Sha biyar Ya kasnce (A.S) idan ya hadu da makiya yana mai yaki yana cewa:
Ya ubangiji zukata sun kwarara zuwa gareka, kuma wuyaye sun miku, idanuwa sun zaro, kuma an ciratar da kafafu, an tsofar da jikkuna. Ya ubangiji hakika abin da ake boyewa na gaba ya futo fili, kuma tafasar nan ta gaba ta kunkuna a zukata. Ya ubangiji mu muna kai kukan boyuwar annabinmu, da yawan makiyanmu, da rarrabar kawukanmu.
Ya ubangiji ka yi budi tsakaninmu da mutanenmu da gaskiya domin kai ne fiyayyen mai budi.