![]() |
![]() |
|
![]() ![]() ![]() |
Wasika ta Talatin
[Zuwa ga Mu’awiya]
Ka ji tsoron Allah cikin abin da yake gareka, ka duba hakkinsa a kanka, ka koma cikin abin da ba a yi maka uzurin jahiltarsa, domin biyayya tana da alamomi bayyanannu, da tafarkuna masu haske, da hanya tsararriya, da hadafi abin nema, da masu hankali suke zo mata, kuma masu sokwanci suke saba mata, wanda duk ya kauce mata ya karkace daga gaskiya, ya fada cikin dimuwa, kuma Allah zai canja ni’imarsa, ya saukar da shi azabarsa.
Ka ji tsoron Allah a kanka! Hakika Allah ya bayyana maka tafarkinka, kuma tun da lamurranka suka kai ka ga dimuwa, to ka hau kan matukar tabewa, da sauka cikin kafirci, kuma ranka ce ta cusa maka sharri, ta jefa ka bata, ta gangara da kai halaka, ta tsananta maka tafarki.