Wasika ta Talatin da Daya
[Daga wasiyyarsa ga dansa Hasan (a.s) da ya rubuta ta a yankin “Hadhirin” yayin da yake dawowa daga yakin Siffin]
Daga Uba mai karewa, mai furuci ga -tsananin-zamani, mai juyawar rayuwa, mai sallamawa ga zamani, mai zargin duniya, mazaunin mazaunar matattu, mai tafiya daga cikinta gobe. Zuwa ga da mai burin abin da ba zai riska ba, mai bin tafarkin wanda suka riga suka mutu, mahallin rashin lafiya, mai wucewar zamani, abin jifa gun musibu, bawan duniya, mai sayar da dimuwa, abin bibiyar bala’o’i, ribatacce gun mutuwa, abokin zogin rai, ma’abocin bakin ciki, hadafin aibobi, kayayye gun sha’awa, magajin mutuwa.
Bayan haka, yana daga cikin abin da na gano na juyawar duniya daga gareni, da taurin kan zamani a kaina, da fuskatowar lahira zuwa gareni, akwai abin da yake hana ni tunawa da wanina, da himmantuwa da abin da abin da yake gabana.
Sai dai ni akwai bakin cikina da ya kebance ni ban da na mutane, sai ya juyar da ni daga ra'ayina, ya kawar da ni daga son raina, kuma ya nuna mini hakikanin lamarina, sai wannan ya kai ni ga gaske da babu wasa a ciki, da gaskiyar da babu karyar da ta cakuda da ita.
Kuma na same ka kai bangarena ne, kai na same ka kai ne dukkanina, har sai da ya kasance idan wani abu ya same ka kamar ya same ni ne, kuma kamar idan mutuwa ta zo maka ta zo mini ne, sai lamarin da ya dame ka ya kasance ya dame ni, sai na rubuta maka wannan littafin nawa, ina mai taimaka maka da shi in na wanzu gareka ko na mutu.
Kuma ni ina yi maka wasiyya da tsoron Allah –ya daya- da lizimtar lamarinsa, da raya zuciyarka da ambatonsa, da riko da igiyarsa, kuma duk wani tsani bai kai tsanin da yake tsakaninka da Allah madaukaki ba, idan ka yi riko da shi!
Raya zuciyarka da wa'azi, ka kashe ta da zuhudu, ka karfafe ta da yakini, ka hakaka ta da hikima, ka kaskantar da ita da ambaton mutuwa, ka tabbatar da ita ga karewa, ka wayar da ita ga musibun duniya, ka tsoratar da ita tsananin zamani, da munin juyawar darare da ranaku, ka bujuro mata labarum magabata, ka tuna mata abin da ya samu wanda yake gabaninka na farko, ka yi tafiya gidajensu da abin da suka bari, ka duba abin da suka yi kuma me suka bari, ina suka zauna ina suka sauka! Zaka same su cewa sun bar masoya, sun sauka gidan bakunci, kuma kai ma saura kadan kai ma ka zama daya daga cikinsu.
To ka gyara masaukinka, kuma kada ka zubar da lahirarka don duniyarka, ka bar magana da abin da ba ka sani ba, da zance da abin da ba a sanya ka ba, ka kame daga tafarki idan ka ji tsoron batansa, domin kamewa gun dimuwar bata ya fiye maka hawa abin tsoro, kuma ka yi umarni da kyakkyawa sai ka zama daga mutanensa, kuma ka ki mummuna da hannunka da harshenka, ka nisanci wanda ya yi shi da kokarinka, ka yi kokari a cikin –tafarkin- Allah matukar kokari, kuma kada zargin mai zargi ya rike ka a tafarkin Allah, ka kutsa wa tsanani zuwa gaskiya duk inda yake, ka yi ilimin addini, ka saba wa kanka da hakuri kan mummuna, kuma madalla da kyakkyawan hali kokarin yin hakuri, ka jingina kanka cikin lamurra dukkaninta zuwa ga ubangijinka, domin kai kana jingina ta zuwa ga kogo ne mai zurfi, da Kariya mai girma, kuma ka tsarkake niyya a cikin lamari ga ubangijinka, domin bayarwa da hanawa tana hannunsa, kuma ka yawaita neman zabi -yin istihara-, ka fahimci wasiyyata, kada ta bi bayanka ta wuce haka nan, domin mafi alherin magana ita ce wacce ta yi amfani.