Huduba Ta 10

[Game da shedan, amma yana nufin wasumutane ne]

Ku saurara ku ji! Shedan ya tara rundunarsa, ya jawo dawakansa (mahayan dawakai) da kuma rundunar kasa, hakika ni a tare da ni akwai basira, ban taba samun rikecewar al'amarina a, kuma ba a taba rikitar da ni ba. Na rantse da Allah! Sai na cika musu tafki da ni ne mai shayarwarsa! Ba sa zo masa, kuma ba sa dawowa zuwa gareshi.