Wasika ta Ishirin da Biyar

[Yana rubuta irinta ga wanda yake sanya shi wakilin sadaka da zakka, nan wani bangare ne na wasikar domin nuna adalcinsa cikin komai, komai kankantarsa]

Je ka a kan jin tsoron Allah daya wanda ba shi da abokin tarayya, kada ka tsorata wani musulmi, kada kuma ka keta shi bisa tilas, kada ka riki sama da hakkin Allah daga dukiyarsa, idan ka je wani wuri sai ka sauka gun ruwansu ba tare da ka cakuda shiga cikin gidajensu ba, sannan sai ka tafi wurinsu da nutsuwa da kawaici, har sai ka tsaya tsakaninsu sai ka yi musu sallama, kada ka yi rowar gaisuwa garesu.

Sannan sai ka ce: Ya ku bayin Allah, waliyyin Allah kuma halifansa ya aiko ni gunku domin karbar hakkin Allah daga dukiyoyinku, shin akwai hakkin Allah a cikin dukiyoyinku? Idan wani ya ce: Babu, to kada ka ce masa ba haka ba ne. Idan kuwa wani ya ce akwai, sai ka tafi tare da shi ba tare da ka tsorata shi ko ka yi masa kashedi ba, ko kuma ka zungure shi ko ka takura shi ba. Sai ka karbi abin da ya ba ka na zinare ko azurfa, idan kuwa yana da awaki ne ko rakuma, to kada ka shiga wurin sai da izininsa, domin mafi yawanta nasa ne, kuma idan zaka shiga wurin kada ka shiga kamar wani wanda aka sallada a kanta, ba tare da takura ta ba, kuma kada ka sanya dabba ta firgita kada ka tsorata ta, kuma kada ka bata wa mai ita rai, ka raba dukiya gida biyu, sannan sai ka ba shi zabi, idan ya zaba kada ka kama abin da ya zaba, sannan sai ka raba sauran gida biyu, sai ka sake ba shi zabi, idan ya zaba kada ka kuma kama abin da ya zama, haka nan zaka yi ta yi har sai abin da yake a cikinsa akwai rabon hakkin Allah a dukiyarsa ya rage, sai ka karbi hakkin Allah a gunsa.

Amma idan ya nemi ka yi masa zodiya (kamar idan ya sha’afa ko ya yi kuskure domin lissafin da ya yi akwai kuskure), sai ka yi masa (a sake maimaitawa tun daga farko), sannan sai ka kara cakuda su, sai kuma ka yi abin da ka yi tun farko, har sai ka karbi hakkin Allah daga dukiyarsa.

 Kada ka karbi tsohon rakumi ko takwarkwasasshe, ko karyayye, ko rarrauna, ko mai ido daya. Kuma kada ka bayar da amanar wannan sadaka (zakka) ga wani sai wanda ka aminta da addininsa, yana mai tausayawa ga dukiyar musulmi, har sai ya isar da shi zuwa ga waliyyinsu jagoransu don ya raba musu a tsakaninsu.

Kuma kada ka wakilta wani a kan karbarta sai mai nasiha da tausayi, kuma amintacce mai kiyayewa, ba mai takurawa ko mai tsanantawa ba, ba mai wahalarwa ko gajiyarwa ba. Sannan sai ka tattaro dukkan abin da ya taru gunka, (ka kawo) sai mu sanya shi inda Allah ya yi umarni da shi.

Idan kuwa amintacce ka ya (je karbar) zakka, to ka karfafa masa kada ya raba taguwa da danta, kuma kada ya tatse nononta ta yadda wannan zai cutar da dan da take shayarwa, kuma kada ya takura mata da hawa, ya daidaita tsakaninta da sauran dabbobi (a hawa da sanya aiki), kuma ya hutar da wanda ya gaji (a cikin dabbobin).

Kuma ya nemi taimko (a ayyukansa da) dabbar da karfafa a sawunta (rakumi) da kofato (kamar jaki), sannan ya gangaro da dabbobin zuwa ga duk wani rafi da suke wucewa, kada ya nisanta su daga duk wani wuri mai ciyaye da shuke-shuke, ya sanya su hutawa a wasu awowi, ya saukake musu ya saurara musu gun duk wani dan ruwa da aka samu ko ciyayi, har sai ya iso da su gunmu da kibarsu da izinin Allah, suna masu cika da kiba, ba wahalallu ba ko wadanda wahala ta gajiyar, domin mu raba su bisa littafin Allah da sunnar annabinsa, wannan shi ne ya fi girmamawa ga ladanka, kuma mafi kusa da dacewarka, in Allah ya so.