ashtari da ku da dukkan wadanda suke tare da ku, sai ku ji ku bi daga gareshi, ku sanya shi kariya kuma garkuwa, ku sani shi yana daga cikin wadanda ba a jin tsoron rauninsa ko faduwarsa, ko jinkirinsa ga abin da ya kamata a gaggauta zuwa gareshi, ko kuma gaggautawarsa ga abin da jinkirta shi ya fi katari.