Huduba Ta 15

Daga Zancensa (A.S) Game da abin da ya mayar (da shi) ga (baitul mali na dukiyar) musulmi na daga abubuwan da Usman ya bayar (da su kyauta ga wasu mutane)

Ya ce: wallahi! da na samu an auri mata da shi, kuma an mallaki bayi da shi, da na mayar da shi; ku sani hakika akwai yalwa a cikin adalci, kuma duk wanda adalci ya yi masa kunci, to zalunci ya fi yi masa kunci!