Wasika Ta 19

Zuwa ga wasu ma’aikatansa

Amma bayan haka, labari ya zo mini cewa; wasu daga cikin dagatai sun kawo kukan kaushin hali da kekasarka, da kuma wulakanci da jafa'I, sai na duba ban cewa a kusantar da su ba domin tarayyarsu, ko kuma a nisantar da su, a yi musu jafa'I domin alkawarinsu ba, ka sanya musu wani bargo mai taushi da zaka cakuda shi da wani abu na tsanani, ka yi mu'amala da su tsakanin tsanani da taushi, ka cakuda musu kusantarwa, da kuma nisantarwa, in Allah ya so.