HUDUBA TA 1:

[Tana kunshe da bayanai kan godiya ga ubangiji, da halittar samammu da da mala’iku da Dan Adam, da zabin annabawa, da aiko annabi (S.A.W), da Alkur’ani da hukunce-hukuncen shari’a da ambaton Hajji]

1-Kasawar Dan Adam A Kan Sanin Zatin Ubangiji:

Godiya ta tabba ga Allah wanda masu magana suka kasa fadar kalmar yabo wadda ta cancanta gareshi, sannan masu lissafi suka kasa lissafa ni'imominsa, kuma masu kokari suka kasa aiwatar da hakkinsa a kansu, wanda masu zurfin tunani suka kasa sanin hakikanin zatinsa, kuma masu nutso a cikin kogin ilimi ba zasu taba isa zuwa ga zatinsa ba, wanda suffofinsa ba su da iyaka da aka iyakance, ko wata siffa ta samammu ko wani lokaci kididdigagge, ko wani ajali iyakantacce. Ya halicci halittu da kudurarsa, ya sanya iska yana kadawa da rahmarsa, Kuma ya kafe duniya da duwatsu da ya sanya a bayan kasa.

2-Addini Da Sanin Ubangiji:

Abu na farko a ckin addini shi ne sanin Allah, sannan kamalar sanin Allah shi ne gasgatawa da shi, kuma cikar gasgatawa da shi, shi ne kadaita shi, sannan kamalar kadaita shi, shi ne tsarkake shi, cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi(n halitta) gare Shi saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba shi ne abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuma ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya gididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: Akan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin (Alhalin Allah yana ko'ina bai kebanta da wani wuri ba).

Kasantacce ne ba tare da faruwa ba, samamme ne ba daga rashi ba, yana tare da komai ba tare da sun hadu ba, kuma shi ba shi ne sauran samammu ba, ba tare da sun bambanta ba, mai aiki ne amma ba da motsi ko amfani da kayan aiki ba, shi mai gani ne yayin da babu wani mai ganinsa daga halittarsa, makadaici ne yayin da babu wani wanda yake samun nutsuwa (debe kewa) da shi, ba ya kuma samun dimuwa saboda rashinsa (ba abinda rashinsa zai iya sanya Allah madaukaki dimuwa da fitar hayyaci).

3-Hanyoyin Sanin Allah Madaukaki:

Na Daya: Halittar Duniya:

Allah Madaukakin sarki ya kagi halittarsa da kagowarsa, ya fare ta fararwa, ba tare da wani tunani ba da ya kokkoma masa, ko wani gwaji da ya amfana daga gareshi ba, ko wani motsi da ya farar[1], ko wani tunanin rai da ya yi kai-kawo a cikita.

Ya jingina al’amura bisa lokacinta, ya kuma daidaita tsarin tsakanin masu sabawarta, sannan ya sanya wa kowace halitta dabi'ar da ta dace ita, ya lizimta mata makamancinta, {mutum yana neman mutum dan’uwansa, zaki da zaki kamar yadda kowannensu ya san abincinsa da makwancinsa da yadda kuma zai yi tarbiyyar zuriyarsa da makamancin haka.} Yana mai sane da ita kafin ya fare ta, yana mai kewaye da sanin iyakokinta da karshenta, ya san hakikaninta da sasanninta.

Sannan sai Ubangiji ya keta sasannin sarari, ya tsaga nahiyoyi, da magudanar iska, ya kuma gudanar da ruwa da tunkudarsa mai ambaliya ce, daduwarsa (karuwarsa) da mikuwarsa (da kwaranyarsa) masu hauhawa ne, Ya dora shi akan iska mai karfi, mai girgiza kowane abu tana tumbukewa, ya umarce ta da dawo da shi, ya dora ta akan tsananinsa, (wato ya sallada iska akan igiyoyin ruwa) ya gwama ta zuwa iyakarsa (domin haka ne iska take juya shi yadda ta so), iska ce da ya sanya ta daga karkashinta mai rarrabawa da fatattakawa, ruwa yana daga sama mai tunkudar juna[2].

