Wasika Ta 17

Yana mai amsa ga wata wasikar Mu’awiya

Amma neman da ka yi in ba ka Sham, a yau ba zan iya ba ka abin da na hana ka shi jiya ba.

Amma fadinka cewa: Yaki ya cinye larabawa, sai wasu ‘yan rayuka da suka rage, to duk wanda gaskiya ta cinye shi to yana aljanna, wanda kuwa karya ta cinye shi yana wuta.

Amma daidaituwarmu a yaki da mazaje, ba ka fi ni karfin zartuwar kokwantonka a kan karfin zartuwar yakinina ba, kwadayin mutanen Sham ga duniya bai fi kwadayin mutanen Iraki ga lahirarsu ba.

Amma da ka ce: Mu ‘ya’yan Abdulmanafi ne, haka ne mana, amma sai dai Umayya, ba kamar Hashim ba ne, Harbu ba kamar Abdulmudallib ba ne, Abu Sufyan ba kamar Abu Dalib ba ne, kuma mai hijira ba kamar sakakke ba ne, mai bayyananniyar nasaba ba kamar wanda aka raba ba ne, mai gaskiya ba kamar mabarnaci yake ba, haka nan mumini ba kamar mabarnaci ba ne. Kai kancon na baya, na bayan da yake bin marigayansa zuwa gangarawa cikin wutar jahannama.

A hannunmu akwai kuma fifikon nan na annabta, wacce da ita ne muka shiryar da madaukakin mutum, kuma da ita ne muke daukaka dalili.

Yayin da Allah ya shigar da larabawa a cikin addininsa jama’a-jama’a, kuma wannan al’ummar ta sallama masa bisa tilas ko da zabi, kun kasance cikin wadanda suka shiga wannan addini: imma dai don kwadayi ko don tsoro, yayin da masu rigo sun rigaya sun rabauta da rigonsu, kuma masu hijira na farko sun tafi da falalarsu.

Kada ka sanya wa shedan rabo a cikinka, kuma kada ka ba wa kanka wata kafa a kanka, wassalam.