Wasika Ta 23

Yana fada yana mai yin wasiyya kafin mutuwarsa yayin da Ibn Maljam ya sare shi

Wasiyyata gareku ita ce; Kada ku tara wani abu da Allah, kuma Muhammad (s.a.w) kada ku tozarta sunnarsa, ku tsayar da wadannan ginshikai biyu, ba ku da wani zargi.

A jiya ni ne sahibinku, a yau kuwa abin lura ne gareku, gobe kuwa mai rabuwa da ku ne, idan na yi saura, to ni ne mai jinina, idan kuwa na kare, to daman karewa ce makomata, idan kuwa na yi afuwa to afuwa kusanci ne gareni, kuma lada ne gareku, ku yi afuwa “Shin ba kwa son Allah ya gafarta muku ne”.

Wallahi! Babu wani wanda ya yi mini mufaja’a da mutuwa da na ki, ko wani mai zuwa da na yi musun sa, ban kasance ba sai mai kama da mai neman ruwa da dare, ya tafi sai ya nema kuma ya samu, “Abin da ke wurin Allah shi ya fi ga nagari”.