Wasika Ta 9

Daga Wasikarsa (A.S) Zuwa Ga Mu’awiya

Sai wasu mutane suka yin niyyara kashe annabinmu, da kuma kawar da asalinmu, suka yi mana mugun kulli, suka yi duk abinda suka yi, suka hana mu ruwan dadi, suka tilasta mana tsoro, suka tilasta mu zuwa ga duwatsu masu tsandauri, suka kuma kunna mana wuta, sai Allah ya yi mana gamdakatar da kariya ga shari’arsa, da kuma kariya daga dukkan wani mummuna, mumininmu yana neman lada da wannan aiki da ya yi, kafirinmu yana kariya ga asalin (kabilarmu), duk kuma wanda ya musulunta na kuraishawa sai ya zama wannan bai shafe shi ba saboda wani kawance da yake kare shi, ko kuma wata jama’a da take yin kariya gareshi, kuma shi ya aminta daga kisa, manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan bala’i ya tsananta mutane suka labe sai ya gabatar da ahlin gidansa ya kare sahabbansa da su daga zafin takobi da masu, sai aka kashe Ubaida dan Haris a (yakin) Badar, kuma aka kashe Hamza a (yakin) Uhud, aka kashe ja’afara ranar yakin mu’utat, kuma wani mutumin da nag a dama da na fadi sunansa shi ma ya yi burin irin abin da suka samu na shahada, sai dai su an gaggauta ajalolinsu, an kuma jinkirta nasa ajalin.

Mamakin wannan zamani ya girmama! Da na kasance (a yau) na zamanto ana hada ni da wanda bai kai tafin kafata ba, bai da wata sabikiyya (rigon ayyukan alheri da hidima ga musulunci da al’umma da ilimi da sadaukantaka da dukkan kamala) kamar tawa, wacce babu wani mutum da yake da irinta, sai dai wani mai da’awar karya ya yi da’awar abinda ni ban san yana da shi ba, kuma ba na tsammanin Allah ma ya san yana da shi, godiya ta tabbata ga Allah a kowane hali.

Amma abin da ka tambaya na bayar da wadanda suka kashe Usman zuwa gareka, ni na duba wannan al’amarin ban ga zai yiwu in ba ka su ba, gareka ne kai, ko ga waninka. Na rantse da Allah! idan ba ka bar batanka da shakawarka ba, dasannu zaka gan su ba da jimawa ba suna nemanka, kuma nemansu ba zai wani dora maka wani nauyi ba a kasa ne ko a kogi, ko kan dutse ko malemalin kasa, sai dai shi nema ne da zai bata maka rai, kuma ziyara ce da haduwrta ba zata faranta maka rai ba, aminci ya tabbata ga ahalinsa.