Wasika Ta 20

Zuwa ga Ziyad dan Babansa

A lokacin yana wakilin Abdullahi dan Abbas a Basara, shi kuwa Abdullahi shi ne gwamnan imam Ali (a.s) a Basara, da yankin Ahwaz, da Karman, da Faris

Ina rantsuwa da Allah rantsuwar gaskiya, idan labari ya zo mini cewa ka yi ha'inci a rabon musulmi da wani abu dan kankani ko babba, sai na tsananta maka tsananin da zai mayar da kai mai karancin dukiya, mai nauyin baya (miskinin talaka), mai kaskancin lamari (wulakantacce), wassalam.