Wasika Ta 7

Daga Wasikarsa (A.S) Zuwa Gareshi (Mu’awiya) Kuma

Bayan haka, hakika wasu wa’azozinka masu karo da juna sun zo mini, da kuma wasika da aka yi wa ado, da ka kyautata rubutunta da batanka, ka kuma zartar da ita da mummunan ra’ayinka, wasikar mutumin da ba shi da wani hasken basira da yake shiryar da shi, ko wani jagora da yake nuna masa hanya, wanda son rai ya kira shi sai ya amsa masa, kuma bata ya jagorance shi sai ya bi shi, sai ya yi surutu maras ma’ana, ya kuma bata yana mai tabewa.

Daga cikin wannan wasikar

Domin ita bai’a daya ce da ba a sake wani nazari a cikinta, kuma ba a farar da wani zabi a cikinta, mai fita daga cikinta abin suka ne, mai kokwanto a cikinta munafiki ne.