Wasika Ta 29

Wasika ta Ishirin da Tara

[Zuwa ga mutanen Basara]

Kuma ya kasance daga watsewarku da sabawarku da akwai abin da, da kun jahilce shi, amma sai na yi afuwa ga mai laifinku, na dauke takobi daga mai juyawarku, na karbi mai gabatowarku, idan abubuwa masu halakarwa suka ketare da ku, da raunin tunani da ra’ayoyi masu kauce gaskiya, da suke sanya ku jefar da ni, da saba mini, to amma ni kam na riga na kusantar da dokina, na riga na hau abin hawa ne.

Kuma wallahi idan kuka sanya ni dawowa zuwa gareku -sakamakon sake sabawarku- sai na yi muku wani ladabi -da kawo harin- da rakumi a zai zama kamar cin lamushewar lomar mai hadiya, sai dai cewa na san alheri ga wanda yake mai biyayya daga cikinku, da kuma hakkin mai nasiha. Ni ba mai shisshigi ne mai tuhumar wanda ba ruwansa ba, kuma ni ba mai warware alkawari ne ga mai cikawa ba.