[Daga Umarninsa (a.s) zuwa ga wani mai’aikcinsa da ya aika shi kan tara zakka yana umartarsa da tsoron Allah a boyayyun lamurransa, domin babu wani shaida in ba shi ba, kuma babu wani madogara sai shi]. Yana cewa:
Ina umartar sa da kada ya yi wani abu na biyayyar Allah a fili, sannan sai ya saba masa a boye, domin duk wanda zahirinsa bai saba wa badininsa ba, kuma aikinsa bai saba wa maganarsa ba, to hakika ya kiyaye amana, kuma ya tsarkake niyyar ibada.
Kuma ina umartar sa da kada ya fuskance su da munanawa, kada ya tsorata su, kuma kada ya nuna kyamar su, yana mai nuna fifiko a kansu da shugabanci a kansu, domin su ‘yan’uwa ne na addini, kuma mataimaka ne a kan fitar da hakkoki.
Ka sani kana da rabo da aka wajabta a cikin wannan zakka, kuma hakki ne sananne, da masu tarayya da kai daga miskinai, da raunana masu talauci, kuma mu masu ba ka hakkinka ne, don haka ka cika musu hakkinsu, idan kuwa ba ka yi haka ba, to kai kana daga masu mafi yawan abokan husuma da rigima a ranar lahira, , kuma tir da wanda abokan husumarsa gun Allah su ne talakawa, da miskinai, da masu roko, da wadanda ake korewa, da wadanda ba shi ya yi musu nauyi, da matafiya!
Wanda duk ya yi sako-sako da rikon amana, ya yi linkaya cikin ha’inci, bai tsarkake kansa da addininsa gaga garesu ba, to hakika ya jefa kansa cikin tabewar duniya, kuma shi a lahira yana daga cikin mafi kaskanci da tabewa. Kuma mafi girman ha’inci shi ne ha’intar al’umma, kuma mafi razanin algusshu (kwange da ha’inci kan abin da aka wakilta mutum) shi ne yi wa imaman shiriya algusshu, wassalam.