Wasika Ta 36

Wasika ta Talatin da Shida

[Daga wasikarsa yayin da yake magana kan wata runduna da ya tura wa wasu makiya, wata amsa ce da ya rubuta wa dan'uwansa Akil dan Abi Dalib]

Sai na tura masa wata runduna mai yawa ta musulmi, yayin da labarinta ya je masa, sai ya yi shiri yana mai guduwa, ya warware alkawari yana mai nadama, sai suka same shi a wata hanya, rana lokacin ta kusa komawa (mafadarta), sai suka yi wani dan kwami (yaki), nan da nan sai dif kafa ta dauke, ba a yi wani abu ba sai kamar tsayuwar awa daya kacal, sai ya tsere yana mai gumde bakin ciki, bayan an riga an riki mashakarsa, ba abin da ya rage masa sai wani dan jan lumfashi, wahala kan wahala ta sanya bai tsira ba.

Kyale Kuraishawa da tserewarsu cikin bata, da kaikawonsu cikin sabawa, da tsaurin kansu cikin dimuwa, hakika su sun hadu a kan yaka ta kamar yadda suka hadu kan yakar manzon Allah (s.a.w) kafina, sai Kuraishu ta samu nawa sakamako daga gareni! Lallai ne sun yanke zumuncina, sun tube mini mulkin dan ammina.

Amma abin da ka tambaya game da shi na ra'ayina a yaki, to ra'ayina shi ne yakar masu halatta shi har sai na hadu da Allah, kuma yawan mutane a gefena baya dada mini wata izza, kuma rabuwarsu da ni ba ya kara mini wata dimuwa.

Kada ka yi tsammanin dan babanka (dan kabilarka wato shi Imam Ali (a.s)) ko da kuwa mutane sun bar shi (ba su taimake shi ba), cewa shi mai kaskan da kai, da rusunawa ne, ko mai rauni ne ga kyale zalunci, ko mai saukin ja ne ga mai ja, ko mai tausasa bayan hawa ne ga mai zama. Sai dai shi yana kamar yadda dan'uwan Banu Salim ya ce ne:

*Idan ka tambaye ne yaya kake, to ka sani ni

Mai tsananin hakuri ne bisa musibun zamani

* Yana nauyaya gare ni a gan ni da wani bacin rai

Sai makiyi ya yi dariya, ko masoyi ya bata rai