Wasika Ta 32

Wasika ta Talatin da Biyu

[Daga wasikarsa zuwa ga Mu'awiya]

Ka halakar da jama'a daga mutane masu yawa, ka yaudare su da batanka, ka jefa su cikin kumfar koginka, duhu yana mamaye su, shubuhohi suna wangarar da su –buga su ko'ina da ambaliya-, sai suka karkata daga manufarsu, suka juya kan dugadugansu, suka juya bayansu, suka dogara kan lissafinsu, sai dai wanda ya koma daga ma'abota basira –wayewa-, wadannan sun bar ka bayan sanin ka, suka gudu zuwa ga Allah madaukaki suka bar taimakonka, domin ka dora su kan wahala, ka karkatar da su daga manufa.

Ka ji tsoron Allah ya kai Mu'awiya, ka ja ranka daga biyayyar shedan, domin duniya mai yankewa ce daga gareka, kuma lahira tana kusa da kai, wassalam.