Sa’annan Ubangiji (S.W.T) ya tayar da wata iska mayofinciya (mai kanjamawarwa da busarwa, ba ta barbara ga ‘ya’yan itace ko tsakanin gajemare da gairagizai) ya lizimta mata matabbatarta, ya tsananta magudanarta, ya nisantar da mafararta, ya umarce ta da sirka ruwa, da tayar da ambaliyar kogi (teku), sai ta kada shi kadawa mai tsanani irin kadawar gajimare, ta yi watanda da shi a sararin samaniya, tana mayar da na farkonsa zuwa karshensa, tana mayar da na karshe farko, tana kuma hada kan mai zuwa da mai dawowa (mai kaiwa da mai komowa) har ya makala malalarsa, ambaliyarsa kuma ta fitar da kumfa[3]. Ya daukaka shi a cikin iska mai daidaitawa, da sarari mai yalwa, sai ya daidaita sammai bakwai daga gareshi, ya sanya kasansu ambaliyya maras kaikawo da kwarara, samansu kuma rufi abin kiyayewa, rufinta madaukaki ne, ba tare da amudi (dirka) da yake rike ta ba, babu wata kusa da take tsarata.

Sannan ya kawata ta da adon taurari, da haske mai hudowa, ya gudanar da fitila mai haskakawa a cikinta, da wata mai haske: a falaki mai kewayo, da rufi mai wanzuwa, da falakin rakimi mai juyawa.

Na Biyu:Halittar Mala'iku:

Sannan ya tsaga abinda yake tsakanin sammai madaukaka, sai ya cika su da mala'iku, daban-daban; Daga cikinsu akwai wasu gungu kodayaushe suna masu sujjada ba sa yin ruku’u, da wasu masu yin ruku'u kodayaushe ba tare da sun mike tsaye ba, sannan wasu daga cikinsu suna tsaye a cikin sahu ba tare da sun rarraba ba, sannan wasu daga cikinsu suna cikin tasbihi kodayaushe ba tare da sun kosa ba, bacci ba ya daukar idanunsu, ko kuma rafkanwar hankula, ko gajiyawar jiki, ballantana sha’afar mantuwa.

Daga cikinsu akwai amintattu akan wahayin ubangiji, kuma ‘yan sakonsa zuwa ga manzanninsa, masu kai da kawo wajen zartar da hukucin ubangiji da umarninsa. Sannan wasu daga cikinsu masu tsaron bayin Allah ne, wasu kuwa masu tsaron kofofin aljannarsa ne.

Daga cikinsu akwai wadanda kafafuwansu suke a kan doron kasa ta karshe, wuyayukansu kuma sun zarce sammai madaukaka, sannan sasanninsu sun zarce fadin duniya, sannan al'arshin ubangiji yana kan kafadunsu, ganinsu yana mai kaskanta gabarinsa, suna masu kanannadewa a karkashinsa da fukafukansu. An sanya hijabin izza tsakaninsu da wadanda suke bi musu, da suturar labulen k’udra, ba sa siffanta ubangujinsu da surar tunani, ba sa kuma jingina masa siffar halittu, ba sa iyakance shi da wajaje, ba sa nuna (kamanta shi) shi da tsararraki.

Na Uku, Halittar Adam:

Sannan Allah mai girma da daukaka ya tattaro kasa daga sassa daban-daban, ta tudu da ta kwari, mai dadi da mai zartsi, kasa ce da ya kwabata da ruwa har ta koma yumbu, bayan nan ya kara mata lema kadan sai ta koma mai danko, sai ya halitta surar (Adam) daga gareta ma’abociyar sassa da mahadai, da gabbai da mararrabu, ya busar da ita har ta kakkame, ya sandarar da ita har ta bushe kayau, zuwa wani lokaci kididdigagge, zamani sananne.

Sannan sai ya yi hura a cikinta daga ransa, sai ga shi ta zama surar mutum ma’abocin kwakwalwa da yake tunani da ita, da tunani da yake tasarrufi da shi, da gabbai da yake amfani da su, da ala da yake jujjuya ta, da sani da yake bambance wa tsakanin gaskiya da karya da shi, da mashakai da madandanai, da launoni da jinsosi, yana abin kwabawa daga turbayar tabo iri daban-daban, da makamantan juna da aka harhada, da kishiyoyin da suke hannun riga da juna, da kwababbun abubuwa mabanbanta,  na daga zafi da sanyi, da taushi da tauri, da bakin ciki da farin ciki.

