Wasika Ta 33

Wasika ta Talatin da Uku

[Daga wasikarsa zuwa ga Kusam dan Abbas yana gwamnansa a Makka]

Amma bayan haka, ka sani mai ba ni labara daga yamma ya rubuto min yana sanar da ni cewa an turo wasu mutane daga Sham zuwa ga aikin hajji, masu makantar zukata, kurumtar ji, shafaffun gani, wadanda suke neman shafe gaskiya da bata, suna bin abin halitta don sabon mahalicci, kuma suna tsarkake neman duniya tsantsanta da addini, suna sayan magaugauciya (duniya) maimakon majinkirciyar masu tsoron Allah (lahira), alhalin babu wani mai rabauta da alheri sai mai aikata shi, kuma babu wanda ake saka wa da sharri sai mai yin sa.

To sai ka tsaya da abin da yake hannunka tsayuwar mai niyya mai kafewa, mai nasiha mai hankali, mai biyayya ga jagoransa.

Na hana ka yin abin da zaka kawo hanzari, kuma kada ka zama mai takama yayin ni'ima, ko mai rusuwa yayin talauci, wassalam.