Wasika Ta 22

Zuwa ga Abdullahi dan Abbas

Ibn Abbas ya kasance yana cewa: Ban taba amfanuwa da wata mgana ba bayan ta manzon Allah kamar yadda na yi da wannan maganar:

Amma bayan haka, hakika mutum kan iya farin cikin riskar abin da bai iya kubuce masa ba, kuma kubucewar abin da bai kasance mai riskarsa ba takan bakanta masa rai, to farin cikinka ya ksance na abin da ka samu na lahirarka ne, kuma bakin cikinka ya  a kan abin da ya kubuce maka nata ne, amma kuma abin da ka samu na duniyarka kada ka yawaita shi da farin ciki, abin da ya kubuce maka nata kada ka yi bakin ciki a kansa kana mai raki, himmarka ta kasance ga abin da yake (domin) bayan mutuwa ne.