Sa’annan Allah ya nemi bayar da amanar da ya dora ta akan mala’iku[4], ya yi wasiyya da shi a garesu na rusunawa da kaskantakar da kai da sujjada a gareshi, da tankwarawa don girmama shi, Mai girma da daukaka ya ce: “Kuyi wa Adam sujjada, sai suka yi sujjada banda Iblis” da k’abilarsa, k’abilanci ya rike shi, tabewa ta rinjaye shi, ya yi jiji-da-kai da girman kan halittarsa da wuta, ya kuma wulakantar da halittar yunbu, sai Allah ya ba shi rata domin cancantarsa ga fushinsa, da kuma cikawar nan ta jarrabawa, da kuma zartar da alkawarinsa, sai ya ce: “Kai abin jinkirtawa ne zuwa ranar wa’adi sananne”

Sannan Allah madaukakin sarki ya zaunar da Adam (A.S) a wani gida, ya tanadar masa jin dadin rayuwarsa a cikinta, ya amintar masa wajan zamansa, ya yi masa gargadin Iblis da kiyayyarsa, Sai makiyinsa ya yaudare shi domin hassada gareshi game da gidan wanzuwa, da abokantakar abrar, sai ya sayar da yakininsa da kokwanto, niyyarsa kuma da rauni, ya musanya farin ciki da tsoro, dimuwa kuma da nadama. Sannan sai Allah ya yalwata masa karbar tubansa, ya jefa masa kalmar rahmarsa, ya yi masa alkawarin gangarawa aljannarsa, ya kuma saukar da shi gidan jarabawa da yada zuriya.

Na Hudu: Hikimar Aiko Da Annabawa:

Allah madaukaki ya zabi Annabawa daga ‘ya’yansa, ya dauki alkawarinsu da yin wahayi garesu, ya dauki amanarsu da isar da sakonsa, yayin da mafi yawancin halittarsa suka canja alkawari suka kuma jahici hakkinsa, suka riki waninsa ababan bauta tare da shi, shaidanu suka kautar da su daga saninsa, Suka kuma yanke su ga barin bautarsa, sai ya aika musu manzanninsa ya kuma bibiya musu annabawansa domin su neme su da bayar da hakkin halittan nan ta fidirarsa[5], su kuma tunatar da su abin mantawa na daga ni’imarsa, su kuma kafa musu hujja da isarswa, su kuma motsa musu abin nan da yake kunshe na  tunanin hankali, su kuma nuna musu alamomin  kudura; na rufin samansu madaukaki da shimfida (duniya) abin sanyawa a kasansu, da rayuwa (kayan rayuwa)  da take raya su, da ajaloli da suke karar da su,da wahalhalu da suke tsofar da su, ya fararrun abubuwa da suke bibiyar juna akansu.

 Allah bai taba barin halittarsa ba annabi dan sako  ko littafi saukakke ko hujja tabbatacciya ko tafarki tsayayye ba, manzannni ne da karancin yawansu ko yawan masu karyata su ba ya cutar da su, imma wanda ya wuce kuma aka gaya masa na bayansa, ko wanda zai zo da na gabaninsa ya sanar da (al’umma) shi; akan haka ne karnoni suka yadu, zamanoni suka wuce, iyaye suka gabata, ‘ya’yaye suka maye gurbinsu.

Na Biyar: Hikimar Aiko Manzo Muhammad (S.A.W)

Har Allah Madaukakin Sarki ya aiko muhammad (S.A.W) domin cika alkawarinsa, da kammala annabtarsa, yana mai karbar alkawarin imani da shi akan annabawa, alamominsa shahararru ne, haihuwarsa mai daraja ce, alhalin a lokacin mutanen duniya suna masu rarraba addinai daban-daban da son rai iri-iri[6], da kungiyoyi mabanbanta, daga mai kamanta Allah da bayinsa, sai mai shisshigi a sunayensa da mai nuni zuwa waninsa {Da sunan yana nufin Allah}.

Sai Allah ya shiryar da su daga bata da samuwar manzo, ya kuma tseratar da su daga wauta da jahilci saboda darajarsa.

Na Shida Wajabcin Imamanci Da Halifanci Bayan Manzo (S.A.W)

Sa’annan ya zaba wa Muhammad (S.A.W) haduwa da shi, ya kuma yardar masa da abinda yake gunsa, ya kuma girmama shi da barin wannan duniya, ya kwadaitar da shi daga barin cakuden nan na jarabawar duniya, sai ya karbe shi zuwa gareshi yana abin girmamawa, ya kuma bar muku abinda annanbawa suke bar wa al’ummarsu, domin annabawa ba sa barin al’ummarsu haka nan; ba tare da tafarki bayyananne ba, ko wani mai kulawa {Halifa}tsayayye ba.

