Huduba Ta 11

[Yanamai gaya wa dansa Muhammad dan Hanafiyya yayin da ya ba shi tuta ranar yakinJamal]

Duwatsu suna gushewa amma kada ka gushe! Ka cije turamenka (wato; hakoranka na ciki), ka ba wa Allah aron makwankwadar kanka, ka kafa kafafunka a kasa, sannan ka jefa ganinka can karshen mutanen, ka kuma runtse idanuwanka (wato; kada ka ji tsoron su), ka sani kuma cewa; taimako daga Allah ne madaukaki.