Wasika Ta 2

[Wasika zuwa ga muatanen Kufa bayan cin nasara a kan tawayen mutanen Basra a shekara ta 36 a lokacin da mutanen Kufa suka kasance sun taka rawar gani]

Ya ku mutanen Kufa rokon Allah madaukaki ya saka muku da alheri daga Ahlin gidan Annabinsa (A.S) mafi kyawu daga abinda yake saka wa masu aiki da biyayya gareshi, kuma -ya saka muku da ladan da yake bayar wa ga- masu godiya ga ni’imarsa, hakika kun ji kun bi, an kira ku kun amsa.