Daga Wasikarsa (A.S) Zuwa Ga Mu’awiya
Ka sani mutanen da suka yi wa Abubakar da Umar da Usman bai’a su ne suka yi mini bai’a akan abin da suka yi musu bai’a, don haka wanda ya gani yana da ikon zaba, kuma wanda ba ya nan ba shi da ikon yin raddi a kai, ka sani kuma shura ta muhajirun ce da ansar, idan suka hadu a kan zabar wani mutum suka ambace shi imami, to wannan shi ne abin da yake cikin yardar Allah, idan kuwa wani ya fita daga al’amarinsu da suka(n al’amarin) ko da wata bidi’a tasa, to sai su mayar da shi kan abin da ya fita daga gareshi, idan ya ki kuwa sai su yake shi a kan binsa ba tafarkin muminai ba, kuma Allah ya dora masa abin ya jibinta (ya dora wa kansa).
Abin mamaki ya kai Mu’awiya, idan da ka duba hankalinka ba son ranka ba, da ka same ni wanda ya fi kowa barrantuwa daga jinin Usman, kuma da ka san ni ba na cikinsa, sai dai ka yi da’awar laifi, sai ka yi ta yin da’awar hakan idan ka so! Wassalam.