Wasika Ta 28

Wasika ta Ishirin da Takwas

[Yana bayar da amsa ga Mu'awiya]

Amma bayan haka, wasikarka ta zo mini tana fadin zabin da Allah ya yi wa Muhammad (s.a.w) ga addininsa, da karfafawarsa ga wanda ya karfafe shi

daga sahabbansa, kuma lallai wannan zamanin ya ba mu abin mamaki game da kai, da ka zama kana ba mu labarin jarrabawar da Allah ya yi mana, da ni'imarsa garemu game da annabinmu, sai ka zama kamar mai kai dabino Hajara, ko mai kiran mai koya masa harbi zuwa ga harbe-harbe.

Kuma sai ka ce wane da wane su ne suka fi kowa fifiko a musulunci, sai ka fadi abin da idan haka ne to babu ruwanka a ciki, idan kuma ya samu tawaya to laifinsa ba naka ba ne, kai ba ka cikin wanda ya fi ko wanda aka fi, kai ba jagora ba ko wanda ake jagoranta, me ya kawo sakakku da 'ya'yan sakakku cikin wannan lamarin, me ya hada su da wani abu da yake tsakanin muhajirai na farko, da kuma jerin darajoji, da sanin dabakokinsu! Abin mamaki da kibiya ta shigo da take bare ce, kuma sai ga wanda hukuncinta yake kansa yana hukunci cikin lamarin.

 Shin kai wannan mutumin ba zaka tsaya a iyakarka ba, ka san takaitawar matsayinka, kuma sai ka tsaya inda gwargwadon matsayinka ya tsayar da kai ba! Meye naka na yin galaba kan abin rinjaya, kuma cin nasarar da mai nasara ya yi ba naka ba ne, kuma kai me tafiya ne a cikin dimuwa, mai yawan karkata a cikin nufin.

Shin ba ka ganin -ko da yake ba ina gaya maka ba ne, sai dai ina ambaton ni'imar da Allah ya yi mana ce- cewa wasu mutane sun yi shahada a tafarkin Allah daga cikin muhajirai, kuma kowa yana da falala, amma har sai dai shahidinmu ya yi shahada, sai aka ce masa "Sayyidus Shuhada" shugaban shahidai, kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kebance shi da kabbarori saba'in yayin yi masa salla!

Kuma shin ba ka ganin an yanke hannayen wasu mutane a cikin tafarkin Allah -kuma kowa yana da falalarsa- har sai da aka yi wa dayanmu wannan kamar yadda aka yi wa dayansu, amma sai aka kira namu da "Mai tashi a cikin aljanna, kuma mai fikafiki biyu"!

Ba don Allah ya hana mutum tsarkake kansa ba, da na ambaci falaloli masu yawa da zukatan mutane suke sanin su, kuma kunnuwan masu sauraro ba sa kin su. Ka bar duk abin da kibiyar harbi ta kauce masa, hakika mu sakar Ubangijinmu ne, kuma mutane bayan nan su kuma sakarmu ne.

Dadaddiyar darajarmu, da kyawun alherinmu a kan mutanenka –kabilarka- ba su hana mu cakuda da ku ba, sai muka aura, kuma muka aurar, irin yadda tsararraki suke yi, ku kuma ba ku kai wannan matsayin ba! Yaya kuwa zaku kai wannan matsayi alhalin annabi (s.a.w) yana cikinmu, makaryaci yana cikinku, zakin Allah yana cikinmu, ku kuma zakin sojojin taron dangi yana cikinku, shugabannin samarin aljanna suna cikinmu, ku kuma kuna da yaran gidan wuta, mu muna da mafificiyar matan talikai, ku kuma kuna da Hammlatul Hadabi, da abubuwa masu yawa da muke da su na fifiko a kanku!

