Wasika Ta Sha shida

Yana fada (A.S) ga sahabbansa yayin yaki

Kada ya tsananta a kanku idan kuka samu rusuwa da zaku sake dawowa domin sake kai hari, ko wata gewayowa da bayanta akwai kai hari, ku ba wa takubba hakkinsu, ku kuma yi shirin dukan da zai kai jiki kwance, ku kwadaitar wa kawukanku akan sukan (masu da takubba) suka mai tsanani da duka mai nauyi, ko kasha saututtuka domin hakan ya kawar da rushewa, Kuma na rantse da wannan ya tsaka kwaya, ya halitta masu rai, ba su musulunta ba sai dai sun mika wuya ne, sai suka boye kafirci, yayinda suka samu masu taimakawa sai suka bayyana shi.