Wasika ta Ishirin da Bakwai

[Zuwa ga Muhammad dan Abubakar yayin da ya sanya shi gwamnan Misira] yana cewa:

Ka kaskantar da fukafukanka, ka tausasa bangarenka, ka sakar musu da fuska, ka daidaita su a bayar da lokaci da kallo, don kada masu girma su yi kwadayin zaluncinka garesu (talakawa), kuma kada raunana su yanke kauna daga adalcinsu garesu.

Kuma Allah madaukaki zai tambaye ku zama da bayinsa  game da karamin aiki da babba, da na zahiri da na boye, idan kuwa ya yi muku azaba, to ku ne kuka yi zalunci, idan kuwa ya yi afuwa to shi ne ya yi rangwame.

Ku sani ya ku bayin Allah cewa, masu jin tsoron Allah sun tafi da rabon duniya da ladan lahira, sai suka yi tarayya da ma’abota duniya cikin duniyarsu, amma ‘yan duniya ba su yi tarayya da su ba cikin ladan lahirarsu ba, sai suka zauna duniya da mafi kyawun yadda aka zauna ta, suka ci ta da mafi kyawun yadda aka ci ta, sai suka rabauta da duniya kamar yadda masu holewa suka rabauta da ita, suka dauki abin da masu girman kai suka dauka daga gareta, sannna sai suka cirata daga gareta da guzuri isasshe, da kasuwanci mai riba, suka samu dadin gudun haram a duniyarsu, suka samu yakinin cewa su ne makotan Allah gobe a lahirarsu, babu wani nemansu da ake mayarwa, kuma babu wani jin dadinsu da ake ragewa.

Ya ku bayin Allah ku ji tsoron mutuwa da kusantarta, ku yi mata tanadi, domin tana zuwa lamari mai girma, da babbar magana, da alherin da babu sharri tare da shi har abada, da sharrin da babu alheri tare da shi har abada. Wane ne ya fi kowa kusanci da aljanna fiye da mai aiki cikinta! Waye kuma ya fi kowa kusanci da wuta fiye da mai yin aikinta! Ku sani ko farautar mutuwa ce, idan ku tsaya mata sai ta kama ku, idan kun guje mata sai ta cimma ku, ta inuwarku lizimtarku (zama tare da ku), ga mutuwa a kulle ta a makwankwadar kanku, duniya kuwa ana nade ta daga bayanku; (wato duk wani minti daya da kuka ba wa baya, sai a nade shi, ba zai sake dawo muku ba!)

Ku ji tsoron wuta da zurfinta mai nisa ne, zafinta mai tsanani ne, azabarta sabuwa ce, gida ne da babu rahama cikinsa, kuma ba a amsa wani kira a cikinta, kuma ba a yaye wani bakin ciki a cikinta.

Idan kuna son tsoronku da Allah ya tsananta, kuma zatonku gareshi ya kyautata, to ku hada tsakaninsu, domin mutum kyakkyawan zatonsa ga ugangijinsa yana kasancewa ne gwargwadon tsoronsa ga ubangijinsa, kuma mutanen da suka fi kowa kyautata zato ga Allah, su ne suka fi kowa jin tsoron Allah.

Ka sani ya kai Muhammad dan Abubakar cewa ni na sanya ka jagoran mafi girman jama’ata guna mutanen Misira, kai ya cancanta ka saba wa son ranka, kuma ka kare addininka, kuma ko da ba ka da komai sai awa daya ta rage maka. Kada ka fusata Allah da neman yardarm wani mutum daga halittunsa, domin Allah yana cike gurbin waninsa, amma babu wani mai cike gurbin Allah.

Ka yi salla a lokacin da aka sanya mata, kada ka gaggauta lokacinta don wani abu, kuma kada ka jinkirta ta daga lokacinta saboda shagaltuwa da wani abu, kuma ka sani cewa kowane abu na aikinka yana bin sallarka ne.

Ka sani jagoran shiriya da jagoran bata ba daidai suke ba, haka ma masoyin Annabi da makiyin Annabi ba daya suke ba, kuma Annabi (s.a.w) ya gaya mini cewa: Ni ba na ji wa al’ummata tsoron mumini ko mushriki; amma mumini imaninsa zai hana shi (cutar da ita), amma mushriki Allah zai rinjaye shi da ikonsa, sai dai ni ina ji muku tsoron duk wani munafukin boye, masani a harshensa, yana fadin abin da kuka sani, yana aikata abin da kuke ki.