Wasika Ta  14

Sha hudu Daga cikin wasiyyarsa ga rundunarsa kafin haduwa da makiya a Siffaini

Kada ku yake su har sai sun fara muku, ku sani bisa godiyar Allah ku ne masu hujja, kuma ku bar su, su fara to wata hujja ce, idan kun samu rusa su to kada ku kasha mai gudu, kada kuma ku farwa mai gajiyawa, kada kuma ku yi farmaki kan mai ciwo, kuma kada ku farwa mata da cutarwa, koda kuwa sun ci mutuncinku, suka zagi jagororinku. Ku sani su raunana ne a karfi da raye da hankali, mu ana umartar mu ne da kamewa gabarinsu alhalin suna ma mushrikai, mutum yana iya haye wa mace a lokacin jahiliya ma da cutarwa da take kamar da dan dutse ko ‘yar sanda, amma sai a aibata shi da wannan da shi da zuriyarsa.