Musuluncinmu an riga an ji shi ko'ina, fifikonmu a jahiliyya ba mai inkarin sa, littafin Allah yana hada mana abin da ya guje mana, kuma shi ne fadinsa madaukaki: "Ma'abota kusanci sashensu sun fi sashe a littafin Allah", da fadinsa madaukaki: "Lallai wanda ya fi cancanta da Ibrahim su ne wadanda suka bi shi, da wannan annabi, da wadanda suka yi imani, kuma Allah shi ne majibincin muminai", don haka wani lokaci mu ne muka fi cancanta da kusanci, wani lokaci mu muka fi cancanta da a yi wa biyayya.

Kuma yayin da Muhajirai suka kafa wa Ansar hujja a ranar Sakifa da -kusancin- Manzon Allah (s.a.w), sai suka yi galaba a kansu, idan kuwa don shi ne aka yi galaba, to mu ne masu gaskiya, ba ku ba. Idan kuwa ba da shi ne aka yi galaba ba, to mutanen Madina –Ansar- suna kan maganarsu.

Kuma ka raya cewa wai ni na yi hassada ga dukkan halifofi, kuma na yi shisshigi a kan dukkaninsu, idan kuwa haka ne, to ba kai ne aka yi wa laifi ba, balle a kawo hanzari wurinka.

Kuma wannan kokawa ce da,

aibinta ya nesanta daga gareka

Kuma ka ce ana ja na kamar yadda ake jan rakumi mai kaucin hali don in yi bai'a, abin mamaki, ka so ka yi suka sai ka yi yabo, ka so ka kunyatar sai ka kunyata! Musulmi ba shi da wani laifi don ya kasance abin zalunta matukar ba yana shakku ne a cikin addininsa ba, ko kuma yana kokwanto a cikin yakininsa ba!

Wannan hujja ce da nake nufin waninka da ita, sai dai ni na ambata maka gwargwadon abin da ya samu daga gareta a ambatonta.

Sannan sai ka fadi abin da yake tsakanina da Usman, ai kai ya kamata ka amsa wannan saboda kusancinka da shi, wane ne ya fi zama mai keta huruminsa, ya kai ga kashe shi! Wanda ya taimaka masa –kamar Ali (a.s)- sai -Usman- ya zaunar da shi ya nemi ya dakata, ko kuma wanda –Usman- ya nemi ya taimaka masa –kamar Mu'awiya-, sai ya ki zuwa, ya kai shi ga mutuwa, har sai da kaddararsa ta zo masa, sam ba haka ba ne, wallahi Allah ya san wadanda suke zamewa –daga yaki- daga cikinku, da masu cewa da 'yan'uwansu ko zo nan wurinmu, sannan kuma ba sa zuwa yaki sai kadan.

Ban kasance ina bayar da uzurin cewa na soki abin da ya farar na bidi'o'i ba, idan kuwa laifina shi ne nuna masa hanya da shiryar da shi, to sau da yawa aka zargi wanda ba shi da wani laifi. Kuma sau da yawa mai yin nasiha yakan samu zato. "Ni ban yi nufi sai gyara gwargwadon yadda zan iya, kuma neman dacewa ta bai kasance sai da Allah, a kansa na dogara".

Sannan ka ce ba ka da wani abu gareni ni da sahabbaina sai takobi, hakika ka ba ni dariya bayan sanya kuka! A yaushe ne ka samu Banu Abdul-mudallib suna masu noke wa makiya, ko kuma masu tsoron takubba?! Ka zauna kadan domin Hamal dan Badar zan kawo yaki.

Kuma wanda kake nema zai neme ka, ya kusanto maka abin da kake nesantarwa, ni mai zo maka ne da gaggawa cikin rundunar Muhajira da Ansar, da masu biyayya garesu da kyautatawa, wadanda tirmutsinsu mai tsanani ne, kurarsu mai yaduwa ce, masu sanye da wandunan mutuwa, mafi soyuwar haduwa gunsu ita ce haduwa da Ubangijinsu, a tare da su akwai zuriya 'yar Badar, da takubba Bahashima, wacce ka san yadda kaifinta ya samu dan'uwanka, da dan'uwar babarka, da kakanka, da danginka. "Kuma ba nesa take ba daga azzalumai".