Wasika Ta 21

Zuwa ga Ziyad dan Babansa kuma

Ka bar barna kana mai tsakaitawa, ka tuna gobe a yau, ka rike dukiya sai wanda yake gwargwadon larurarka, ka yi 'yan bukatunka na yau kawai da dan abin da ya rage.

Shin kana son Allah ya ba ka ladan masu kaskan da kai alhalin kana cikin masu girman kai a wurinsa! Kuma kana kwadayin ya ba ka ladan masu yin sadaka –alhalin kana juyawa cikin ni’imar da kake hana raunana da zaurawa-? Ka sani mutum ana saka masa da abin da ya yin e, kuma zai ga abin da ya aikata ne, wassalam.