Huduba Ta 12

[Yayinda Allah ya ba shi nasara kan ma'abota Rakumi: Ashabul Jamal]

Wanidaga sahabbansa ya ce masa: na so a ce dan'uwana wane yana tare da kai domin ya ga abin da Allah ya ba ka na taimako a kan makiyanka. Sai imam Ali (A.S) ya ce masa: Shin kaunar dan'uwanka garemu take (wato; yana goyon bayanmu yana tare damu)?

Saiya ce: haka ne.

Saiimam (A.S) ya ce: To hakika ya halarci yaki tare da mu, kuma da akwai mutane da suka yi musharaka da mu a wannan yaki namu da suna cikin tsatson mazaje, da kuma mahaifar mataye, da sannu kuma zamani zai yo habonsu (wato; zai zo da su), kuma imani zai karfafa da su.