Wasika Ta 5

Daga Wasikarsa (A.S) Zuwa Ga Ash’as Dan Kais Gwamnan Azarbaijan

Ka sani hakika aikinka bai kasance abincinka ba, sai dai shi amana ce a wuyanka, kuma kai abin kula ne da kai gun na sama da kai, kuma ba kada hakkin yin zalunci kan al’umma, ko kuma ka yi wani tunani (kan wani aiki) sai da nutsuwa, kuma a hannunka akwai dukiya daga dukiyoyin Allah madaukaki, kuma kai kana daga cikin masu tsaron taskarsa, har sai ka bayar da shi gareni, kuma ni ba zan kasance mafi sharrin shugabanninka gunka ba, wassalam.