Wasika Ta 34

Wasika ta Talatin da Hudu

[Wasikarsa zuwa ga Muhammad dan Abubakar yayin da labari ya zo masa na rashin jin dadinsa da kawar da shi daga shugabancin Misra, sannan aka sanya Ashtar ya je ya karbi matsayinsa, to a kan hanyar Ashtar ne kafin ya karasa Misra Imam Ali (a.s) ya rubuta masa  yana cewa]

Labari ya same ni cewa ba ka ji dadin sanya Ashtar a maimakonka ba, to ka sani ni ban yi haka don rena kokarinka ba, ko neman dada maka himma. Kuma da na karbi wani abu da yake hannunka na jagoranci, sai in ba ka wanda ya fi sauki gareka, kuma wanda ya fi kayatarwar jagoranci gareka.

Ka sani mutumin da na ba shi jagorancin Misra mutum ne mai soyayya garemu, mai tsananin fushi kan makiyanmu, Allah ya yi masa rahama! Ga shi ya cika kwanakinsa, ya hadu da mutuwarsa, mu muna masu yarda da shi, Allah ya ba shi yardarsa, ya ninka ladansa.

Ka bayyana ga makiyinka, ka ci gaba kan basirarka, ka shirya wa yakin wanda ya yake ka, ka kira zuwa ga tafarkin ubangijinka, ka yawaita neman taimakon Allah ya isar maka abin da ya dame ka, ya kuma agaza maka kan abin da ya sauka kanka, in Allah ya so.