Wasika Ta 18

Zuwa ga Abdullah dan Abbas gwamnansa a Basara

Ka sani Basara masaukar Iblis ce, kuma madasar fitina, ka yi zance da mutanenta da kyautatawa garesu, ka cire musu kullin tsoro daga zukatansu.

Kuma labarin tsanantawarka da kausasawarka kan Banu Tamim ya zo mini, kuma alhalin Banun Tamim babu wani tauraro nasu da zai buya sai wani ya sake bullowa, sannan kuma babu wani rigo na gaba da suke da shi a jahiliyya ko a musulunci, kuma suna da wani zumunci gunmu, da wani kusanci na musamman, kuma mu masu samun lada ne a kan sadar da shi, kuma masu zunubi ne a kan yanke shi.

To ka tausasa ya kai baban Abbas, Allah ya yi maka rahama game da abin da ya gudana a hannunka da harshenka na alheri da sharri! To mu masu tarayya ne a cikin wannan, Ka kasance gun kyakkyawan zatona gareka, kada tunanina game da kai ya yi rauni, wassalam.