Wasika Ta 35

Wasika ta Talatin da Biyar

[Daga wasikarsa zuwa ga Abdullahi dan Abbas, bayan kashe Muhammad dan Abubakar a Misira]

Amma bayan haka, hakika an ci Misira, kuma Muhammad dan Abubakar ya yi shahada, muna neman ladansa gun Allah (s.w.t), da ne mai biyayya, mai aiki da wahala, shi takobi ne mai yankewa, kuma ginshiki ne mai kariya.

Kuma ni na kasance na kwadaitar da mutane kan haduwa da shi, na umarce su da taimakonsa kafin yakin, na kira su a boye da a bayyane, kuma na maimaita kiran kuma na koma, daga cikinsu akwai mai zuwa bisa tilas, da mai kawo dalili na karya, da mai zama ya ki zuwa yana mai kin taimakawa.

Ina rokon Allah ya sanya mini wani budi na gaggawa, wallahi ba don kwadayina na yin shahada yayin haduwa da makiyina ba, da kuma abin da na dora kaina ba na shirin mutuwa, da ban so in wanzu tare da wadannan ba ko da rana daya, da ban so haduwa da su ba har abada.