Wasika Ta 4

[Zuwa ga kwamandojin rundunarsa]

Idan suka koma zuwa ga inuwar biyayya to wannan ne muke so, idan kuma al'amura suka kai ga mutanen zuwa ga sabawa da keta doka, to ka bugi wanda ya saba maka da wanda ya bi ka, ka kuma wadatu da wanda ya bi ka yake tare da kai gabarin wanda ya zauna gabarinka, domin ka sani wanda yake jin kiwar yaki, fakuwarsa tafi halartarsa, kuma zamansa ya fi tashinsa –motsawarsa- tare da kai.