Huduba Ta 13

Daga Zancensa (A.S) Game Da Sukan (da ya yi wa) Garin Basara Da Mutanensa [Bayan Yakin Jamal (yakin Rakumi)]

Kun kasance rundunar mace, mabiya dabba[1], ya yi kuka sai kuka amsa, an soke shi sai kuka gudu, dabi’unku munana ne, kuma alkawarinku sabawa ne, addininku munafunci ne, ruwanku mai gishiri ne, wanda yake cikinku abin kamawa ne da laifinsa, kuma wanda ya bar ku mai riskar rahama ne daga ubangijinsa. Kai kace ni ina ganin masallacinku kamar kirjin (gaban) jirgin ruwan da Allah (S.W.T) ya aiko masa da azaba ta samansa daga kuma ta kasansa, sai wanda yake cikinsa ya nutse.

A wata ruwayar: na rantse da Allah (S.W.T) sai wannan gari naku ya nutse -a ruwa- kai ka ce ni ina ganin masallacinta ya koma kamar gaban jirgin ruwa, ko kuma wata jimina mai faduwa -kifewa- kan kirjinta.

A wata ruwaya: kamar gaban kirjin tsuntsu a cikin wata ambaliyar ruwa.


[1]Rakumi