Wasika Ta 3

[Wasikarsa zuwa ga Alkali Shuraihu Dan Haris]

An rawaito cewa Alkalin a kotun Amirulmuminin Ali (A.S) Mai suna Shuraihu Dan Haris ya sayi gida a zamanin imam (A.S) da dinare dubu tamanin, sai labari ya zo masa game da haka, sai ya kira Shuraihu ya ce da shi:

Labari ya zo mini cewa ka sayi gida da dinare tamanin, ka rubuta takarda a kan haka, ka kuma kafa shaidu a game da shi. Sai Shuraihu ya ce: Haka ne ya Amirulmimini (A.S).

Ya ce: Sai imam Ali (A.S) ya kalle shi kallo na mai fushi sannan ya ce da shi: Ya Shuraihu! Ka sani da sannu wanda ba ya duba littafinka, ba ya tambayarka shedu, zai zo maka har ya fitar da kai daga cikinta kai tsaye, ya mika ka zuwa cikin kabarinka kai kadai.

Ka duba ya Shuraihu! Kada ya zama ka sayi wannan gida ba daga dukiyarka ba, ko ka yi cinikin da ba da kudin halal dinka ba, sai ya zama ka yi hasarar gidan duniya da na lahira!

Amma dai da ka zo mini yayin da zaka sayi abin da� ka saya da na rubuta maka wannan takarda, da ba ka yi kwadayin ka sayi gidan ba koda da dirhami ne ko sama da hakan.

Takardar ita ce: wannan shi ne abin da bawa kaskantacce ya saya, daga matacce da aka matsa masa da tafiya (daga wannan duniya), ya sayi gida daga gidajen dimuwa daga gareshi, ta bangaren masu karewa, da shatawar halakakku, kuma wannan gida yana da iyaka guda hudu:�

Iyaka ta farko tana tukewa zuwa ga gidan cututtuka, iyaka ta biyu tana tukewa zuwa ga musibu, iyaka ta uku tana kaiwa ga son zuciya mai halakarwa, iyaka ta hudu tana tukewa zuwa ga shaidan mai halakarwa, ta cikinsa ne ake bude kofar wannan gidan.

Wannan rudadde ya sayi gidan da buri, daga wannan abin takurawa zuwa ga ajalinsa, ya sayi wannan gida da sharadin fita daga izzar wadatar zuci, da shiga cikin zillar nema da kaskanci.

Darasi daga wadan da suka gabata

Mai sayen wannan kaya ba abin da ya samu daga sayen, kuma alhaki ne a kan mai rididdiga jukkunan sarakuna, mai daukar rayukan jabberai, mai kawar da mulkin fir�aunoni, kamar kisira da kaisar, da tubba�a da himyara, da dukkan wanda ya tara dukiya a kan dukiya ya kuma yawaita, da wanda ya gina gini ya daukaka shi, ya kawata ya kuma adonta shi, ya yi kuma tari ya adana ya taskata, ya duba da rayawarsa ga �ya�ya, {to yana kansa} ya halarto da su gaba daya zuwa ga matsayin halartowa da hisabi, da wajan sakamakon lada da azaba, idan al�amari ya kasance da rarrabe hukunci, (A nan ne masu barna suka halaka).

Kuma hankali zai yi sheda da haka idan ya figa daga ribacewar son zuciya, ya kuma kubuta daga soyace-soyacen duniya.