Wasika Ta 8

Daga Cikin Wasikarsa (A.S) Zuwa ga Jarir Dan Abdullah Al-Bajali Yayin Da Ya Aike Shi Zuwa Ga Mu’awiya

Amma bayan haka, idan wannan wasika tawa ta same ka, to ka dora Mu’awiya akan Magana yankakkiya, ka rike shi da al’amari mai karfi yankakke, sannan sai ka nemi zabinsa tsakanin yin yaki (irin yakin nan) mai kora (daga kasa), ko sallamawa (irinta) mai (nuna) gajiyarwa, idan ya zabi yaki sai ya ka shirya zuwa gareshi, idan kuwa ya zabi aminci sai ka karbi bai’arsa, wassalam.