![]() |
![]() |
|
![]() ![]() ![]() |
[Ya rubuta abin da za a yi da dukiyarsa ne a cikinta bayan dawowarsa daga yakin Siffain]
Wannan shi ne abin da bawan Ali dan Abidalib ya yi umarni da a yi aiki da shi a dukiyarsa don neman yardarm Allah, domin ya sanya ni aljanna da shi, ya kuma ba ni aminci]
Yana mai cewa:
Hasan dan Ali (a.s) ne zai yi wannan aikin, ya ci bisa kyakkyawa, ya ciyar bisa kyakkyawa, idan kuma wani abu ya faru ga Hasan kuma Husain yana raye, to sai ya ci gaba da wannan aikin bayansa, ya yi kamar yadda yake yi.
Kuma �ya�yan Fadima (a.s) suna da sadakar Ali (a.s) kamar yadda yake ga �ya�yan Ali (a.s), kuma na sanya tafiyar da wannan ga �ya�yan Fadima ne saboda neman yardar Allah (s.w.t), da neman albarkar kusanci da Manzon Allah (s.a.w), da girmamawa ga huruminsa, da daukakawa ga kusancinsa.
Kuma an shardanta wa wanda zai sanya shi a hannunsa ya bar dukiyar a kan asalin yadda take, ya ciyar daga abin da ta haifar kamar yadda aka yi masa umarni da shi aka ba shi, kada ya sayar da wasu �ya�yan itaciyar shukar dabino, (a bar su) har sai an cika gonarsu da wani dashen (su yi ta yado).
Wadanda suke kuwa daga kwarkwarorina wadanda nake kusantar su -da suke da da ko ciki- sai a rike ta saboda danta, ita tana da albarkacinsa, idan kuwa danta ya mutu tana raye, to ita �yantacciya ce, hakika ya yaye mata bauta, �yanci ya �yanta ta.