Na Bakwai, Alamomin Kur'ani Da Na Hukunce-Hukucen Musulunci:

Littafin Allah madaukaki yana a hannunku wanda yake a matsayin mai bayyanar muku da halas da haram, da wajibai da mustahabbai, da hukunce-hukunce masu shafewa da shafaffu, da rangwamensa da tilas dinsa, da kebantattun hukunce-hukuncensa da gama-garinsa, da daukar darasinsa da misalansa, da sakakkunsa da iyakantattunsa, da muhkamansa da masu shubuha, yana mai fassara dunkulallunsa {gumurtsinsa} yana mai bayyana ritsitsinsa.

Da wanda aka riki alkawarin bayi akan saninsa, da kuma wanda aka yafe wa bayi jahiltarsa, da wanda aka tabbatar da faralinsa a littafi, da wanda shafe shi yake sananne a sunna, da kuma wanda aka wajabta rikonsa a sunna, da wanda aka yi rangwamen barinsa a littafi, da kuma wanda wajabcinsa yake da lokaci kayyadadde, da mai gushewa a gaba {wato wanda lokacinsa yake fita}, da mai bayyanar da haramunsa; imma babban laifi da aka yi alkawarin wuta ga mai yinsa ko karami da ya yi fakon gafarta shi, da wanda kadan dinsa yake abin karba, yawansa abin yalwatawa daidai gwargwadon iyakar iyawa.

Na Takwas; Hikimar Wajabta Aikin Hajji:

Allah madaukaki ya wajabta muku hajjin dakinsa mai alfarma, wanda ya sanya shi alkibla ga mutane, suna gangaro masa irin gangarowar dabbobo a tabki, suna shauki gareshi irin cincirindon nan na tattabari,  ya sanya shi alami na kaskan da kai ga girmansa, da karkata ga izzarsa, ya zabi masu sauraron da suka amsa ga kiransa, suka gaskata kalmarsa, suka tsaya matsayar annabawansa, suka kamanta da mala’ikunsa masu dawafi da al’arshinsa, suna masu taskace ribobi a wajan kasabin bautarsa, suna masu gaggautawa zuwa ga ma’alkawartar gafararsa.

Ubangiji ya sanya shi alami na musulunci, kuma harami na masu neman mafaka, ya wajabta hajjinsa, ya wajabata kiyaye hakkinsa, ya tilasata halartarsa a kanku, sai mai girma da daukaka ya ce: “Allah ya wajbta hajjin daki akan mutane ga wanda ya sami ikon zuwa gareshi, wanda ya kafirce hakika Allah mawadaci ne ga barin talikai”.


[1] - Domin Allah ba jiki ba ne balle ya yi motsi.

[2] - Karkashin kadawar iska mai karfin gaske, wato ya bai wa iska ikon kada ruwa yadda take so, ta kuma mayar da shi zuwa fuskar da yake so, Sannan ya sanya iska a matsayin mai kula da ruwan ta yadda yakan sanya masa iyakoki, ya sanya sarari a karkashin iska ya kuma sanya ruwa yana motsi a samansa.

[3] - Wato ya sanya ruwa yana ambaliya sannan igoyoyin ruwa suna gamuwa da junansu, iska mai karfi takan auku ta yadda yakan fara daga wani wuri mai nisa, sannan ya sanya ruwa ya tafiyar da igiyoyin koguna zuwa bangarori daba-daban, kuma kamar yadda iska yake da karfi a cikin sarari haka yake kaiwa kogi hari ta yadda yake kwasar farkon kogi ya aika shi zuwa karshensa, sanna ya sanya ruwan da yake zaune a wuri guda zuwa mai motsi sama da kasa, ta yadda yakan hada ruwa da junansa, ya haifar da tudu kamar tsaunuka.

[4] - Wato ya nemi mala’iku da su zo da amanar da ya ajiye a cikinsu na alkawarin biyayya.

[5] - Wato abin da halitta su akansa na kadaita shi, da imani.

[6] - Wato ayyukansu suna jujjuyawa ne tayadda umarni na tunaninsu ya zo masu ne.